← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 34

Sashe 10

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana aje su ko gidan bai shiga ba yace zai koma, aiko nan Hajja ta hau bakinta " Dama bak'ar zuciya da bak'in halin da kake gwada mata kenan a gidan shiyasa har yau kuka kasa samun zaman lafia, yo in ba haka taya wannan 'yar karamar tasan yaren zubar da ciki in ba a bak'in halinka ne yayi niyyan tunzurata ba, wlh kadai canja dan wannan ba yi bane" tun da ta fara zuba ya zuba mata ido har sanda ta sauke aya sannan yace shi zai tafi idan ta gama..

Kama baki tayi tare da fad'in "jeka ina nan zaka dawo ka sameni" itama ta shige ta barshi anan Aymanah kam har ta d'an huta....

"Hmmm Yanzu nasan Nina haifeki nasan kin had'iye nonon baki zubar ba, kada ki damu da wani cin maganinsa da barazanar su uban nan Ku, duk ki d'auke su a matsayin busar sharo, aikinki yayi kyau yanzu zamu D'ora daga inda muka tsaya, wannan wata dama ce da aikin mu zai tafi yadda mukeso" umma tace Murmushin mugunta kunshe a fuskarta...

Tasowa tayi tare da dafa hannun kujerar da Umma ke zaune "amma ta yaya kike ganin abubuwa zasu zo mana da sauki bayan kina ganin yadda komai ya kwab'e Umma?"

"Hmmm! Kedai ki zuba ido kawai kisha kallo ai yanzu kin d'auko hanyar babynah"

Itama murmushin ta saki tana wani juye baki gefe "kina nufin kice zan mallaki Ya Mu'azzam na juya shi yadda nikeso?"

"More than dis Baby ai har da ubansa da uwarsa sai mun juya wannan karon"............

_lallai mai sonka shike bibiyarka yasan wane hali kake ciki, masoyana nagode sosai da add'u'oinku a gareni, nagode da kulawarku Allah yabar zumunci, maryam Abdul dinku tana muku fatan alkhairi a koda yaushe, Allah yasa mu dace duniya da Lahira..._

*Maryam Yusuf Zango(Ummu khady)*

*Bilkisu Hashim(mom zee)*

*Bilkisu Zamfara(maman Nana)*

*kun kasance wani sashe na rayuwata ina matuk'ar yaba karamci da k'auna irin taku, baki bazai iya fad'ar yadda nike jinku a raina ba, Allah yabar zumumci.....*

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*_Zunubi d'aya shedan yayi Allah (S.W.T) ya Kore shi daga cikin aljannah, zunubi d'aya Annabi Adam (A.S) yayi Allah ya fitar dashi daga cikin aljannah, mu kuma da dinbin zunuban mu muke son shiga cikinta🤔, Allah ka cece mu badan aikin mu ba sai don rahamar ka👏🏻_*

Duniya Makaranta✍🏼

*Page* 3⃣9⃣

_______kwance take kan three seaters idanuwanta a lumshe saidai ba bacci take ba, da sassafene sosai dan garin ko gama haske bai ba, tana sanye da kayan bacci Pyjamas pink and white gashinta na cikin net as usual, kaga ganinta kasan tayi nisa cikin tunani........

Fuskarsa take hangowa, murmushin sa, dariyar sa, fushin sa, tsare gidansa, takunsa, iya adonsa, k'amshinsa mai fizgar numfashi, tashi zaune tayi tare da ware idonta gaba d'aya "meke damuna ne wai? Meyasa zan damu dashi har haka?" Ta fad'a a fili...

