← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 35

Sashe 3

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

zo kuga yanda idon zee ya Firi-fito Saboda tsoro ,ihu lubna ta fara ta cafko rigar zeee ta matse ta ihu tai tayi ,idanuwan lubna sukai jajawur gumi ihu lubna ta kuma sakawa nan ta fadi as tana birgima take class ya har gitse tuni malamai suka zo aka samu wani malami a cikin su ya farai mata karatu ihu ta kuma yi tana surutai " ku gayawa zeena tunda ta tab'oni sai ta gane kurenta mesa zata b'atan rai wallahi yau Sekin gane kurenki in kinje gida kuka wiwi zee keyi ta bud'e baki "lubna kiyi hkr" baruwana se kin gane kurenki ,fizge -fizge lubna ta fara da k'yar aljana suka sauka tai bacci zo ku ga yanda idanuwan zeena ke tsiyayar da hawaye ta had'a gumi nan monitor suka fitar da lubna ,asalub'e zee ta zauna Kan bench inta nan 'yan class suka fashe da shewa ,d'ago kai tayi ta bisu da Ido tai k'wafa ,nan suka dinga had'a Baki suuna cewa "anyi walk'iya mung...... Tashi tsaye tai "wallahi duk se kun gane kurenku banzaye kawai ,ihu suka kuma sawa suka kuma had'a Baki "anyi walk'iya.... ,dai2 tym in aka buga k'ararrawa da gudu suka dinga fita Saboda sun San halin zeemasifa............... . *©Queen meemi* *meemiqueen.pun.bz
[9:24pm, 01/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page7*

. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠
. .
*®NWA . [SAT 10 2016] dedicated to Lubie & bena*

. . Asalub'e taje gida idonta yai zuru- zuru haka tai sallah ta zauna cin abinci sai had'e rai take ,haka Sadiq ma ya shigo gidan wujiga-wujiga da alama yunwa yakeji sai k'walawa mum kira yake shigar sa falon yai tozali da zee sai kai Loma take "wayyo zee dama yunwa nakeji" zama yai ya tsumbula hannu cikin kwanon yakai Loma,zee ta rik'e hannunsa "waya baka izinin samun ban zan hannunka daba ka eanke cikin abinci na"? ta ture hannun " haba zee yunwa fa nakeji" "to baraka bari mum tazo ta baka ba ko faty bara tazo inacin abinci ta saka hannu ba sekai da girman ka". "wallahi zee sai naci Saboda yau a school banci komi ba kai hannu yai ya cigaba daci tsam ta tashi taje ta wanko hannunta shi kam ya cinye yana mata gwalo k'wafa tai "zaka sani ne".

***********

wajen 3 zee ta tashi ta shiga toilet Dan yin wanka Saboda Lokacin islamiyar su yayi,mum na d'aki tana kallon tsoffin picture inta ihun zee ta jiyo da gudu ta fita ta bud'e toilet en tana "meye zee"? "wayyo mum shikenan abunda lubna ta fad'a gaskiyane wayyo na shiga uku" tsaki mum tayi "idan bara ki fad'an ba to kiwa mutane shuru" gunjin kuka taci gaba " mum Aljana ne ta kashen fitilar K'wan band'akin nan Lokacin Dana shigo akunne yake Amma na sunkuya ina cud'a k'afa na ina d'agowa Naga d'if ya mutu shine na d'aura zanina na d'auka shigowa akai Seda na duba Naga bakowa "kuka ta kuma fashewa Jikinta na rawa "dama munyi fad'a da lubna ashool kuma tana da aljanu shine tace wai in sauraraeta inna koma gida"hannu mum dake Kan hab'ar ta ta sauke " Amma ke zee anyi mai wawta to wutar nepa aka d'auke ,Inde kinyi adduar shiga toilet to Allah zai kareki kuma ki kwantar da hankalinki wasa take "rufo mata band'akin tai dak'yar zee ta k'arasa wan kan tai shirin school idon nan yai luhu-luhu Saboda kuka.

************

haka suna zaune da dare duk an hallara Ana hira faty na Kan cinyar mum Lokacin tana Sadiq na Kan kushin sadeey na zaune tana note uwargarin zee tana danna wayar mum ,faty ta taso ta zauna Kan ciyar zee tana k'ok'rain k'wace wayar hannun zee ,kin bata tai faty tasa kuka da tsamin bakinta tana "ki bani"doke hannunta tai "dalla tashi kibar nan uwar naci " dai- dai sai cinyar zee faty ta dai -dai ta ta gantsara mata cizo cin zafin datai yasa ta murd'a bakin Auta nan ta fara ihu mum tace" sannu zeena yanzu autar ki kaiwa haka "? "Mum kina ganin de cizon da tai mun bayan an hanata cizon mutane" "to kuma sai ki mata dukan k'arfi ai ba k'warunku d'aya ba " "ai hakuri mum " kwace wayar tai ta mikawa faty tace kowa yaje ya kwanta tunda 9pm tayi hakan kuwa sukai. *********** zeena har ta kwanta ta taashi don ta tuno fad'an ta da lubna nan tsoro ya shige ta sauri tai ta kunna K'wan cikin haske ya gauraye sai kalle -kalle take ahankali ta kwanta ,sai juye-juye take Saboda bata saba kwanada fitila ba ,taashi tai ta kashe fitilar har bacci yai awon gaba da ita jin motsi yasa ta fasa ihu "wayyo mum ga Lubna nan " mum dake d'akinta ta shiga dakin su zee ta kunna fitila ganin sadeey tai a tsaye Jikinta na karkarwa ga zee akan gado ta k'udun -dune. " wai meye hakane zee ?ke kuma sadeey meya tada ke?" Sadeey tace" fitsari na tashi zanyi shine naji ya zee ta fasa ihu taban Tsoro" zee dake zaune sai fiki-fiki take da Ido "mum wallahi ban d'auka ita bace ba" "jini nan zeena mesa ne yau duk kin birkice na gayamiki Lubna kawai don ta tsorata ki ne" zama tai Abakin gadon abinda" zan gaya miki kinga mutan b'oye in ka nuna kana Yawwan jin tsoro to sunfi shigar ka ina cede kinyi alwala da zaki kwanta da, adduoi,"? eh nayi ,San nan zee ki rage wasu abubuwan kinga girma kike yanzu fa shekararki 15 yrs pls ki rage yawan fushi da tsokana kinga gashi wata kunyi fad'a ta tsorata ki a banza" to mum naji nagode " "addua ta sasu suka kumayi ta kashe fitila ta fita da k'yar da bacci........

