← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 34

Sashe 33

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bunch of Surprise wai can na hango *Marraha fans, Mom zee, Maman nana, kwalliyan Aymanah sune kan gaba, sai dibar rengem ake, dear na, namecy nah, Ummu Annur, sweet sis 'yar inyass, sis mery, bilkis gudaji, dota na Ramlah Aysha D, Ummu Ismail, Hafiza, Ummu nasreen, Ummu jabir and rest (Allah kuna da yawa sorry wadanda ban kira ba duk inayinku wlhy😘)*

Wow! Sai ga *Maman Ussey novellah, khairy B-b, sis na Eshart kadir, maman husna, Shamciya, Jidda, mr Dz, Ummu Ismail and rest (heart you all)*

Au Ashe da sauran wata zugar *Hausa novels, Sweery novel, jinina fans, Duniya Makaranta 2, Mutattauna mata, Aminan juna, soyayya da shakuwa, muhphat dogo novel, zumunci group and rest, _Muz'Aymah_ na godiya da halattar bikin cutie su da kukayi suna muku fatan komawa gida lafiya Amin*

_Allah ya raya Zainab (eynas) akan sunnah Ameen_

Haka aka watse taro lafiya cike da farinciki da annushawa, Eynass alkunyar da suke mata sai girma take kamar ba itace 'yar cas d'innan ba, ta fara barakallah abinta yayin da tsantsan kyanta ke kara bayyana sak Mu'azzam inka cire idon da yatsu da tayi na Aymanah, cute dai da ita kamar yadda Abbinta ke kiranta....

Su Hajja, Momy, Umma sun dage gurin gyaran Aymanah cike da bai musamman Yadda suka ga Angon k'arnin ke rawar kai tuni ya busar da idanuwansa ya mayar da Momy wata kakarsa baya jin nauyinta Sam, sai kunya kawai yake saka Aymanah a gabanta ko a jikinshi, Ammi kawai yake kunya shiyasa itama bata zuwa inda suke...

Watan su biyu suka koma Wanda yayi dai-dai da haihuwar Nusee ta sunkuto saurayinta mai kama da ita Wanda ya amsa sunan Dady suna kiransa da Farhan, nan ma an rakashe an gurji biki, saura Meerah, da Aunty Samha, Samiha ma an samu ita da Fauziya amaryan Uncle salman sai fatan sauka lafiya.....

Sai cillata sama yake yana cafewa itako sai wangale baki take dan ta bala'in saninsa kamar me, muddin yana gida to shine Nanyn ta, ita Aymanah har mamaki take yadda yake cire mata pampers intai kashi ya wanketa tas, ba ruwansa, wani sa'in ma idan an barta da pant tasha iska tayi masa fitsari wani sa'in har kashi yin masa takeyi, tumbud'i ai yasha ba adadi dan wani lokacin sai ya d'agata ta zubo masa abinsa a baki amma Sam baya nuna damuwa ko kad'an, ita kam ba abinda zatace da Allah sai godiya wannan baiwar da ni'imar da yayi mata wacce ba kowa yayi wa ba, kuma badan tafi kowa ba ni'imace kowai daga garesa.....

Zama tayi gefen tare da aje bowl d'in Fruit salad, data hado musu a centre table...

"O'O Abbi da cute d'insa kuna sha'aninku fa" kallon ta yayi tayi masa kyau cikin shigar kananun kaya jean and top, tayi ma kanta wani irin style kamar wata 'yar Baby...

"Hmm! Kina dai Sha'aninki Ummi, wannan swagg haka duk dan a tada hankalin Innocent Abbi ne?" Dariya tayi "nidai ba ruwana! Uhum Yawaa Abbi ya maganar karatun nawa?" Ta fad'a cikin narkewa da tausasa harshe...

"Oh kinga fa Shaf na manta bari Nazo yanzu" yace yana mik'a mata Zee dake zillon zuwa gurinta tasha Mama.......

