Sashe 25
Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiri na sosai su Ammi da hajja suka shiga yi Mata kamar wata sabuwar amarya, shima farooq nasa b'angaren hadda sabunta fenti da sauran gyara-gyare.....
B'angaren Umma kam abun ba'a cewa komai, ta dawo goro ko abin saye, wulakanci na sosai takesha a gun matan yayan nata, hadda su habaici da komai, ga 'yan kud'in hannunta ta gama cinyesu, har wayar hannunta ta sayar ta mayar da Nokia rakani kashi, duk kuma ta cinye kudin, dole ta dawo cin duk abinda aka kwaba a gidan aka bata gashi ba koshi take ba, duk tabi ta fita hayyacin ta....
Kawayen da take da masu zugata suna tayi komai ba komai lokacin ta ne duk sun gujeta, sai yanzu ta fara nadama da Dana sani Mara amfani...
Babban tashin hankalinta gaba daya wayar Dady da 'ya'yanta ba mai zuwa kota kira duk a kashe takejin layukan alaman a daina aiki dasu, tashin hankali na sosai ta shiga bata ga miji bare 'ya'ya ga wahalar rayuwa na kaiwa bakin salati ma gagararta yake, bare tayi tunanin zuwa gurin boka...
Tana so taje can gidan ta nemi yafiyar su ta roki arzikin a mayar da ita dakinta ta gane kurenta ba dama, Dan Yayanta ya sheda mata Dady yace muddin ta taka kafarta gidan nan zai tsinke sauran igiyoyin koda yana da niyyar maida ita, kuma ya sheda mata shine ya hana yaransa kusantar ta, dole tasha jinin jikinta dan ya karar da auren ai asirinta ya gama tonuwa...
😅 _Allah sarki Umma ta fara ban tausayi😢_ lol.
*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_
*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
🌎 *Duniya Makaranta* 🌎
_Idan kasha ruwan rijiya kada ka jefa mata dutse a cikin ta, komai k'ankantar alkhairin mutum a gareka kada ka butulce masa_ 👌🏻
*Page* 5⃣4⃣
______kwance take saman faffad'an k'irjinsa tana wasa da bakin lallausan gashin da ke gurin kasancewar suna kebe ne a d'akin baccin su sun baje a bed suna hutawa, bayan komai ya gama wakana yadda ya dace, idanunsa a lumshe tace "Yaya?"
"Uhm Habibty!"
"Yaya na dade banje gida pls tun da case ya kare yaushe zaka kaini tun da ka hana ni fita koda da driver ne, wlh nayi missing nasu"
D'an bud'e idonsa yayi da ke cike da bacci ya kalleta na sakanni "Am very sleepy baby let sleep we will talk after OK"
"Uhm" ta fad'a a tak'aice, tare da kara hugging nasa tightly, shima gyara pillon kansa yayi tare da return her huge back, minti kad'an bacci mai cike da nishad'i yayi gaba dasu....
Basu suka farka ba sai 4 after, zare jikinsa yayi a hankali tare da shiga toilet a gaggauce ya d'ora alwala, ash jalabiya ya zura, sannan ya koma bakin gadon tare da sunkuyawa ya shafo gefen fuskarta, a hankali ta fara bud'e kyawawan kwayoyin idaniyanta kafin ta ware su gaba d'aya a kansa, hannu ya mika mata ta kama kana ya mikar da ita tsaye "asr ta kwace mana muje kiyi alwala kizo muyi kinji" girgiza masa kai tayi dake baccin bai gama sakinta gaba d'aya, hannunta yaja saida ya sadata da toilet sannan ya fitar musu da darduma tare da fitar mata da hijab da zanin da take sallah dasu....
Jam'i ya jata bayan sun kammala yace "kika ce dazun kina so kije gida?"
"Eh mana Yaya" ta amsa masa tana ninke hijab da zanen "kina so muje yanzun?"
