← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Miscarriage" ya maimaita a fili dama Ashe ciki ne da ita da gaske kamar yadda yake hasashe, amma kuwa ya zama wawa daya kasa gane hakan tun farko, yayi sake wanda yaja masa rasa gudan jininsa, baisan lokacin da hawaye suka wanke masa fuska ba cike da juriya irin tashi yayi saurin goge hawayen tare da cewa nurse d'in suje a gwada nashi in zaiyi dan shi kowa ma bai samu gayawa ba asalima yabar wayoyin a mota, yafi so sai yaga ta farfad'o tukun kafin ya samu nutsuwar sanar da gida...

Cikin sa'a kuwa jininsu yazo d'aya aka d'iba nan take...

Duk yadda Mudi yaso gate man d'in ya bari ya shiga gidan fur ya murje ido ya ce baisan zancen ba tunda oga bai kirashi ba dama gashi k'abila sarkin kafiya da rik'o gashi wani gabjeje kakk'arfan gaske, haka dole Mudi ya koma ya gayawa Momy an hanashi Shiga..

Wayar Mu'azzam taci gaba da kira cikin b'acin rai sosai gashi tana ring amma baya d'agawa aiko takai k'arshe a k'uluwa sai kwafa take...

Zuwa yanzu kuka Samha takeyi dan tasan ta gama kad'ewa har ganyenta musamman da taga kiran mijinta ya shigo mata, kasa d'agawa tayi sai fad'i take "na banu na gama ai" itama Samihar hankalinta Sam baya jikinta gashi ta kasa samun umman ta a waya...

Ganin wani kiran ya k'ara shigowa a wayar ne yasa ta had'iye yawu tare d'agawa hankali tashe "kina ina" taji saukar muryarsa a kunnenta a kausashe "um...um..inaa..." Katse ta yayi..

"Good duk ma inda kike daga nan ki wuce gidanku har na nemeki" bin wayar tayi da kallo kafin ta rushe da kuka tare da d'ora hannu akai "Wayyo Allah na, amma dai Samiha kin zaja min"......

Manage pls am busy

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*Daga Umar bin khattab (R.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace "da zaku tawakkali ga Allah matuk'ar tawakkali, daya azurta ku kamar yadda ya azurta tsuntsu ya wayi gari da yana mai jin yunwa sannan ya maraita yana k'osasshe( darasi ka dogara ga Allah dayi masa kyakyawan zato zai azurta ta inda bakayi tsammani ba).*

Husnul Muslim👌🏻

*Page* 3⃣4⃣

________hannunsa cikin nata ya zuba mata ido, tayi fayau da ita ga fuskarta duk ta kumbura saboda duka, d'ayan hannunsa yakai ya shafo cikinta, kwallar da ta tarar masa a ido ce ta sauko a fuskarsa " shikenan na rasa my lovely baby? U must pay I swear! Both of you" ya fad'a a sarari cikin jin d'aci a ransa, jinin da aka saka mata ya kalla yana sauka a hankali alaman zai dad'e kamin ya k'are, kallon yadda take sauke numfashi yayi daga gani tana jin jiki, k'ara runtse hannunta yayi a nasa cike da tausayin ta "get well soon my habibty Aymaa..wish you speed, jet, quick recovery dear" kifa kansa yayi kan gadon da take kwance, kan nasa wani irin ciwo yake masa d'aurewa kawai yake yi, cikin jarumta irin tasa...

"Sir!" Nurse d'in d'azu ce sam ko shigowar ta baiji ba, d'agowa yayi tare da kallonta ba tare da yace komai ba, k'asa tayi da kanta kafin tace...

"Ba zata farko da wuri ba saboda munyi mata allurar bacci dan ta samu Hutu sosai, kaima kana buk'atar ka huta, it better kaje gida ka samu Hutu kaima ka kuma ci abu mai kyau ko zaka samu kuzari a jikinka, pls kaje zan kula da ita kafin 'yan gidan ku suzo fatar ka kirasun" sai lokacin ya tuna daya kira gida ma...

"OK thanks" kawai ya fad'a tare da mik'ewa, har wani jiri-jiri yake ji, mota ya isa tare da d'aukar wayarsa Ammi kawai yaga ya kamata ya kira, ganin miss calls d'in yayi ba adadi, yasan bazai wuce akan wad'ancan criminals d'in bane, bai bi ta Kansu ba ya kira Ammi, yace dan tazo hospital yanzu gashi tare da Aymana ba tada lafia, amsa masa tayi bayan yayi mata bayanin hospital d'in, sannan ya Kira Adnan akan yazo ya kai shi gida dan bayaji zai iya driving d'in......

Yana tare da Adnan a reception yana mishi bayani, sai ga su Ammi on expected hadda Hajja ashe tazo tana ma tare da Ammin sanda ya kira, aiko duk rud'e take jin Takwarallen ta ce ba lafia dake tun zuwansu ta fahimci cikin da take d'auke da shi, Ammin ma ta dad'e da ganewa shiyasa kullum take cikin kiran Aymana tana gaya mata ta kula da kanta sosai dan ita a nata tunanin sun san da abinsu....

"Ibrahima ina ita Balkisun take, meya sameta an kwantar da ita ne, inji dai da sauki?" Hajja ta shiga jero masa tambayoyin ko gaisawa bata bari sunyi ba...

"Eh da sauk'i Hajja kuzo mu Shiga ciki" Adnan yace musu, wannan nurse d'in tana zaune gefenta akan kujera, da murmushi ta tarbe su tare da mik'ewa tsaye tana gaida su, Ammi ce ta samu sararin Amsa mata itama tana maida mata murmushin, Hajja tuni tayi kan Aymana tana salati "oh! Ni Balki mi zan gani meya kumbura mata fuska da jiki haka?"