_Second to the last page inshaa Allah_

*Siddiqa ce*
[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

🌎 *Duniya Makaranta* 🌎

_idan ka saki hawayenka akan filo, to ka sake su ne a banza, sake su akan tabarmar sallarka, to idan kayi haka ka kai kukan ka gurin mai share maka su👌🏻_

*Page* 6⃣0⃣

________d'ago ido tayi ta kallesa bayan ta gama duba tarkacen visa da passport d'insu na tafiya Saudiya, Hadda Admission latter d'inta wato yana nufin a can zatayi karatun, dama yana satar kallon ta yaga me zatayi, sab'anin tsallen farinciki da ihu da yake tunani daga gareta sai ya yaga sabanin haka, fuskar dai ba yabo ba fallasa ga kuma kallon tuhuma da take masa.....

Sabira ya kira tazo ta tafi da Zee sannan ya juyo yana fuskantar ta da alaman tambaya "yadai Habibty? I seen like ur not happy! why?"

" Is Not exactly what I mean, but Yaya like ka zabi iyalanka akan kasarka kenan, yanzu it is pair! Ka aje aikinki na taimakon k'asarka saboda kawai ni meyasa ba zanyi karatun anan ba? Kana tsoron wani Abu ya same mu ne? To idan mun tsallake mun bar k'asar what's up iyayen mu da 'yan uwan mu, al'ummar k'asarka fa?" Ta karasa fada cike da damuwa..

Hannu ya saka ya kama hannayenta duka biyu tare da kallon cikin idonta "is not my intention at all Baby, nasan kaddara na yadda da ita, kuma nasan no way to run away from our destiny but what I want u to know is, nima karatun zanje na k'aro yadda zan k'ara samun experiences akan aikina, ina kishin k'asata fiye da tunanin ki Aymanah, saidai hankali na zaifi kwanciya muje can d'in so pls try to understand me I'm selfish at all, about iyayen mu kuma da kike magana nasan ba abinda zai same su, kodai kinaso kicemin kin manta da waye iyayen namu, sufa suka haifemu suka rene mu, kuma suke karemu tare da taimakon Allah, mezai sa kiyi tunanin akan dan bama nan zasu cutu, pls ki cire wad'annan tunanin a ranki, I know ke d'in ta daban ce, bakyaso abinda wani zai cutu a dalilinki so believe me ba abinda zai faru inshaa Allah okey" duk cikin taushi da sanyi yake maganar...

Murmushi ta sakar mishi tare da Runtse hannunta sosai a nasa, tana jinjina Sanyi da sauki irin nasa, da wani daban ne aida yanzu ta gama kwab'e musu, watakil ma hadda duka tayi wasa "Madallah! Da kai miji na gari mai karanci da kawaici, nagode da fahimtar dani da kayi a siga mafi kyau, ina rokon ka yafemin akan rashin fahimtar ka dana pls forgive me? I understand you Hayat Al-Rouh"......

Shima martanin murmushin ya mayar mata tare hugging nata tightly " I done nothing wrong Habibty! Inasonki kamar yadda halinki da ke k'ara nutsar dani cikin k'aunarki, ke k'arama ce da tunanin Manya, 'yar kwaila ta" ya karashe da sigar tsokana.....

"Uhum um! Zaka fara ko Yaya, Allah zan koma maka kwailar kuwa!" Ta fad'a tana dukan k'irjinsa da hannayenta bayan ta cuno baki gaba cike da shagwaba....

Rik'e hannayenta gam yayi yana dariya "u see jifa me kike yi yanzun, ki dage dayi har cutie na ta girma ta tayaki" harara ta watsa masa tare da Murgud'a baki, tare da mik'ewa tsaye tana hura hanci.....

"Kuma ma an fasa maka tausa yau kaje cutie taka ta maka" dariya ya fashe da ita hadda kwanciya akan seat d'in dan tsayin da tayi da yadda take girgiza ba karamin dariya ya bashi ba uwa wata matashiyar 'yar dambe......

