← Book details Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Zuri'a Daya Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

By
_Maryam Abdul_

*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*

*An karb'o daga Abu Huraira(R'A) yace Manzon (S.A.W) yace "Allah madaukakin sarki baya duba ga jikkunan ku da surorin jikinku saidai yana duba kawai ga zuciyoyin Ku da ayyukan ku..*

Husnul Muslim👌🏻

*Page* 3⃣0⃣

_________kara matseta jikinsa yayi tare da fara hura mata iska cikin kunnuwa cike da salon jan hankali, yayin da ita kuma tayi lakwas jikinsa jikinta ya fara mutuwa sai zuciyarta dake aikin harbawa da sauri-sauri kamar wacce tasha gudu, ido a lumshe dan Sam ba zata iya d'aukar zazzafan kallon nan nasa ba.....

Hannayensa ya saka ya fara zagaye sannan jikinta dasu cikin kwarewa, a kan lip d'in ta ya tsayar da idanuwansa da suka fara sauyawa daga ainihin kalar su zuwa kalar shauk'i, hannunsa d'aya ya saka kan lip d'in yana murzawa sannu-sannu murmushi yad'an saki mai sauti tare da aza nasa lips d'in kan nata, a firgice ta ware idonta akan nasa tare da tattaro sauran kuzarinta ta turasa, baya yayi tare da fizgar ta da k'arfi ta biyosa suka zube kan bed d'in kamar wasu kayan wanki, k'ok'arin mirgina wa tayi daga jikinsa yayi saurin rik'eta gam da hannu d'aya tare da zuba mata idanuwansa gaba d'aya da suka gama narkewa da tsantar k'auna da sh'aukin ta, itama idon ta k'ir a kansa duk da iya daurewa tayi akan kallon nasa Dan sosai wasu sinadarai da batasan na miye ba ke fita daga idanuwansa suna sukar nata idon ta, hannayensa yasa ya zagaye ta tare da janta ta fad'o gaba d'aya kansa sannan yayi turning d'inta ta koma k'asa, ya dawo sama, kwaba fuska tayi bayan ta rintse idanuwanta gam, dai-dai kunnenta ya rad'a mata "I'm in need of youuuuu plsssss may u help me??" ...

Girgiza kai ta shiga yi kamar kad'angaruwa tana so ta turawa ko ta samu da ta zame jikinta dan ta gama tsorata dashi bata k'aunar sake faruwar wancen bak'on al'amarin na wancen ranar a kanta, tana matuk'ar tsoron lamarin da iya gaskiyarta, saidai tarkon da ya sakata na gaske ne wanda zaiyi mata wahala ta iya kwatar kanta daga gareshi "no...no pls I don't... want it! Pls let be.... alone" ta fara cikin tsoro da rawar murya tana ci gaba da turasa, hawaye sun fara biyo fuskarta "OK..OK...karkiyi kuka ya isa, ba abinda zanyi miki ki barni kawai naji dumin jikinki dan Allah?" Shiru tayi masa dan ita kam bata yadda da ba abinda zaiyi mata ba, jin shirun nata ne ya sakashi kwanciya dakyau gefenta tare da janta jikinsa ya d'ora kanta a k'irjinsa, hannu ya saka ya share mata hawayen tare da ja musu blanket d'in, dake yanayin garin da sanyi ansha ruwa, kanta ya fara shafawa a hankali, yana tofa musu addu'a, har bacci ya kwasheta zuciyarta na cike da tsoronsa, saidai samuwar body contact d'in nasu ya saukar mata da nutsuwa sosai a cikin baccin sai Jan numfashinta tace hankali kwance.....