************

. *to fanz ena Kuyi hkr da wan nan Saboda sallah ta k'arato insha Allahu Zeenatu zai daka ta anan sai kuma bayan sallah idan mai kowa mai komi ya kaimu insha Allahu zan cigaba,Fatan zakuyi sallah lafiya ku kasance dani akoda Yaushe taku har kullum meemi . *Happy eid el Adhar to u ol* *©Queen meemi*
[9:24pm, 01/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page8*

♠.         ♠.         ♠.           ♠.           ♠.           ♠
♠.              ♠.          ♠
                *®NWA*
*dedicated to lubie maitafsir & Benazir*
     *[9 Sep 2016]*

********
Zee tsaye a Gaban Allo ajin yayi tsit Ana jira aji ta fara karatun haddar da aka basu malam haruna dake tsaye ganin Zee Tai shiru yace "zeenatu ke nake saurare" tsuru -tsuru Tai da idanuwa take ya Nuna Munay da taxo Tai nata karatun Cikin nutuswa ta karanto dai-dai iya Inda akaa basu haddar haka ya umarceta dataje ta zauna ya kirawo Aneesa itama tayi ta zauna nan ya had'e rai ya juya gun Zee yace " wato duk abokan surutun naki sun iya haddar banda ke ko? me ya hanaki to"?. Shiru Tai ya daaka Mata tsawa ,jiki na rawa tace" ya sayyadi wallhi k'auye mukaje biki shiisa banyi haddar ba Amma na iya rabi " "ay dama zeena bakya hadda to wallhi kinsan Allah,idon baki haddar nan ba sekin D'an D'ana " ya sayyadi ta fad'a kallonta Yai "meye"? Dama cewa nai zan biya da qur'anin nan ya mika Mata aya biyu ta karanta Tai shiru ya d'ago ya" Naga kink'i k'arasawa nan ta kai qur' anin dai-dai idon ta ya" sayyadi bana ganin rubutun ne haka ta mutsits-tsike idonta ta kuma k'urawa qur anin Ido ,"wayyyo Allah na wai meya faru da idon nawa ne"? Hata kuma maimai ta ayoyin  bayan haka ta kuma tsayawa dariya malam haruna yasa nan 'yan class ma suka tuntsire da dariya.

*******
Haka tabisu da Ido Tai k'wafa ,"ya sayyadi na gama" ta sunkwi dakai ,had'e rai yayi ai" sekin k'arasa kunya ce ta isheta ta kai wajen mintuna ahaka ganin zata b'ata musu lokacin yasa ya karb'e qur'anin yace ta matso kamar an dasa ta.

*******
"Ba dake nake magana ba" bulala ya d'auko Yai Mata k'warara biyar ya K'ara Mata page d'aya "kuka take ahankali tana matse Ido munay ta sunkuya tana dariya haka malam haruna ya cigaba da karatunsa ita kam se kalle-kallen 'yan class en take taga Wanda yai Mata dariya ta rubuta Shi alist can ta gano ummi bogaza sunan Wata aclass en nasu dariya Zee tasa ganin bogaza da Tai na dariya haka malam haruna ya gama ya fice k'irrrr aka kad'a da sauri taje wani lungu ta tsaya ganin bogaza yasa tazo ta rik'eta "wa kikewa dariya don na kasa hadda " wallah ni ban miki dariya ba jikin ta se b'ari yake don dama tsoron Zee take d'uuu 'yan makaranta sukazo wucewa nan suka taru Wata kubra tace" ummi wallahi kima Zee duka kalleki ba jibgegiya  duk ajinmu ba Wanda ya kaiki k'iba Amma ki zauna jikinki na kar- karwa kan Zee".

ganin hakan yasa Zee ta cafko ummi bogaza ta kai Mata duka dambe suka fara ummi bogaza ta d'aga Zee takai kass I'donta ya rufe sai dukan Zee take zo kuga idon Zee ya raina fata se Hawaye take cikin k'arfin hali ta gantsarawa bogaza cizo nan fad'an ya kuma rikicewa sai da wani mutum yazo wucewa ya rabasu kowa ya kama gabansa.
Chapter 3 · 0% Book details