← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 35

Sashe 30

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau aka kawo lefen zee tamkar na budurwa Aneee sai rawar kai ake da munay suna tare a d'akin aneesa zee tace "nide gabana fad'uwa yake wallahi bana son aure Yanzu" munay tace "kaji banza idan ba kiyi bamu guri, don kin samu ma zance miki Anty inkika zama matar yaya" zee tace "dalla karki fad'an mana dole dai kice da mijin iya baba" Anee tace "Ke ki had'a mana k'auye day mana" zee tace "ba abinda zan kawai zan kirawo husna ummu samha tazo tai mana lucture" munay "tace bar matar yayan nan wallahi se Munyi" zee tace "ni fa nafiso abari na gama poly d'ina kinga Yanzu hutun second semester zami" anee tace "kyayi kya gama har anko sai mun fitar" wayar zee ce "tai k'ara ma'aruf ne ta juya musu baya tana k'us-k'us.

haidar kuwa Dan tunda yaji ankawo lefen zee duk ya birkice domin yana samun information gun kb saboda Anee na gaya Mai ,yau da yake zaune office ya kifa kai yana tunani kansa yaji yana ciwo ya tashi ya fita ,gun kb yace su had'u gidan gonar sa yana zaune sai Shan tea yake kb ya shigo aboki ya fad'a haidar suka gaisa ,haidar yace "Dubai zan tafi ,Bazan iya ganin zee ta tare da wani ba" kb yace "har kullum ina baka hak'uri saboda komi daga Allah ne ka kwantar da hankalinka I tsumma a randa", Dariya haidar yasa "wannan Karin maganar fa"? kb yace "agun kaka na koyo kasan goyan kaka ne ni" haka sukai ta hira sosai ya mantar da Shi .

*Bayan kwana 2*

rashin kunyar da hajar keyi da irin tab'argazar da takewa haidar yasa Shi damuwa kad'an -kad'an ya fara rashin lafiya a tsai-tsaye ,wajen k'arfe 4 na yamma haidar yaje saiwa mami turare a supermarket Bayan ya d'akko yazo gun counting idon sa ya gano Mai zee da ma'aruf da faty sun shiga supermarket d'in Sam bai bari sun Ganshi ba saima wani kishi da yaji ya zubo Mai domin muddin ya tsaya zai iya barin abun fad'e don yanda yake ji kamar ya kauda ma'aruf haka ya koma gida a fusace tunda yaje gida k'irjinsa Ke ciwo ,ga hajar nayi Mai hauka aka kamar ya kurma ihu k'irjinsa har wani ta fasa yake zuwa yayi ya d'akko kank'ara ya d'ora ko zai samu sanyi a ransa Amma ko gezau kawai hawaye ne ke zuba,tashi yayi zai je side din mami kamar me yaji kansa na juyawa ga k'irijin sa ya rik'e be aune ba yajishi wanwar ak'as.

ihun Mai gadi ne ya sa su mami suka fito lokacin husy ta dawo Hutu ,haka hajar ma ta fito nan suka cika gun da kururuwa da k'yar aka sashi a mota husy ta jasu sai hospital,nan danan aka karb'eshi da yake private ne cikin awa d'aya suka shawo kan matsalar fitowar doctor yana goge gumi yasa su husy saranda tunkan yayi magana cikin hajar ya murd'a take tafara nak'uda da yake dama watan haihuwar ta take ,kuma nan hospital d'in take awo cikin sauri nurses suka shiga da ita Labour room ..

*STORY WRITING & editing*
*Queen meemi*

*ZEENATU by Queen meemi page 81-82*

. .
. .

*NWA*

*Queenmee.WordPress.com*

Bayan kamar awanni akace hajar ta haifi baby gal cike da farinciki mami ta tari nurse d'in, husy kam tana tagar dai-dai inda aka kwantar da haidar sai kuka take suna nan tsaye umma tazo nan suka tafi gun hajar doctor ya buk'aci ganin mami sun zauna yake gaya Mata damuwa ce tayi Mai yawa ya kamu da hawan jini Amma baiyi worst ba kuka ta saka "to doctor ya za ai"? nan yace "ba matsala mun shawo kan matsalar tasa tunda batai girma ba ,Amma adunga Kula da b'acin ransa tunda ga larurar data same Shi "haka ta fito a tana matsar hawaye nan husy ta tare ta suna kuka "husy duk nice silar saka haidar cikin matsala tabbas nasan da matsalar hajar gashi ya k'wallafa raiga zee husy tace "mami sai hak'uri"

dai- dai lokacin aka fito da hajar akai rest room da ita wajen 6pm aka bawa su hajar sallama domin lafiyar ta lau, suka tafi itada umma direct gidan su aka wuce da ita saboda babu damar ta zauna anan tunda larurar data samu haidar,shikam haidar sai 8pm ya farka duk yayi zuru-zuru mami dake zaune ta kalle Shi "haidar sannu" husy ma haka da k'yar yasha tea mami kam ta kasa tsugum Washegari hajar da sassafe ta bugawa mami waya lokacin tana hadawa haidar tea wayar tayi K'ara ta tashi ta mik'o mata ba gaisuwa balle tambayar jikin haidar tace "mami babu naman gashi fa saboda Allah ace tun jiya babu Wanda ya kawo komi" mami tace "to rasa kunya har bakin naki ya bud'? kinsan dai halin da mijinki Ke ciki kuma ina wajen sa Haba kina alkunya mana" tabe baki hajar tayi ta kashe wayar.

