← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 34

Sashe 14

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'ago kai Dady yayi da idanuwan sa da suka gama rinewa zuwa ja tsabar bacin rai da kunya "Hajja nayi Dana sani wlh nayi nadamar auren Suwaiba a rayuwa, Yaya kana jin me Suwaiba tayi? Yaya nayi turr da auren Suwaiba, ta cutar dani ta cutar da dangina ta cutar da 'ya'yanta ta kuma cuci karan kanta, Hajja Meye amfanin rayuwa kamar wannan, meye amfanin haka dan Allah....."

"Hmmm Kabiru sai Hakuri amma ni tun ba yau ba nasan duk aje a dawo Suwaiba na taka muhimmiyar rawa gurin tab'arbarewar zaman lafiyar gidan nan, ga yaran su sun bari sakaka ba tarbiya bare mutunci yanzu dai sai tayi mana bayanin Burinta akan mu, meye ribarta idan ta samu ta mulke mu? Ashe har kisa tana iya aikatawa Ashe rashin imanin ta yakai tayi kisa? Meye laifin Fatima Idan ni da Kai da Mahmud da Ibrahim duk masu laifine a gareta, meya sako Fatima a cika, amma koda yake uwace a gun Balkisu shine laifinta to ita Zainab data Sadaukar da rayuwarta agareki ta kaurare ta haukace ta biye miki meye nata laifin?" Tsawa Dady ya daka mata jin tayi shiru ta kasa magana "ke ake sauraro Tauraruwa mai wutsiya amsar ki muke jira"

Sanda ta zabura dan iya zamanta da Dady bata tab'a ganin fushinsa da bacin ransa kamar haka ba, inna inna ta fara "tom...to...." Can't talk stupid" ya sake daka mata tsawa sanda falon ya amsa...

Momy hawayen nadama sosai ke kwaranya daga idanunta ji take kamar ba ita bace a gun tana tuna rashin mutumci da tayi ta shukawa a gidan wa mijinta wa kishiyarta wa surukarta duk akan muguwar shawarar Suwaiba Wanda ko Uwarta bata saurare a lokacin Ashe Ashe Suwaiba iza mai kantu ruwa take mata Ashe bada zuciya d'aya take zaune da ita ba? Ita ta riketa da zuciyar ta d'aya a matsayin mai kaunar ta Ashe Sam ba hakane a ranta ba, lallai idan kana duniya kullum cikin ganin abubuwan mamaki kake da rashin tsammani wannan shine wuta a masaka a maimakon a ganta makera.

Cikin dakewa ta fara magana "komai nayi, nayi ne dan kwatar wa kaina 'yanci idan Baku manta ba, farkon auren mu sosai Zainab da Fatima suka had'a Kansu guri d'aya suka mayar dani saniyar ware, Zainab taja Fatima jikinta ta ware ni, akayi musu kayan daki iri d'aya aka wareni, gashi sun fini ta ko'ina hakan yqsa na kullace su a raina, haka nai ta kokarin cusa kaina ga Zainab amma taki bani dama"

Murmushi ta saki cikin dakewa "Rasuwar Hashim da auren da Ya Mahmud yayi na Fatima ne ya haskaka min hanya ta, Dana Fahimci tsananin kishi irin na Zainab, nan na samu damar ta, nayi ta ingizata tana hawa, lokacin da na gama fahimtar kishi ya gama rufe mata ido sai nayi amfani da hakan na kuma hada da kaita gun Malamai kamar yadda ta hanyar su na samu har na mallake ka, ko ka manta farkon had'uwar mu a school nuna min rashin so, shiyasa nayi yadda nayi har ka aureni, sannan na hana ka kara kallon wata mace da sunan so bare kace zaka kawota, duniya tamin Dad'i sosai abun da kawai ya ragemin na cika burina shine na mulki kowa da kowa a wannan family duk kowa ya dawo karkashin ikona, bawai dan inason Auren Samiha da Ibrahim bane saboda bana sonsa tun farko sannan yazo yana wulakanta min 'yar da nafiso a rayuwa kawai dan tana sonsa ba yadda banyi ba akan a karkato mana da zuciyarsa amma abin ya gagara saboda taurin kansa Abu yaci tura, duk da ina hangen samun cikar burina idan auren ya yuyu"

