Sashe 8
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sororo tayi a gun kamar an dasa ta, Dan ta tsorata da yanayin sa na yau ya dawo mata sak Ya Mu'azzam d'in ta na da can, bata Ankara ba taji saukar Mari a kuncin ta har guda biyu, aiko batasan lokacin da ta kai tsaye tsabar rikicewa, dafe da kuncin...
"Shashashar banza! Dama tsiyatakun da kike shukawa a gidan kenan? Yaushe kika yada tarbiyar da na baki kika d'ora da wannan banzar tarbiya? Ke a d'an tsugunninki har kinsan ya zakiyi ki zubar da ciki? Ashe dama kin tashi daga Aymana zuwa wata bak'uwa da ban sani ba? Kin bani kunya Aymana kin b'ata wayonki"
Kicin shesshekar tace "kiyi hakuri Ammi wallahi shine baya sona, Ammi kwaila fa ya kirani yace ban isa mace ba, yanzu ma da kika ga yana wannan abun duk don wani buri nasa ne na daban, kuma wlh...."
"Ke! Dakata min, k'arya kike, nafi kowa sanin k'aunar da Mu'azzam yake miki, nasan Mu'azzam sanin da ko mahaifiyar sa batayi masa shi ba, shi kanshi baisan na fahimci son da yake miki ba tun ba yau ba, kin d'auka yana takura ki ne a zuwan k'i? Waima na tambayeki ya tab'a gaya miki baya sonki?" Kai ta shiga girgiza wa alaman Aa dan tasan bai tab'a furta mata baya sonta ba tun can da yake tsorata har lokacin da yake gasa mata magana...
"Kada ki manta jinin jikinsa ne ke yawo a naki jikin ko gama hard'ewa da nakin baiyi ba, amma da yake ke butulu ce shine yau kika kalli k'wayar idonsa kika gaya masa bakya k'aunarsa..." Wlh Ammi bance bana k'aunarsa ba..." Ta katseta.
"Yimin shiru! Cire masa ciki dai-dai yake da furta bakya k'aunarsa, amma zanyi miki uzuri d'aya saboda bakisan waye d'a ba gun iyayensa saboda rashin k'aunar da kike yiwa Mu'azzam ya saka ki jin tausayi da bege irin na uwa, ya hanaki jin zafin rasa cikinki da kikayi, wannan kanki kika yiwa, saidai inaso ki sani duk kika ci gaba da rashin mutuncin da kike masa har kika kai ya saka ki!" Wani mugun bugu k'irjinta yayi ta runtse ido da sauri hawaye suka samo damar bin fuskarta har kamar ruwa "karki yadda ki doso ni, kije ki nemi wata uwar amma bani ba!" Ammin ta sake fad'a a tsawace.
Duk'awa tayi cike da kad'uwa jin furucin Ammi na k'arshe tare da kama kafafun ta tana kuka sosai "Ke kam Fatima sau nawa zan gaya miki kibi wannan 'ya a hankali wannan ai duk aikin kuruciya ne, duka nawa Bilkisun take?"Hajja ta amsa wacce ta jiyo wasu daga cikin maganganun su..
" Inna Ba wata kuruciya a tare da Aymana sai renin wayo shekara 19 ai tasan me takeyi, iskanci ne kawai saboda taga yana bata dama"
"Aa Fatima tsakanin Mata da Miji sai Allah, bakisan me yake mata ba, kuma ko da baya mata komai ai ta rarrashi da nasiha za'abi a magance komai bata hantara da tsawa ba, kuma ma banda abinda ai ba abinda zai kai ga ya saketa, in suka rabu ai burin mu ya fad'i k'asa na wad'ancen shedanun yayi nasara, ki kyaleni da jikalle na Indai ke ba zaki iya lallab'ata, haba tana ji da jikinta duk kun zo kun tashi hankalinta, shima Almuri guda ya d'asa bom ya gudu bari zaizo ya sameni ai" Hajja ta k'ara fad'a tare da Jan hannun Aymanan, itama Ammi ciki ta shige ta barsu anan dan ta gama fahimtar Hajja bata so ake ga laifin Aymana, ga gaskiya ido da ido amma ana danneta...