Bayan kwana 2 da haihuwar hajar mami tasa aka kai mata duk abin bukata can ma sai da sukai fad'a da husy domin suna kaiwa hajar ta ture kaya wai basi Mata ba da yake husy bata k'yaketa tace kar ta d'auka d'in, yau kwanan haidar uku ya fara dawowa normal waya aka bashi yayiwa hajar ba gaisuwa balle ya jiki ta hau fad'an kaya sunyi kad'an baice komi ba ya kashe wayar,haka dai hajar tayi ta rashin mutunci kubra na zugata k'arshe ma cewa tayi bazata shayar da 'yar ba tunda mami bata k'aunarta har haidar din sai da aka kai ruwa rana san nan tace sai an bata kud'in shayar wa ran umma ya b'aci tayi mata duka babanta kam cewa yayi zai sallamata duk da jegon data Ke, ranar suna kuwa yarinya taci suna Aysha an yanka raguna 2 aka duk gudun mawar data samu haka ta bawa kubra tace taje gun boka ai mata aiki kan haidar da mami,umma addua kawai takewa hajar.

satin haidar biyu Allahu yasa ya warke kb ne ya d'auke shi suka koma gida yana son sanar Mai bikin zee da ya rage 3wk Amma yak'i gaya Mai saboda ciwon sa,bayann sati d'aya haidar ya dad'a girgijewa kullum sayyaje ganin baby Mai kama da husy sak Amma da b'acin rai yake dawo wa din hajar ta bud'e huta musammn da kubra ta dada shigarta yau sai data ambaci mami tayi rashin kunya haka ya mammareta taci kwalar sa badon da sanayyy ba da tuni ya saki hajar.Allah ya shirya maasu hali irin hajar.

ganin katin bikin zee ya sa yayi haidar damuwa shiri yayi tsaf, yayiwa mami sallama zai je Dubai ya d'an huta yayi haka ne don ya guje ganin auren zee don Shi ya san wahalar da yasha tabbas ya san ya rasa zee zaiyi ta addua Allah ya gyara halayen hajar
Washegari yayi shiri k'arfe 8 ya fita sai da ya biya ta k'ofar gidan su zee ya bawa sadiq later da ambulan yace ya bawa zee san nan kb ya Lula dashi birnin kano don ya hau flight da wuri .

*Story writing&editing*
*Queen meemi*
.

[3:30pm, 17/11/2016] Queen💋Meemi: . . . *ZEENATU by Queen meemi page83-84*
â™ 
â™ . â™ . â™ 
â™ . â™ . â™ . â™ 

*NWA*

*dedicated to Lubie &bena*

*Queenmeemi.WordPress.com*

sadiq kam komawa yayi ya mik'awa zee sak'on haidar akasalance ta bud'e ta fara karantawa kamar haka _zeey naji labarin zaki aure nayi jimamin rashinki zuciyata bazata iya ganin kin auri wani ba, ayanzu na bar k'asar ma ,Allah ya baki zama lafiya keda sabon angonki yasa ya rik'emin Ke amana ga gudummawa ba yawa luv u 4 ever_

_daga_
_haidar_

jikinta ne ya jik'e sharaf da gumi kamar me jin zaifi,zuciyar ta taji na rad'ad'i surar haidar ta fara tunanowa ahankali siraran hawaye suka zubo Mata "I miss u so much haidar" d'ayar ambulan ta d'auke ta Bud'a kud'i ne 'yan bandir na dubu suka suka zubo d'auka tayi yayinda taji kud'in na k'amshin turaren haidar lumshe Ido tayi tana ajiyar zuciya,ganin ba sarki sai Allah yasa ta tashi ta kwanta bacci,d'akin mami ta tashi ta lek'a ganin su sadeey tayi nata kuma kallon lefe "tsaki tayi ku bakwa gajiya da kallon lefen nan ne"?, "eh wallahi ya zee kinsan kayan da D'an karan kyau" tab'e baki tayi ta koma d'aki tana nai zancen zuci.

mami na zaune Alhaji baba na kan kujera wan baban haidar ne "agaskiya mami banji dad'in abinda ya faru ba ,ashe Shi haidar sun rabi da yarinyar nan, ai ban sani ba sai jiya mariya Ke gayan kakanta abokina ne banji dad'i ba ,nan mami tace sai hak'r don nice ma sular rabuwar nasu gashi na aura Mai 'yar k'anwata Sam baya jin dad'in zama da ita har ni kaina" ,Alhaji baba yace "anyi kuskure dama Allah baya barin hak'k'in wani Dan wani idan kace tukunyar wani bazata tafasa ba taka ko gumi bazatai ba,Haba hajiya gashi kin sayawa d'anki rashin kwanciyar haankali da kanki, ina mamakin matan da zasu sa d'ansu ya rabu da matansa alhali ya naso don son zuciya ai gashi kin rabu data kirki a ganinki ta mallake miki d'a ko? to aiga irin ta nan kin aura Mai wata Ke tana gasaki" "sai hak'uri nayi nadama sosai", "Yanzu ita yarinyar aure zatayi Ke nan ko"? "eh wallahi" jinina kai yayi "Allah ya bata zama lafiya,ita kuma wan nan Allah ya shirye ta, kinga ko! gashi nan D'an naki yayi nesa dake ,d'a Mai biyayya Mai yasa wasu iyayen Mata 'ya'yan da suka fi muku biyayya kunfi tursasu akan abinda basa so"?. "Ayi hak'uri sharrin shed'an ne" tashi yayi "Toni kam na tafi Allah ya gyara al amuran"

*Bayan sati biyu*
Chapter 30 · 0% Book details