Nan dai taci gaba da warware duk kullin da tayi tiryen-tiryen har Zuwa lokacin da auren Su ya tashi da zuwa gurin boka da sukayi da Momy akan a lalata auren Aymanah da yadda auren ya juye ya dawo kan Mu'azzam, da yadda tai ta zarya akan a lalata auren dan kawai ta kara dand'anawa Fatima bakin ciki, sannan daga baya ta koma kan Zainab, da yadda takai 'yarta gurin boka dan ganin sun yi nasara da yadda Mu'azzam ya lalata musu aiki sannan tace "kuma wlh tallahi ba Wanda ya isa ya dakatar dani ko ya Shiga tsakanina da burina dan sai na cika burina" tana kai nan ta tashi ta fice daga falon baki d'aya........

Da ido kowa ya bita cike da mamakin rashin imani irin nata bako alamar nadama a tare da ita, Momy zuwa lokacin kukan nadama sosai takeyi tana kaico da biyewa Suwaiba da son zuciyarta da tayi lallai son zuciya bacinta......Ashe Suwaiba ta wuce duk inda take tunanin ta..

Itama Samiha kuka take sosai ta Riga tasan duk yadda ta kai ga son ya Mu'azzam dole ta bar shi, Ashe bata gama Sanin wacece Mahaifiyar ta ba Ashe Ummanta ta wuce duk tunanin ta, mema yasa ta biye mata..gashi ta ja mata mafi girman asara a rayuwar ta.....

_Sorry my friend kuyi hakuri dani abubuwa ne sukamin yawa, cikakkiyar lafiya ma banda ita, pls Ku sakani a addua don Allah, and ina bukatar comments dinku fa, shiyasa ban samun kuzarin typing sosai, aci gaba da gashi😘😘😘😘one love fans_

*Siddiqa ce dai*👌🏻
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*tufafi sune suturarka ta zahiri, imani shine suturarka ta badini, yi kokari ka gyara ciki da waje👌🏻*

Duniya Makaranta✍🏼

*Page* 4⃣3⃣

_______cike da bacin rai, cikin zafin nama Dady ya yunk'ura zai tashi ya bi Umma Abba yayi saurin dakko hannunsa ya mayar da shi ya zaunar, sai lokacin ya bud'e bakinsa yayi magana tun da aka fara badak'alar...

"Me kake shirin yi Kabeer? Zauna har ka samu nutsuwa gaggawa aiki ne na shaidan" sannan ya juya ga Momy da bayan shabar hawayen Dana sani ba abinda takeyi..ita kanta kunyar kanta take bare mutanen da take a gaban su, mijinta, surukarta, kanin mijinta, kishiyarta, da uwa uba yaranta wannan wace irin bak'ar rana ce ranar Dana sani ranar nadama yau tayi kaico da sanin Suwaiba a rayuwa..

"Zainab!" Abba ya kirata, d'ago idanu tayi cike da rauni tayi wata kalar tausayi saidai ta kasa amsawa "ban tab'a tunanin rashin wayon ki da bak'in kishin ki zai kaiki ga shirka ba, Ashe bushewar zuciyar ki yafi yadda nike tunani, Zainab ina kika watsar da tarbiyar da Gwaggo ta baki, meyasa kika biyewa son Zuciyarki har haka, meyasa kika kasa d'aukar kaddara kamar yadda Fatima ta d'auka? Kin d'auka don son zuciya ko wani ra'ayi na auri Fatima ko ita ta yadda ta aureni, wlh babu ko d'aya daba da rashin d'an uwana ba yadda za'ayi haka ta faru, amma kin kasa yadda kin kasa ganewa, kika daura tsana kina yaki da hukuncin ubangiji dan wannan ba yakin Fatima bane da Ubangiji kike yi, duk irin shawarwari da nasihar da nake miki da Wanda duk wani mai k'aunarki ke miki kika watsar, kika ba Suwaiba damar shiga cikin rayuwar ki yadda takeso, tayi amfani da wannan damar tayi ta rura wutar gaba a cikin gidan nan ta haddasa *Ricikin cikin gida* na tsawon shekaru.."