************
Direct tsohon part d'in su ya wuce, ya safa da marwa ya shiga yi cikin Falon, amon muryarta yake ji tana ta amsawa a kunnensa kamar yanzu take fad'a masa, Ashe da har haka yarinyar nan ta tsane shi bai sani ba, da ya d'auki abin nata da sauk'i amma yanzu ya tabbatar wa kansa ba zata tab'a sonsa ba, dak'yar ya isa saisaita kansa ya danne zuciyarsa ya shiga cikin gidan Dan gaisawa da Momy, yana shiga Falon nata ta dakatar da shi ta hanyar nuna masa inda ya fito...
"Karka kuskura ka shigomin, muddin ba zaka cika Umurni na ba, tuka fara tunanin canja wata Uwar ka gane! Kaje can na barwa Fatima ta had'a gaba d'aya kai da tsiyatakun yaranta" zai bud'e baki yayi magana ta katse shi "ka ficemin nace ko kuma nayi maka baki" ta fad'a a tsawace, wadda har Samha dake falon sanda ta zabura a tsorace tana zare ido, juyawa yayi ya fice ransa na matuk'ar suya, da alama so suke ya buga wannan shine rana zafi inuwa k'una, a balcony ya had'u da Samiha zatayi magana ya zabga mata wata uwar harara wacce ta tilasta mata janye wa gefe ta bashi hanya ya wuce fuu kamar iska....
Murmushi ta saki wadda yafi kama da keta "Hmmm Mu'azzam u will soon know my true colour.........
_ina baran Addu'arku na rashin 'yar Yayata da mukayi yau d'innan, wanda ya tilasta dole na tsaya anan, pls pray for her😢😭😭 My Fido may ur gentle soul rest in perfect peace_ 👏🏻👏🏻👏🏻
*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*_Makaho bai tab'a ganin haramun ba, kurma bai ta sauraren Karya ba, bebe bai taba yin gulma ba, Mara hannu bai taba sata ba, da ni'imomin da Allah yayi mana muke sab'a masa, muji tsoron Allah_*
Duniya makaranta✍🏼
*Page* 3⃣7⃣
_________Tsitt kakejin parlon, banda Muryar Abba bakajin ta kowa a gun "yanzu ku Samiha da Samha abinda kuke aikata wa k'anwar taku ya kyautu? Fisabillah kun kyauta..." Karaf Hajja ta amshe...
"Yo wad'annan kyautatawa suka sani, da hankalin su dana mota ai duk d'aya, yanzu banda abin ya zamo na gida ai da Allah kad'ai yasan inda abin zai tsaya dan kila har hursuna sai sunyi tunda shege ne..." Haba Inna dan Allah dena fad'ar haka" Ammi ta fad'a ba tare da tasan tayi ba, Su Momy kuwa harare harare kamar su yasar da idanun kasa, sun cika fam dan tun da aka maida zancen abinda ya faru Abba da Dady ke zuba fad'a duk akan 'ya'yansu.
"Shikenan duk ba wannan ba Inna, yanzu inaso naji daga gareku dalilinku na had'uwa Ku duketa duka ma bana hankali ba, kamar ba 'yar uwarku ba, kamar ba jininku ba kamar Ku ba *Zuria d'aya* bane? Meye dalilin ku?" Dady ya fad'a yana kallon gefen da Samihar da Samha ke zaune, Samiha ce tayi katsal tace..
"Dady tunda akayi auren banda rashin kunya ba abinda take mana a gidan bani kad'ai ba har Ya Mu'azzam gashinan" ta nuna gun da Mu'azzam din yake, ko d'ago baiyi bare ya nuna yasan zancen da take hakan yasa taci gaba...