Hannu tasa ta shafo cikin ta, cike da shauki, ya akayi ta rasa gane tana d'auke da cikinsa har sai bayan ta rasa shi? Amma kuma taya zatayi tunanin yin ciki bayan sau d'aya tak suka tab'a had'a makwanci dashi, koda yake hukuncin Allah ne samuwar ciki, duk da taga many changes a tare da ita kamar rashin ganin period nata saita d'auke shi a matsayin tsallaken wata ne, to amma yawan bacci da kasala fa, ga ci kamar gara da kwadayin tsiya amma duk hankalinta bai kawo nan ba, d'an tabe baki tayi tare da cewa "gara ma daya bare ai" tashi tsaye tayi tare da d'ora hannuwa akan kirji tana zagaye falon a duk lokacin zata rufe ido shi take hangowa, me kenan?

Kasa samun cikakkiyar nutsuwa tayi wannan ne karo na farko data farajin tanaso ta koma Kano idan ta taho Gwarzo a kwanaki ukun da tayi bata ganshi ba, kodai tana so ta bashi Hak'uri kamar yadda Ammi ta umurce ta shiyasa ta kasa samun nutsuwa (hohoho su Ayma an shigo system🤪).

Sake zama tayi tare zama tare da dafe kanta, tunani ta shiga yi tunanin rayuwar su ta baya, tun farkon saninta dashi ta sani tun tana k'aramarta yake mata kwarjini, har koma tsorata ta, tana iya tuna lokacin da take nan Gwarzo gurin Hajja yadda take tsorata ta da kira mata sunansa idan tana kukan banza ko wata barna ko kuma tana rigima, ba zata manta lokacin da take kano ba ko magana take idan yazo gun yanzu jikinta zai d'auki rawa ta kuma rufe bakin kenan, tana tuna yadda yake matuk'ar tsaurara musu da kuma rashin wasa dasu, da yadda yake dukansu idan sukayi laifi, duk da yakan d'au lokaci kafin ya taho k'asar, hakan bai canja komai ba daga halinsa, mace d'aya ce ta sani yake kulawa iya saninta wato Aunty Samiha ita d'in ma bata wasu lokuta yakan murje ido yayi mata halin nasa, to Amma meyasa ita ya bata kyakkyawar kulawa yake nuna mata tsatsan so? Duk da aje shi a matsayin yaudara amma meyasa? Da gaske yanzu tana son jin dalili amma waye zai gaya mata tun da ta hanashi damar haka tun lokacin da yakeson sanar da ita, tunawa da maganganun Amminta tayi...

" _Nafi kowa sanin kaunar da Mu'azzam yake miki, nafi kowa sani waye Mu'azzam, sanin da nayi masa ko mahaifiyarsa ba ta sanshi haka ba.....kada ki manta jinin jikinsa ke yawo a jikinki_ karajin maganganun Ammi take ji a kunnuwanta kamar yanzu take yin su, ta sani akwai shakuwa sosai tsakanin Ammin ta da Ya Mu'azzam d'in har mamakin yadda suke fira sosai take da Murmushi da komai, ta kuma San duk rikicin da ake cikin gidan bai tab'a saka bakinsa ba, saima nuna kamar baisan komai ba da yake yi, tabbas Amminta tasan Yayan nasu sosai Amma meyasa ita ta kasa gane komai, meyasa ta kasa yadda dashi, har yanzu ta kasa yadda da sonta yake duk da zuciyarta ta gama yadda da gaskiyar kalamansa da aikinsa, to idan baso bane meyasa zai bata jininsa a dai2 gabatar da zata iya rasa ranta, kuma ai Amminta ba zata tab'a gaya mata k'arya ba.......

"Aymanah!" Hajja ta fad'a da k'arfi tana girgizata "ke lafia me kike tunani haka tun dazu inata magana shiru" saurin tattaro nutsuwarta tayi tare da k'ak'alo murmushin yake tana basarwa...

"Hajja dan Allah kibar ni zafin nan haka, haba sai kace wacce ta haihu da gaske" tace tana turo baki "yo meye marabin dambe da fad'a kam ai duk ana tare, ke banda ma rashin kunya yarinya ana miki gata kina wani iyayi so nake na kwato maki girma gurin wancen dayan shashashan amma dake kema 'yar uwarsa ce shine kika min iskanci shiyasa ai Fatima ke cinye miki mutumci dan ba laifi kin fitsare kema, dallah ni tashi ko ta gwada miki tsohon kashi yanzu er neman rub'abb'iya kai" sanin halin Hajja yasa ta mik'e tana zumb'ura baki tana gunguni..