Ido ya zuba mata yana kallon yadda ta k'ara yi masa kyau da baccin, ba laifi yad'an samu 'yar nutsuwa kasancewar su a tare dumin jikinsu ya had'u guri d'aya, yana cike da zazzafar k'aunarta da shauk'in kasancewa tare da ita, saidai he can't force her at any cost, yana so ta gasgata k'aunarta yake ba sha'awarta ba, yafiso yayi komai cikin amincewar ta da yardar ta, he wish to see dis day in his life, baisan sanda murmushi ya sub'uce masa ba yana cikin burin rayuwarsa ganin ranar da Aymana zata fara sonsa koda kad'an do yana hango burbushin son nasa a kwayar idon ta saidai ba lallai ta fahimci tana sonsa d'in ba....

Yakai kusan to 1 bai bacci ba daga k'arshe ma tashi yayi yaje toilet d'in ta yayi wanka tare da d'auro alwala yazo yayi nafila kamar yadda ya saba, saida yaji bacci ya fara kama idonsa sannan ya shafa addu'o'insa wanda mafi yawan ciki na neman had'in kan Zuri'ar tasu ne da kuma na neman soyayyar Bilkisu gimbiyar mata.lol.

Kwanciyarsa ba wuya bacci yayi gaba dashi mai cike da d'adi da mafarkai masu dad'in gaske Suna cikin good time shida Aymanarsa a duniyar su su kad'ai...

Samiha iyayen lab'e yaukam yanda taga dare haka taga rana tasha kuka kamar ranta zai fita, dan gaban idon ta ya shiga part d'in Aymanar bai kuma fito ba wanda ya tabbatar mata a can ya kwana suna tare, yau kam takai k'arshen lab'e dan shi Sam ma ya manta ya dura mata tab din bacci aiko taga ni ganin idon ta..

"Meya sameki my Meeha, Meya sameki a idanu kuka kikayi me aka miki?" Ya shiga jero mata tambayoyin lokacin da yazo tayar da ita tayi sallah, tana zaune tsakiyar Gado ta jingina da gadon idon yayi mata luhu-luhu alaman tasha kuka, da ido kawai ta bishi, saurin dakatar dashi tayi da hannunta lokacin da yazo zai tab'a ta "karka ka kuskura ka tab'a ni, mayaudari, makaryaci, maciyin Amana" ta fad'a cikin k'araji da tsawa, tsayawa yayi chak yana binta da ido cike da mamaki..

"Wato nika rainawa hankali kake kiranta kwaila a gabana shine kuma ka iya lallab'awa ka shige d'akin kwailar kake nuna mata soyayya saboda yaudara, ka nunamin ba itace gaban ka Ashe dama yaudara ta kake, shiyasa take iskancinta iya son ranta baka magana Ashe wato taga gadon baccinka ta gama ganin girmanka, Ashe kai....."

"Ke! Dakata!" Ya daka mata tsawa, tare da murtuk'e fuska yana binta da kallon kin ma Renani.

"Dama ta taba zama na gaya miki bana sonta? Kona gaya miki bazan shiga dakinta ba? Manta gaba d'aya, d important thing daya kamata ki sani shine keda ita matsayinku d'aya a gareni duk aurenku nake soyayya kuma ni nasan wa nafiso a raina, kika kara gayamin banzar magana akan wannan zancen zan shayar dake mamaki dan na fahimci sam baki gane ina miki kara bane" yana kai nan ya juya ya fice cikin b'acin rai, K'ara rushewa tayi da sabon kuka lallai tana cikin bala'i meye mafita, ko Sallar bata tsaya yi ba ta dannawa Ummanta kira "dota lafiya sassafen nan" kuka ta saki "oh dota, Mu'azzam ko?" Eh " ta fad'a cikin kukan "ok Bari zan kiraki anjima, idan Dadyn ki ya fita" daga nan sukayi sallama, sallar da batayi ba kenan wai ita tana cikin damuwa (wawiya ga gun da zaki samu warakar damuwar ki a sauk'ak'e kin tsallake, subhanallah)

************

"Dota gayamin menene matsalar? daba An hanamu zuwa gidan ku ba aida har gida zan iskoki kin d'agan hankali"

"Umma ya fara kulata jiya a d'akinta ya kwana wallahi Umma asirin su yayi aiki baki ga iskancin da fa take a gidan ba" ta fad'a cikin kuka...