Tsabar murna batasan lokacin da ta daka tsalle tare da yasar da kayan hannunta tsakar dakin ta dire a jikin dake yana kwance akan sofa "da gaske My khaleel"
Fuskewa yayi bayan ya riketa sosai yanayin yadda ta fad'o masa zata iya jin ciwo "me haka Aymanah, bana hanaki irin wannan shirmen ba, to an fasa fitar" kara d'aure fuska yayi tamau just like dodonta...
Ji tayi ba dadi, nan take ta koma wata kalar tausayi, tayi narai-narai da ido har kwalla ta taru mata "pls yi hakuri Yaya bazan kara ba Allah" banza yayi mata kuma yaki kallon sashen ta...
Kara rikicewa tayi sai hawaye sharr "pls ya Allah bazan kara ba" saurin juyowa yayi ya kalleta sai ta bashi tausayi, tunani yayi wato ita mace komin girmanta kuka baya bata wahala wala na farinciki ko bakin ciki kona sakarci kona rikecewa..
Kukan Mamar Zakiyya da ita Zakiyyar kanta itama yanzu kukan take saboda kawai yayi mata fushi....
"Is OK banason kukan" ya fad'a yana share mata fuskar amma fuskar sa ba walwala sosai..
"Ka hakura Yaya?"
"Na hakura mana baby ai kema kinsan bazan iya fushi dake ba ko yaya, lafiyarki data unborn nake dubawa ki rage wannan rawan kan yanzu ke babba ce kuma momy to be u'um!" Ya fad'a da murmushi...
Itama murmushin tayi tare da boye fuskarta da tafukan hannayenta "uhum su kunya manya! Bayan kin gama wahalar dani daga dawowa na ko hutawa ban ba, waike fitina"
Zaro ido waje tayi bayan ta sauke hannayenta "kai Yaya nifa kace, Allah Yayan nan ka cika wayo, bayan Kaine....." Dariya ya fashe da ita yadda take maganar da iya gaskiyar ta kuruciya a filin Allah....
"Wannan matar tawa badai kuruciya gashi kuma girma yazo, oh ni Ibrahim jikan Sa'idu uwar zan rena ko 'yar"
"Allah ko Yaya zan rama ni kake kira 'yar reno ba?" Tashi tayi zata wuce tana hura hanci, cinye dariyar yayi tare da riko hannunta da sauri " oh wasa nake fa Maman baby, gobe ma zamuje pre-natal kin tuna" tura baki tayi gaba bata tanka ba...
"OK shikenan kanki kika yiwa tun da bakya magana barin tashi nayi tafiyata gida ni d'aya.....
Da sauri tace " Allah na tuna Yaya ai gobe zamuje" lakuce mata hanci yayi "my fitina baby yi maza ki shirya muje time is going!"
A hankali ta tashi ba wannan rawan kan duk da dad'i takeji a ranta na sosai saidai bataso tayi abinda ran Sahibin zai baci, murmushi ya saki tare da Shafo Sumar sa....
"Silly gal, koman ta yayi ta had'u ta ko ina" ya fad'a a ransa......
**************
"Allah Akbar! Allah sarkin hikima Salmanu yau kaine a gabana? Yaushe ka dawo kuma ina kake tsawon lokutan nan?"
Sosa keyarsa yayi tare da k'ara sunkuyar da kai "Abba na kwana biyu da dawowa, wlh Abba nima basan meya sameni ba lokaci d'aya naji na tsani auren da Aymanah kamar yadda naji Zariya tamin matukar Zafi, Abba Sokoto naje nayi ta rayuwata ni d'aya cikin kunci bana ko son tuna gida da komai daya shafi rayuwata, tsawon watanni Shida, sai kuma kwatsam rana d'aya naji na dawo kamar yadda nike naji cewar gida da kewar Aymanah, Abba wlh bansan meya faru ba"
"Aa Salman ka dena damun kanka nasan ba laifinka bane daga baya amma kam a gaskiya farkon lamarin raina ya sosu har sanadin haka na had'ata aure da d'an Uwanta a ranar da akayi niyyan d'aura maka aure da ita, amma kuma daga baya dana gane Ashe ma matsalar daga cikin gidana ta fito...." Nan ya labarta masa komai daya faru tare da cewa kayi Hakuri Salmanu wannan kaddarar rayuwarku ce a haka dan Allah ka yafe musu suma rudin zuciya ne dana shed'an suka ingiza su".....
