← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 35

Sashe 33

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar ta tana shiga part d'inta ta dinga dariya.
Shigar mami kitchen ta taka maganin nan ta gama abinda take ta fita zuwa d'akinta, tana zuwa d'aki taji kanta na juyawa 'yar K'ara tayi ta zube agun da gudu husy taje, nan ta ganta kwance ak'asa ihu tasa ta fita waje rasa ma Mai za tayi nan ta dawo ta buga wayar haidar lokacin yana office take ya d'auka kuka take tana sanar dashi baiyi wata-wata ba yaje ya d'au muk'ulli ya tafi husy na zaune gaban mami data farfad'o ko magana bata iyayi nan suka taimaka suka shigar da ita mota suka tafi hajar kam tana gano su ko ajikinta.

*Bayan kwaana 2*

haidar husy da zee na asubiti d'akin mami da tunda aka kaita bata magana Sai dai ruwa da take sha gashi likitoci since ciwon dai basu ga komi ba,haka dai suke zaune 'yan dubiya da 'yan uwa da abokan arixiki nata zuwa hajar ce ta shigo nan suka gaisa tana ma mami ya jiki Sai harar zee take sukam basu san tana yi bama nan tace "ya haidar ina son kud'i saboda zan kai Aysha asibiti" bai ce k'alaba ya zaro dubu biyar ya bata arene ta karb'a ta fita, dama ita bata tambayar sa unguwa duk randa tai niya fitar ta take ,Bayan fitar ta tana tsaye ta buga wayar kubra nan tace Ke Aiki yaci kuma da Alama haidar yasha maganin saboda Yanzu kud'i Nace ba gardama ya bani gashi mami akwance dama ita Ke hanashi min wani abun Dariya kubra tasa tace "ay dama ba ina gaya miki ba kika zauna shirme hajar tace "ai Yanzu na gano dawan garin".

*Story writte&editted*
*By Queen meemi*
[5:35pm, 21/11/2016] Queen💋Meemi: *ZEENATU by Queen meemipage 90-91*

â™  â™ . â™ 
â™  â™ . â™ 
â™ . â™ . â™ 

*NWA*

*Queenmeemi.WordPress.com*

washegari zee ce zaune Ke matsa k'afar mami tana shafa Mata magani Bayan ta gama ta d'akko abinci ta tana bawa mamin bayan ta gama ta d'auki kayan mami ta wanke ta shanya duk ita Ke dawainiya da mami tun kwanciyar ta a asibiti don tama hana husy yi yau da yake satin ta d'aya abin dai ba labari kullum zee Ke zuwa da safeta ta zauna har dare san nan su tafi ita da haidar Sai husy ta kwana da ita ,su mum ma sunzo da dad dubiya

soyayyar zee ce Ke dad'a wanzuwa a zuciyar haidar yanda yaga take Kula da mami duk irin abinda tai Mata bata Kula ba gashi hajar ma da take kamar 'yar Tata so biyu tazo nan ya dinga shiwa zee Albarka Yanzu ma da suke zaune a harabar asibitin yace "zee kin zama tauraruwa ta ki Kula dani san nan kuma mahaifiya ta Allah ya biyaki da Aljanna" murmushi tayi "my husby in ban maka ba wa zanwa? ka nunan soyayya kaine tauraro na dole na so duk wani Abu naka" lips d'in ta yake kalla yanda take maganar sai ta bashi sha'awa, suna hira sai ga dad d'inta ya shigo gano shi yasa suka mik'e nan haidar ya gaida Shi, suka shiga word ya kuma duba ta nan yaja hannun haidar yace "Ni ina ganin ciwon nan bana asibiti bane kaga yau fa sati daya ke nan ya kamata akoma da ita gida insha Allahu Ni zan samo wani malami" ,haidar yace "ba matsala insha Allahu zami magana a sallame mu.

bayan fitar dad haidar yaje gun doctor yayi Mai bayani kan sallama zasuje suyi na Hausa bai musa ba ya basu saboda yana tunanin hakan.

Washegari k'arfe goma aka sallame su suka tafi dad kwa zuwa yayi ya sanar da malamin abinda Ke faruwa nan yace zai istikhara san nan yazo gobe,kuma zayyo rubutu don yasha.

mami kam har Yanzu dai baki bai samu ba zee kam tana gidan komi ita Ke Itada husy duk wani abin hajiya ita keyi sai dai hajiya taita binta da da kallo hawaye na zuba

haka maman hajar data zo ita tayi ta d'awainiya dasu duk bakin da sukayi kowa sai Shi Mata albarka yake ,hajar kwa tana part dinta ko ajikinta duk yan uwan mami sai Allah wadai suke da canjin kawayenta,gashi idan haidar yayi Mata magana kam halayen ta ta hayayyak'o Mai sai dai yayi shiru.

washegari da sassafe malam yazo haidar da husy ga mami a kwance yazo ya zauna ya Farai Mata adduoi tareda watsa Mata ruwan magani amai tafara nan yace wa haidar "abinda Ke damun mahaifiyar ka Gaskiya akwai sihiri ajikinta kuma abin mamaki na jikinta ne yayi Mata sai dai Bazan fad'a ba don gudun fitina sai dai duk acikin su wanda kukaga ya tsargu da harara to shine Allahu ya'alam". magunguna ya fad'a musu wanda za asayo da adduoi wanda zata na yi Shi kuma yace aje Islamic chemist sayo.