"Me!" Ta fad'a da k'arfi "amma shine aunty tace Sam baya kulata ta hanashi ya shiga sabgarta! Amma ba komai zasu san dani suke zancen su duka, kinga dena kuka sannan ki fitar da damuwar sa a ranki, dama ai dan iskan yaro ne, kece kawai kika kwallafa rai a Kansu amma tabbas zanyi maganinsu su duka, share hawayenki kawai ki jira mezai faru kinji 'yata"

"Tau Umma dan Allah kiyi wani abu wlh ina sonsa sosai banaso na rasa shi"

Kama baki Umma tayi "tau shikenan yanzu dai ki fara kwantar da hankalin ki tukunna kinji?"

"Tau Umma sai na jiki" bin wayar tayi da kallo ita ta rasa meyasa Samiha ta nace akan son matsiyacin yaron nan data matuk'ar tsana a rayuwa, a da ta so tayi amfani da hakan domin cimma wani burinta saidai ta fahimci bahagon yaro ya wuce duk inda take tunanin ta b'ullo masa, wata iriyar dariya tayi sannan ta tashi ta fara shirin tunkarar bokan nata wato mai gobe da nisa🤭(lol baiwar d'aguti sai a bada himma).

Aiki take tana tuna irin yadda ta samu nishad'i a cikin baccin ta na jiya, wanda bata tab'a samu ba in her life time, jin motsi bayanta ne yasa kata saurin jiyowa ido biyu sukayi dashi wani lallausan murmushi ya sakar mata tare da zuwa har inda take yayi hugging d'in ta tare da bata peak a goshi "morning habibty, hw was ur nyt?" Ya fad'a a hankali, lumshe ido tayi tare da ware su a hankali saidai bata tanka masa ba saima janye jikinta da tayi ta wuce cikin store rik'e da doya a hannunta, yana zaune kan kujerar da ke kitchen d'in, da kallon kawai yake binta, yuka ta d'auko tare da d'ora doyar kan cutting bord, kama wuk'ar yayi, bataji ma tasowar sa ba..

"Kawo na tayaki Habibty?" Bata buk'atar musu hakan yasa ta sakar masa wuk'ar tare da kama wani aikin, tana yi tana satar kallon sa, yadda yake fere doyar cikin kwarewa ita fa har mamaki take wai Yaya Mu'azzam d'in nanne dodonta mai tsorata yau tsaye a gabanta yana wani lallab'ata ita kam sam ta kasa yadda da wai son ta yake wai, Musamman ma da yake cewa wai, wai tun lokacin da yake tsorata tan nan da yi mata tsawa da gasa mata magana duk cikin so ne it can believe, duk da cewa wani sashi na zuciyar ta naso su gasgata soyayyar tasa saidai Sam ta hana bawa kanta wannan damar bare ma shi ta bashi.....

Sosai Samiha tayi laushi ta d'auke idon ta akan duk lamuran su, tare daci gaba da mu'amala dashi kamar ba komai a ranta yana daga cikin plan d'in su, sosai take dannewa idan Aymana na tsula musu rashin kunya da fitsara, amma taci burin duk ranar da mission d'in su ya cika zata ci ubanta.....

Duk ranakun kwananta a d'akinta yake kwana yana amfani da wannan damar ne dan ya k'ara samar musu da kusanci da shak'uwa a tunaninsa da hakan zai samu ya fara cusa sonsa a ranta, saidai duk yadda ya d'auki abin da sauk'i sam ya kasa zuwar da sauk'in dan sosai kusancin ke azabtar da ruhi da gangar jikinsa, wanda shi kad'ai yasan irin wuyar da yake sha, duk yadda yake rarrashi, kwantar da murya da lallami abin ya faskara ta saka auduga ta toshe kunnuwanta, saidai ita tayi baccinta cikin salama ta barshi jinyar gangar jiki da zuciya....
Chapter 1 · 0% Book details