"Koma meye kiyi tayi ba abinda za'a fasa eheee"......

************

" Wash! Umma wlh na gaji wai har yanzu bamu kai ba?" Samiha ta fad'a tana kama k'ugu, gyalen tuni ya dawo a hannu, harara uwar ta balla mata "awoki yarinya keda ake shirin yi miki gata shine zaki fara kiran gajiya, ni kuma da nake zaman zuwar maki kullum nace me kam? Kinga in zaki kama jiki ki kama mu haye wannan dutsen idan ba haka ba kece ciki bani ba, kindai San halin mijinki sarai kinfi kowa sanin shegen taurin kansa da bahagon ra'ayinsa" dutsen ta kalla ta sauke numfashi...

"To Umma mu tafi" ta fad'a cikin juriya da daurewa abinku da ajibota duk tayi wata iri da ita 'yar tafiyar da sukayi daga inda sukabar motar su, haka suka haye dutsin sai a sannan suka hango 'yar bukkar ta mai gobe da nisa, hakan ne ya kara ma Samiha k'arfin tafiyar.....

Tun da ya d'ora idanunsa akan Samihar yaji yawunsa sun tsinke sai wani shu'umin kallo yake binta dashi, itakam wani abin kyankyami take ganinsa Sam baida kamar kwarai sai wani kauda kai take har suka gama maganar su da Umma, anan yace mata ta jirasu a waje zai had'a mata wasu magunguna a jikinta, cikin jin dad'in hakan su zai cimma ruwa Umman ta fita ta jira su waje, tana fita ya fara matsawa kusa da ita itama kuma tana ganin haka ta fara ja da baya cikin tsoro, tsawa ya daka mata...

"Ke! Ki nutsu anan ba'a yiwa aljanu gardama kika kara matsawa daga nan fushin Aljani dan tsirku zai sauka a kanki kibi duniya, ki godemin tunda har kika kasance cikin masu sa'a Aljani dan tsurku ya yaba dake yace zaiyi miki aiki da kansa akan mijinki, amma dole sai kin bamu had'in kai hhhhhhhhhhhhh" ya kece da wata mahaukaciyar dariya...

Haka dai ba imani ba tsoron Allah ya samu ya tumurmuje ta yadda ransa yake so ba tare da wata soyayya ko lallab'awa ba, aiko ta gayawa 'yan garinsu ga azababben warin jikinsa kadai ya isheta, sannan ya gargad'eta ta yadda ta gayama wani koda uwarta ne aikinta ya rushe, umurnin gyara jikinta ya bata sannan yace ta kira masa uwarta, bayan tazo ne ya shaida mata zasu ci gaba da zuwa na tsawon mako ana mata wanka da magunguna, zare ido Samiha tayi kirjinta kamar yayi tsalle ya diro k'asa tsabar kad'uwa fad'i take a ranta shikenan tata ta kare kuma(hmm ai baki ga komai bama tun da kika zabi hanyar sabawa mahaliccin mafi munin sabo a matsayin hanya mai b'ullewa, Ya waduud kayi mana tsari da tsarewarka ka karemu da kariyarka da rud'in Shed'an da kuma na zuciya Ameen)

A hanya taji kamar ta fad'awa uwar ta abinda ya faru sai kuma ta tuna da gargad'in bokan dole ta kama bakinta saidai kam tasan ta banu ta kuma kad'e har ganye, saidai tunawa da mallakar Mu'azzam da zatayi ta juya shi yadda takeso yasa taji zata jure duk wuya har taga ta cimma burinta....

Da Hafiz suka fara cin karo shima isowarsa kenan, da kallon mamaki ya bisu "Umma daga ina haka da tsakar ranar nan?" Harara ta watsa masa
Chapter 10 · 0% Book details