jikin su a sanyaye dukkan su nan malamin ya fita suna Mai godia basu Dad'e ba hajar tazo sai cika take tana batsaewa ta zauna kan kujera tana harara basi mata maganaba tunda sun san ayanda hajar ta canja hali zata iya komai, ba wanda yace Mata komai sai cewa tayi "wanda dai yayi Ma mami sihiri sai a binciko Shi duk da duk mu nan 'yan uwa ne sai bare d'aya" ,nan haidar dake huci duk sun gane itace ya nuna Mata k'ofa ta fita tana ya tsina.

kuka haidar yasa hakama husy data haye sama tana kuka mami kam bacci ta samu ganin hakan yasa zee tazo ta rungume haidar ta baya sorry my husby hak'uri maganin ciwo ne a komi mudai mu dage da addua kowa yayi na gari kan sa, sumar sa take shafawa kukan ya dena ya matseta gam ajikin sa yana Maida numfashi d'shiwa yayi ya shafo face nata yace "zeey bari naje na dawo".
Baya son yanke hukunci nai shiisa yake so mami ta dawo hayyacin ta.

*Story,writte&editted*
*by Queen meemi* . .

. .
[4:06pm, 22/11/2016] Queen💋Meemi: . . . *ZEENATUby Queen meemi page92-93*

â™ . â™ . â™ 
â™ . â™ . â™ 
â™ . â™ .

*NWA*

*Queenmeemi.WordPress.com*

tashin Mami daga bacci yasa ta dawo hayyacinta nan 'yan uwa akai ta san Barka su zee murna wajen k'arfe goma suna zazzaune Mami na kan kujera tana Shan kunun gyad'a, zee da husy na game a waya nan Mami ta kalli zee tace "zeenatu yau na tabbatar naka sai naka dad'in zama sai bare inji hausawa na munana miki, Yanzu kin zame min farin gani Allah yayi miki Albarka nagode" zee da kanta ke sunkuye tace "Mami ba komai innai miki kamar mum na yiwa" haidar ne ya shigo fuskar nan a washe ya zauna Mami naji dad'in ganin warware warki" kallonsa tayi "to yakamata ka d'auki matarka ku tafi kullum d'awainiya take dani ya kamata taje dakinta ta huta,wallahi samun sirika irin zee sai an tona Nikam Yanzu Bana ma sirika dake sai d'iya", kallon zee yayi ya d'aga Mata gira juyar da kai tayi tana murmushi tashi sukayi sukai sallama suka tafi.

Bayan kwana 3 haidar na zaune yayi yana kallon sama zee tazo ta cakumo Shi ta Baya nan ya janyo ta ta fad'a jikinsa, kallon juna suka tsaya yi zee tace "husby mayya faru ne"? kallonta yayi yaja siririn haancin ta, yace zee "Ni fa na gaji da halayen hajar kawai zan rabu da ita tun abinda taiwa Mami kalli fa rashin lafiyar da tai duk itace sila, domin naso sallamar ta Mami ta hana Amma ku dubi abinda take" zee tace "Kayi hak'uri ka k'yaleta idan mai shiryuwa ce zatayi" baice komi ba yace "Allah yasa" nan kamata suka mik'e yace "zo na kaiki kisha icecream" da gudu ta tashi ta sako aftrdress suka tafi kana ganin su kaga masoya masu k'aunar juna.

boka mai kankan na zaune yana surkulle nan yayi surkullen daya sa hajar na bacci ta tashi da K'ara ba addu'a balle salati, Aysha yar wata uku na bacci ta tashi da kuka ,kallon agogo tayi taga k'arfe d'aya dai-dai ko d'aukan Aysha batai ba ta fita shashin Mami suna zaune husy na karantawa Mami novel GIMBIYA MAIMUNATU tana jin dad'in book din duk da awaya take karanta Mata. . . hajar ce ba sallama ta shiga ta tsaya tsege-ge tace wa Mami "to tsohuwa ki gayawa d'anki Lalle ya zo ya maidani d'ayan gidan domin na gaji da zama dake ana samun Ido dama bakya k'aunata wallahi Bazan yarda ba" husy ce ta mike "hajar haukan naki ya isa haka" hajar tace "bai isaba ba banza kawai" dai-dai lokacin haidar ya shigo jiyo kukan Aysha yasa yayi part d'in a sukwane ya shiga d'akin yaganta ak'asa tana kuka da alama daga gadon ta fad'o d'aukanta yayi suka fita, dai-dai yana shiga hajar na watsawa mami ruwa a fuska mik'awa husy Aysha yayi ya zare belt yayi Ma husy duka yana gama dukanta ta cakumi kwalar sa Mami kam kuka take, nan ta bugawa umman hajar waya hajar tace "idan kacika d'an halak ka sakeni wallahi na gaji da zama da kai" shiru ya ratsa gun, jin hajar ta zafi zagi mami yasa haidar ya fusata yakai Mata Mari "hajar ki tafi bana son ganin ki, Mami sai dai ki hak'uri na saki hajar saki d'aya tunda ita ta buk'ata", tsaalle ta buga tace "tafi nono fari" fita tai part d'inta ta d'au waya ta bugawa kubra nan ta gaya Mata kubra tai shewa Amma "Kinyi tsiya tab! kubra da ta kashe wayar tace "dama banason ganinki da wan nan handsome guy d'in yafi dacewa da gentle lady" Ni miemie Nace Allah ya kiyashe mu tab'ewa ka rabamu da muggan k'awaye.
Chapter 33 · 0% Book details