"Allah sarki! Bawan Allah Abbin cutie, to ni bara nazo nayi maka special one irin eh...." Ya k'arasa yana kashe mata ido tare da yunkurin mik'ewa, aiko k'afa me naci ban baki ba, ta runtuma da gudu part d'in, hadda banko k'ofar.....

Dariya ta bashi, saidai murmusawa kawai yayi tare da shafo sumar kansa Wanda na fuskanci is part of his harbit "silly gal" ya fad'a tare da jingina bayansa a kujerar yana lumshe idanuwansa.........

**************

Cikin sati biyu tafiyar su ta kankama, bayan an kammala bikin Ameerah wacce ta haifo Fatima Zarah(anyiwa Ammi takwara) suna kiranta da Zarah.

Cike da so da kewar zuri'arsu suka yi musu b'ankwana bayan sun sha Addu'o'i daga kowane b'angare tare da fatar samun nasara.....

Haka suka bar 'yan uwa da Masoya da k'asar su ta haihuwa suka Lula Saudi Arabiya, inda zasu Zauna a birnin *Riyadh*.......

_🙋🏼‍♀safe trip Muz'Aymah😍👨‍👩‍👧_

*Some years later........*

*Saudi Arabia*

_Riyadh_

"Abbi! Abbi!! Abbi!!! Boyeni bayanka, boyeni Abbi zata dakeni ne" kyakkyawar yarinyar mai zubin Larabawa cikin shiga mai kyau ta Alfarma, dogon gashin nan baki sidik yasha adon beats da ribbons sosai just like take away, a k'iyasce zatayi 4year and half, duk cikin yaren larabci take maganar da siririyar muryarta irin ta yara....

Abbin nata dake zaune kan resting chair cikin wani ni'imtaccen lambu Wanda ke fitar da sanyayyar iska da k'amshi mai kwantar da rai, yana duba wasu documents, idonsa sanye da siririn farin glass, yana sanye da rigar ciki fara kal ta suit da wandon, ta saman na rataye a hannun chair d'in, saurin ije documents d'in yayi tare da janyo yarinyar ya zagayo da ita gabansa tare da zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma.....

"Wato kin tsokano Ummi ko cutie?" Ya tambaye ta yana tsareta da ido, yayin da tayi fiki-fiki da manyan fararen idanuwanta alaman rashin gaskiya....

Kafin tayi, ta bud'i baki saiga Ummin ta bullo ta k'ofar da yarinyar ta fito, sanye cikin fararen kaya irin na ma'aikatan jinya, ta d'ora bakar abaya kai irin ta larabawa, guntun farin hijab a wuyarta, Fuskar a d'auke hannun ta rik'e da 'yar bulala, tana tunkaro su, sai harara take aiko musu da ita...

Murmushi Abbin ya saki ganin yadda cutie ta kara k'ankamesa tana zare ido tana kallon Ummin nata, d'agata cak yayi ya d'ora a cinyar sa tare da rungume ta sosai......

"Allah Abbi yau ba wani bambancin launin fata da za'a nunamin fa, don yau sai wannan marajin cutie taka ta ji a jikinta, duba fa kaga, dawowa kenan amma wai sarkin bannar harta yagamin note book d'in da mukayi presentation yau haba Allah kawai ka barni na dake ta ko zanji sauki sauki"

Tun da ta fara magana yake kallon cikin idonta ta bakinta harta karasa, murmushin Fuskarsa ya k'ara fad'ad'awa sannan ya kama k'unnuwansa tare da rausayar da kai "Ana ahsif Ummi(yi hakuri Ummi) pls so sorry Ummi, a dai yi hak'urin nan da aka saba yi mana d'an Allah"

"Gaskiya nidai Aa Abbi nidai ka barni kawai na daketa Allah Zuciya ta har zafi takeyi" kallon ta yayi da kyau kuma da gaske a zuciye take dan da iya gaskiyar ta take maganar...
Chapter 33 · 0% Book details