← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hajara Amma kin kyauta da kika zo min hutu saboda kadaicin husy na damu na"(hajara 'yar kanwar mami ce) hajara tai dariya "mami ay dama ni tagunki ce boko ne ya sani gaba ",haule ce ta shigo da try d'auke da five alive da cup ta aje ,hajiya ta kalli haule tace ta dauki trolly en hajara ta kai akin baki .
Tashi hajara Tayi yawwa mami bari naje nai wanka tabi bayan haule ,dariya tai ta zauna gefen gado tana tunani saida tai wanka tai sallah nan ta dawo falo ta zauna ,dai-dai lokacin zeena ta shigo tasa after dress ta yane kanta har kas ta durk'usa ta gaida mami hajara ta kalleta ta juya "hala mami wannan ce Amaryar"mami ta ce itace tab'e baki tayi "bale fi tayi" kitchen zeena ta shige ta hau ora sanwa haule na tayata "wajen Karfe 1:30 ta gama ta fito taiwa mami sallama ta koma .
Hajara dake ta zabga Loma ta kalli mami "Amma ba ta iya girki,mami Nifa jiran yaya nake ya dawo" mami tace sai 5 zaki ganshi "dan ma wan nan figaggiyar matar tasa na kanai naye shi aida kullum yana nan" ,hajara tace" tab Amma ta samu sake" .

************
K'arFe biyar haidar na shigowa ya faka motar sa agajiye ya Shiga Zee da sauri ta rungume abin ta. tana mai Welcm wanka yaje yayi ya dawo Zee ta zauna tana bashi abinci suna hirar su rufe Mata ido yayi ya saka Mata key a hannu bu e wa tai taga na mota ne "na meye habiby"? Naki ne tsalle ta daka ta rungume shi "thnk u so much my haidar
"U deserve it dea".
Kiss ta bashi a lips Burum a ka shigo "ya haidar dama ka dawo"?
Juya wa yayi ganin hajara tsaye tana dariya yace "Aa k'anwataa saukar Yaushe "?
Zama tai da fari ko kallon Zee batai ba "dazu na sauka zanwa mami hutu ,Ay naita tryn number inka is switch off".
"Eyya kin san na canja shiisa" ,naga Amaryar ka sede da alama zatai jin kai kallon -kallo,sukai da Zee da haidar ,yak'e kawai yayi "haba kawai don Baku,Saba bane ba".

Tashi tai ta shige kitchen sai kace gidan ta ta akko lemo ta dawo "Amma ya haidar side enka yayi mun kyau "
Hira sukai tayi san nan ta koma ..

*8pm*

Haidar ya Shiga gun mami tana zaune suna kallo da hajara, bayan ya gaida ta sayya ce dama hajiya magana zami kallon hajara tai ,tashi tai ta shige aki .

"Dama mami mota ce karama na saiwa Zee saboda ko zata unguwa Kinga ta huta inta fara zuwa school".
Wani banzan kallo tai mai "to uban Almubazzaranci yanzu ba ka saiwa k'anwarka ba , Amma zaka saiwa wata matarka" .
"Mami ai husy tana da tata motar "
"To ban lamunta ba salon ta sake mik'e k'afar shirya tsiya ko ".
"Mami na Riga fa da na bata key".
"Yayi maka kyau"
"Kiyi hakuri mami" bata ce Kimi ba saima tashi da tai ta Shiga aki.
Asanyaye ya tashi ya fice.mami data zauna kan mudubi wallahi dani yake zancen, dama can ni jini na bai hadu da yarinyar nn ba"
*****
Washegari wajen 11 motar aka kawota red 207 Zee Cike da Murna ta fito tana shafa motar, bu e wa tai ta Shiga tama rasa murnar da zatai mai kawo motar ya tafi da Murna ta Shiga gida sai tsalle take .

Yau ne shigarta na farko side en Zee tunda aka kawo ta ,a fusace ta banke kofar "ina kike fito nan aguje Zee ta fito tace gani mami "shasha bani key in motar nan kin mallaken d'a sai abinda kika ce to idan kwance kika Kwan ni kullum atsaye nake k'i gam".
kuka ne ya zowa Zee da sauri ta akko Muk'ullun ta mik'a Mata afusace ta fita. aki zee ta shige tana kuka .

Mami data Shiga side enta tana ta fa a hajara ta fito "mami meye "? mami tace barni da waccen figaggiyar wai yanzu Dan rashin ciwon kai haidar ya bata mota" .
Hajara tace aini tin gani na da ita yanda naga haidar na Rawar jiki a kanta na san an gama da Shi ,"ai mami ki tashi tsaye kina zaune xata rabaki da Shi".
k'wafa tai "bar ni dashi inya san wata ai besan wata ba.

Bayan dawowar haidar Zee ko a fuska bataa Nuna mai ba, saima wata sabuwar soyayya da ta Farai mai tana kwance kan cinyar sa yana shafa gashin ta "babyna Kinga mota ko"?
" Na ganta har Shiga nai ba abinda zan cema sai dai Allah y saka da Alheri".
shafo face enta yayi ya matseta a jikinsa kirrrrr wayarsa tai K'ara .
K'irjinsa ne ya buga ganin sunan mami,ahankali ya d'auka "kazo yanzu ina son ganin ka"k'it ta kashe
Tashi yayi ya fita hajara ce a bakin ofa tana waya fari ta sakar mai d'auke kai yayi mami na hakimce tana duba less less da super. zama yayi a d'aya daga kujerun yace mami gani.
"Haidar wai Meya canja ka? tunda kai aure ban isa na gaya ma ba ka dauka ba yanzu ashe sai da kasai motar ?,to na k'wace ,tashi ka tafi yana son magana Amma ba yanda zaiyi ganin ta had'e ya tashi ya fita .
"Ya haidar" juyawa yayi ganin ta tawo tana girgiza kawai ya daga Mata hannu "pls kaina ciwo yake" gaba yayi ,binsa tai da ido ta tab'e baki.
"Ko mai zeena, komai zeena. to wallahi nima sonka nake kuma dole ka auren ,ciki da shige.
Rungumeta yayi ta baya ,don ji yayi ta K'ara kima a idonsa "Zee ta baki fad'an abinda mami tai miki ba, naji Dadi tabbas nasan zaki riken sirri, but kiyi hkr insha Allahu zata dawo miki da motar ki ".

bakomi masoyina murmushi tayi mai, tareda kashe mai ido daya........