"Tun abin na a rashin kunya har tazo ta fara zagin mu..." Zagi!" Aymana ta fad'a ta k'arfi tare da ware ido "yi mana shiru har ta kammala bayaninta" Ammi ta tsawace ta, dole tayi kasa dakai tana mamakin sharri k'iri-k'iri..
"Nasha masa magana akan ya d'auki mataki amma yayi biris da zancen wai kuruciya ne, shine fa har Samha idan taje bata barin ta take had'awa da ita ta zage, kai har Ku zagi take yasin Abba" ta karashe tana kukan kirsa....
Aymana kam tuni ta dask'are a gun gata zaune da ranta ana mata sharri "k'arya kike yi Munafuka" Hajja ta fad'a a tsawace "wannan da kuke gani duk kirsa da kitihi ba wanda ta baro baya ta gadi abinta, bayan sun gama cutar da ita kuma shine abin ya dawo 'yar sharri, ko kunsan tun da suka tare a gidan Balkisu ce ke zaman yi musu girki a gidan kamar wata baiwa, bayan su duka matan gida ne, dai-dai da rana d'aya wannan kilibanbar bata tab'a shiga kitchen da sunan girki ba, kuma ni ba gayamin akayi ba nina gani da Idona hakan yasa nayi amfani da hikima ta na gano lallai itace keyi dana bugi cikinta naji tabbas hakane, yo ita batayi korafi akanta ba sai sune shafaffu damai zasu ce ga kara ga icce kuma tsabar mugunta hadda duka gashi sunyi mana asarar Mutum" Hajja ta k'arashe da ranta b'ace...
Gyaran Murya Abba yayi "Yanzu dai duk naji komai, kuma komai daya faru ya riga da ya wuce, duk wani tone-tone ba shine ba, amma dole Ku gyara halayen Ku, dan kuwa ba ku da gaskiya ko kad'an, kome Ummina take muku a matsayin Ku na manya a gareta idan ba zaku iya hak'uri da ita ba kamar yadda na nema tun farko a gareku a matsayin ta na wacce ke da Kuruciya fiye daku, meya hana Ku kawo k'orafi agare mu? Mu d'auki mataki? Amma kukaje kukayi gaban kanku gashi a sanadin haka kun salwanta rayuwa, rayuwar da bata san meye ake ciki ba duk akan son zuciya, yanzu fisabillah idan kune akayiwa haka dad'i zakuji?" Cije leben k'asa Mu'azzam yayi yana jin zafi a ransa "ai dama baka damu kanka akan cikin ba Abba dan mai shi ma ba son shi take ba, nine dai cutar dama" ya fad'a a ransa.
"Baku kyauta ba, Ku bata hakuri sannan Ku kiyaye na gaba tun da wannan dai ya riga ya faru..."
"Haba dai Alhaji, wannan adalci kenan, yarinya ta Rena su, sun duke ta cikin bacin rai, kuma shi ai ya rama mata yayi musu bak'in duka amma kuma duk sai a d'aura laifin akansu wannan ne adalcin?" Momy ta fad'a dan dai ta danne zuciyar iya yanda zata iya amma ta kasa hak'ure wa kamar yadda Umma tace suyi kada tace komai duk abinda za'ayi amma dake ita bata iya boye feelings din ta ta kasa hak'ure wa..
"Zainab! Zainab kenan wai meyasa kika cika son kanki ne da yawa? Yanzu ke da Samha ce aka yiwa haka me zakiji a ranki? Ki ringa nazari akan Abu......"
"Yo kaima Mamuda in banda abinka ai yaci ka saba da halin wad'annan matan" tana nufin Momy da Umma "ai duk banzan halin da wad'annan sakarkarun keyi duk tarbiyarsu ce kun sani sarai, kaidai ayi sha'ani kawai"..