"Babu komai Abba na d'auki komai a matsayin Kaddara Dan naji labarin komai daga Gida(dake Abba ya sanar dasu komai game da abinda su Momy sukayi tun lokacin da abin ya bud'e) Abba har ma nayi aure da wata 'yar uwata, dama dai nazo ne na gaida kai kuma na sheda maka dawowa ta"
"Kai mashaa Allah, madallah Salmanu nayi farinciki, amma shine Alhaji bako gayyata bayan an riga an zama d'aya kodai sun kullace mu ne?"
"A'a wlh Abba ko daya Abin ne yazo a gaggauce bako wani shiri akayi shiyasa nace kar a sanar muku tun da lokaci ne kuranne in yaso daga baya nazo na kawo muku matar Ku ganta, ai tare muke tana ciki"
"To to to Madallah babu laifi Allah yayi muku albarka baki d'aya bari nasa a kawo maka abin tabawa in yaso sai a kiramin surikar tawa mu gaisa daga baya...."
"Aa Abba ai da ma ka barshi...."
"Kul karka soma nan ba gidan Ku bane kam, kusha hanyar sannan kace haka..." Sallamar su Mu'azzam ce ta katse masa maganar sa, suma isowar su kenan suka yo tsinke nan su fara gaisawa da Abba..."
Kallo kallo Salman da Mu'azzam suka shiga yi, shi yana masa kallon sani shi kuma yana mamakin yadda aure ya kasance tsakanin su yadda ya fahimci babu shi a tsakanin su a lokacin da suke tare, itama kallonsa take da mamaki...
Murmushi ya saki tare mika masa hannu, shima salman d'in mayar masa martanin murmushin yayi suka yi musabaha...
Fad'ad'a murmushi Abba yayi yana amsa gaisuwar su, a sanyaye Aymanah ta gayar da Salman din, jin yadda Salman ya kama sunanta rad'am a bakinsa yasa Mu'azzam binsa da kallon tuhuma kafin yayi magana Abba ya tare sa...
"Baka ganesa bane Ibrahim, shine fa wanda ya tashi auren Allah bai nufa ba...." Nan ya basu labarin sa a takaice, fatan alkhairi Aymanah tayi masa bayan ta jajanta masa tayi ta wuce ciki da sunan zata taga Amaryarsa lura da yadda yanayin yayan nata yake duk da ita kad'ai ta fahimci yanayin saboda tsabar sanin duk wani motsin sa tasan ba abinda ke cinsa a gurin bayan kishi, shiyasa ta sulale tabar gun gudun bacin ransa.....
A falon Momy ta same su gaba daya har su Nusee da Amira sun zo Aunty Samha ce kawai babu da yake ta koma gidanta, gaida su Momy da Ammi, tuni Momy ta yalwata Fuskar da murmushi taja Aymanan jikinta tana tambayar ta lafiyar ta da gida, Tsuru Samha tayi tana kallon su cike da Sha'awa tana da bata biyewa son rai ba da yanzu har ita haka Momyn zata yi mata, tasan sosai Momi ta nuna mata k'auna ta gaskiya su kuma suka yaudare ta, ko yanzu tana mata saidai ba kamar lokacin da take tare da d'anta ba "hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta shiga maimai tawa a ranta tana Neman tsarin Shedan, a yanzu bata k'aunar abinda zai saka ta k'untata wani bare koda ta fatar baki bare jininta....