Murmushi mai ciwo yayi "ko zaki iya gayamin tsawon lokacin nan da aka d'auka ina nufin tun da na auri Fatima kika fara gaba da ita wane dadin rayuwa kika tsinta?" Jim tayi meko ta samu na dadi bayan kullum cikin kunci take da jin ana cutar da ita ta maida hankali gurin gaba da duk wani Abu daya shafi Fatima... Katseta yayi, Dan yasan bata da bakin amsawa..

"Amma kinga ita da kullum kokarin ku ya zakuyi Ku cutar da ita ne, tana cikin aminci saboda ta tsarkake zuciyar ta, bata kulle kowa a ciki ba, ta yadda da komai daga Allah ne, ko ta tab'a mayar miki da martani ko kuma ta taba cutar da ke ko 'ya'yanki?" Nan ma tasan aa ne amsar shima shiru tayi sai hawaye kawai take..

"Amma ita Suwaibar da kika yadda da ita kika bata amana da ragamar rayuwarki meye ya biyo baya? Nasan wannan kadai ya isheki darasin rayuwa ki gane ba duka mai maka dariya ne mai kyaunar ka, kamar yadda ba duka mai daure maka fuska ne makiyinka ba, yanzu kin fahimci dariya baso bane, ina burin wannan ya zama darashi agareki"

Shiru kakeji falon yayi tsitt bayan shesshekar kukar masu raunin zuciya ba abinda kakeji, tun daga kan Zulaiha, Samha, Samiha, Nusaiba, Aymanah duk kika suke saidai kowa da dalilin sa na kokawa, Ammi ma zuwa yanzu kukan take Wanda ya garwaya da tsoron Allah da farinciki ranar da ta dad'e tana buri a rayuwa yau gata ta zo mata, tana rokon Allah yasa wannan ne dalilin samuwar zaman lafia mai d'orewa a garesu..

Hafiz ma tunda ya soke kansa bai kara dagowa ba sai hawayen bakin ciki yake zubarwa yana inama Allah bai kaddara masa zamowa d'a a gurin Umma wannan wace irin ranar tonon asiri tayi musu wace irin uwace saidai sanin komai ubangiji ya tsara da sanin sa yasa ya sassautawa Kansa, Hajja ma duk bakinan nata yau ta kasa magana jinjina karfin hali da taurin zuciya irin nasu kawai take a ranta, Ashe inda take tunanin Suwaiba ta wuce nan wannan wane irin rayuwa ne...

Mu'azzam kam na rasa gane yanayin da yake ciki, shi kadai ya barwa kansa sani....

Cikin sabulewar jiki da rashin kuzari Momy taja jiki zuwa gaban kujerar da Abba ke zaune, ta zube guiwowin ta a kasa "Yaya Mahmoud" ta kirashi da sunan da tun suna samartaka take kiransa "yau gani a gaban ka a matsayin k'anwarka kuma matarka, 'yar uwarka, ba dan niba domin Allah da kuma zumunci dan soyayyar da ke tsakanin mu, dan alfarmar zuri'ar mu ka yafemin wlh na gane, na gane kurakurai na tuba dan Allah ka yafemin" sosai zuciyarsa ta karya kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da nadamar ta....

Saidai dole sai gwada yaga idan da gaske ne, shiru yayi mata kamar ba dashi takeyi ba, gun Hajja ta koma ta nemi gafararta tare da neman alfarmar ta saki baki, ta dai yafe mata amma tabar ta da tsakaninta da mijinta, Cike da nauyi da kunya ta kalli Ammi tace....
Chapter 14 · 0% Book details