Kamata Ammi tayi ta zaunar akan kujera "Hajja zauna dan Allah, kiyi hakuri zakiji komai" Mu'azzam d'in yace da ita..

Sallama nurse d'in tayi musu ta wuce, bayan an gaisa ne, ya gaya musu abinda ya faru Wanda ya sani, tare da gaya musu zubewar cikin saidai bai nuna musu rashin sanin cikin ba dan wannan personal ne tsakaninsa da ita, bayaso a gane matsalar su, bare ma ayi blaming Aymanan sa dan yasan Ammi taji ita zata d'orawa laifin gaba d'aya duk da shima da nashi dan yama fi ganin laifin kansa...

"Kai Amma dai anyi shegun yara anan, 'yan iska masu fuskar munafukai..." Kash Hajja dan Allah kiyi shiru ki dena zaginsu bakisan meya had'asu ba" Ammi race cikin rarrashi...

"Wlh Fatima ki fita idona, kedai kinji ciwo wannan 'ya, sam bakiga mugun aikin da suka miki kan 'ya ba? To me zata yi musu illai mugun hali ne kawai da suka gada gurin matsiyatan uwayensu......" Wayyo dan Allah Hajja kiji hakuri".

"Adnan kuje ka mayar da shi gida ya samu ya huta, zan kira Muneera yanzu nasa ta fad'a maka abinci ta bawa Baba Mudi ya kai maka" amsawa yayi ba don yaso ba sai dan shima yasan yana buk'atar ya d'an samu rest of mind...

Family house yace Adnan ya kai shi, tsohon part d'insa ya bud'e ya shiga bayan yace da Adnan d'in baiso Momy tasan yana gidan dan Allah, motarsa ya bayar wa masu aikin gidan dan su wanke mishi, wanka ya sake yi, Allah ya soshi ba duka ya kwashe kayansa ba hakan ne ya bashi damar canjawa, abincin da Muneera ta kawo masa yaci, dake ya gayawa Ammi a nan gidan zai sauka, farfesun hanta da koda ne, sosai yayi masa Wanda ya bashi damar sakin jiki yaci sosai, Ammi is d best mother, imaging kamar muneera ta iya girki haka, malt and milk d'inda aka had'o masa da ita ya had'a da ita, duk da yana, kwanciya yayi minti kad'an kuwa bacci ya suresa..

***********

"Yo ni nace ki boyoni koni nace ki daketa da zaki wani d'oran laifi naga dai duk a karan kanki kikayi komai" tace tana tab'e baki, zuwa gurinta tayi a tunzure tare da cin kwalarta "ni kike gayawa haka? Samiha ni zaki yiwa butulci? Lallai kau yau Yaya zaikai duka matayen nasa asibiti yai ta jinya" rik'e mata hannu tayi "aa me yayi zafi haka malama da har takai ga duka, wai ma meya faru? Yi hakuri sassauto gayamin, ai fad'a ba namu bane muda Muke Neman mafita" ganin tabbas na jaki zataci a gun Samhar dan ta d'ade da sanin tafi k'arfinta, sauke hannun tayi, tare da yin kalar tausayi "Farook ne yace wai daga duk inda nike na wuce gida har sai ya nemeni ya xanyi da Abba?" Janta tayi suka zauna "cool down ma gal, mu samu mu fitan dai zamuyi settling da Farook dan nasan shi da hak'uri" jinjina kai kawai tayi amma bata tunanin zai hak'ura cikin sauk'i dan daga yanayin maganarsa kad'ai zaka gane an hadashi da Bango....

Haka nan suka ci gaba da zama cikin gidan ganin ba sarki sai Allah yasa suka d'an saki ransu hadda cin abincin da Aymanan ta dafa ......

Ba shi ya samu ya tashi ba sai around 3pm, a gaggauce tayi alwala ya gabatar da Zuhr, car key nasa kawai ya suri car key nasa, ya samu motar kuwa a wanke kal, direct clinic d'in ya wuce, ya samu jinin yayi Rabi, amma still bacci take bata farka ba "kai Ibrahima ka gayawa ubanka ne?" Hajja ta tambayesa dan lokacin da suka fito yana kasuwa, Ammi tace zata kira ta tambayesa Hajja dake ta rud'e tace suje dai, ba yadda batai da Ammin akan kira mata shi a waya tace dan Allah tayi hakuri abar zancen nan iya su batason abinda zai tashi wata fitina, kyaleta kawai tayi dan ita bata iya kiran bane...

"Aa Hajja bamu hadu da shi ba amma...." Amma me? Ungo nan kiramin shi" tace rai a b'ace "dan Allah Hajja abar..." Wlh Fatima ki fita idona Idan ke bakisan zafin 'yarki ba ni nasan zafin jikata ko kuwa dan Hashimu baya nan ne kuke so ku nuna mata wariya?"

"Allah ya baki Hakuri Inna ba haka bane, ni rigima ce banaso kin sani"

Kiran mata shi Mu'azzam yayi, ta koma gefe tana zayyana mishi, shi kuma guri ya samu ya zauna tare da zuba mata ido, dake ya saba sosai da Ammi ba wata doguwar kunya a tsakaninsu ya tambaye ta ta tashi ne, ta gayamasa bats tashi ba tun tafiyarsa, jinin kuwa har yayi rabi dake 8hour suka bashi....
Chapter 5 · 0% Book details