*_Writing_*
*_Queen meemi_*

.

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . *ZEENATU by Queen meemi page 32*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠. ♠
♠. ♠.
*®NWA*
*Dedicated to Lubie &bena*
*17,Oct 2016*

Yau da ya kama weekend haidar yace yana sha awar kunu da kosai , Zee na kitchen sai kacaniyar tuyar kosai take ,da yake ta gama dama kunu in, haidar na zaune yana kallon wani film game of the throne, a laptop ihun Zee ya juyo daga kitchen a guje ganin tana yarfe hannu yasa ya kama hannun yana firfitawa da bakinsa.
"Meya same ki dear".
idonta daya ciko da hawaye tace" mai ne ya fallatso mun", sannu yay Mata ya karanta Mata falaqi da nasi don kar gun ya tashi ya rofa ,yace ta bari ya k'arasa tuyar .
Tana tsaye gefe suna tab'a hira tana had'a sauran kayan Shi kuma yana kwashe k'osan .
Ba sallama su kaga hajara a kofar kitchen en .
"Aa ya haidar yau soyayyar ta motsa ne hararar ta yai "ina miki wasa ne" .
dariya tayi "dama mami ce tace kabawa maigadi ya sayo mai motar ta babu" .
"ok zan bayar".
kallon Zee tayi ta sakar Mata harara tai waje.

Aguje ta Shiga akin mami ta tsaya "mami lalle yarinyar nan tana neman Maida ya haidar solob'iyo duk gayun sa Amma shike tuyar kosai ".
Dariya mami tasa lalle kuwa tab namiji da suna hajara "
Hajara tace" mami wan nan Karin maganar ai da suna nane,".
mami tace" barni dashi lokaci ne" .
Hira suke cikin so da k'auna nan Zee ta ya tsine fuska "wallahi cikina ciwo yake habiby" .
kallon ta yayi yace"sannu" kad'an- kad'an sai zazzabi ya rufe ta, kafin K'arfe 11 Zee jikinta yayi zafi zau ganin haka yasa haidar ya kwasheta zuwa aaibiti .
Taimakon gaggawa akai Mata cikin mintuna aka K'ara Mata ruwan akai Mata Allura bacci ya kwasheta.
Gun doctor yaje doctor yake gayya mai ai tana da typot ne .
Waya ya bugawa mami ya gaya Mata Allah ya sawwake tayi Mata.
haidar bai gayawa mum ba (gidan su Zee) saboda doctor yayi masa confirming tana tashi zata ware tunda abin baici k'arfinta ba.
Haidar na zaune wayarsa tai K'ara mami tace "hala kode ciki ne".
Haidar da yaji kunya "yace Aa sunce typot ne".
jinjina kai tayi ta kashe.
Haka ya zauna a hospital in yaa kwana tunda bai gayawa yan uwantaba
Kwa nan su aya Ana treatment en zeey ta warware aka basu sallama tare da magunguna

***********
Wajen 11 suka shiga gida mami da hajara na zaune kan kujeru kusa da wata bishiyar umbrella, suna hira haidar ya fito zeey ma haka wurin mami sukayi zeey ta gaida ita haka Shima haidar in hajara ma ta gaidashi ,Amma ko kallon Zee batai ba, balle tai Mata ya jiki.
Mami tace" ke ya jikin naki"?.
zeey ta ago manyan idanuwanta tace da" sauk'i"
"Ai na auka ciki gareki Ashe dai cima zaune ce ke".
Kunya ce ta kama ta suka mik'e .
Bayan Sun shige mami tace ace wata biyu babu amo ba labari ,hajara tai dariya "lalle kuwa".

************

Bayan kwana biyu a tsakani zeey ta warware tana zaune tana waya da munay tana Mata zan cen zuwan su.
Bako sallama hajara ta Shiga taci kwalliya direct kitchen ta shige ta bu e gidan sanyi ta akko exotic ta fito tana zuka ,zeey da abin ya bata mamaki da sauri ta tashi.
"ke wama kike da suna yanzu in Banda shirme keba matar gida ba sai kawai kizo ki shigemun kitchen Kamar naki, ba tambaya ki au Abu ki fito kina mun kallon banza kina zuk'a ko"?.

Wani lalataccen kallo hajara taiwa Zee "lalle wuyanki ya isa yanka dama kin iya fa a"?.
Dariya zeee tayi "rashin sani ayya fi dare duhu,ni enn nan zeena idan rashin kunya kike ji dashi na fiki haka in fa a donni ba kanwar lasa nace".
"Tun zuwan ki naga irin abinda kike min hak'uri dole nake ,idan nai hkr akan Wanda suka can-can ta, to wallahi k'aryarki na k'yaleki ki raina min hankali."

Hajara tace" naga gidan wana ne don haka sai abunda nai niya"
Chapter 17 · 0% Book details