← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 35

Sashe 22

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kwana biyu da barin zee gidan ,Amma ab'angaren mami hankalinta ba a kwancee ba,domin tun fitar haidar bai dawo ba ,hankalin ta duk a tashe yake wayar sa duk a kashe ,yauma dat ake zaune waya a hannu tana kira jin ta Shiga yasa tayi dariya wayar nata ring Amma ba a d'auka ba sai can ya d'auka.

Mami "tace kai yanzu haidar don mai afkuwa ta afku ,shine zaka K'i kwana a gida ko ,to Ina maka magana da babbar murya ka dawo gida" kit ta kashe .

Juyi yayi kan gadon yayin da ya k'urawa sili ido duk ya fad'a Kamar mara lafiya ,ahankali ya mik'e yana gauraye hanya yaje ya Shiga toilet yayi wanka .yasa jeans da tsht ya fito motar sa,ya Shiga bai tsaya ko ba, sai k'ofar gidan su zee yan mintuna yana tsaye sai ga fitowar dady da yake safiyace da sauri ya fito dady ya kauda kai tare da Shan kunu .
Gaida Shi yayi ya amsa a takaice.

"Dady son Allah kuyi hkr ba lai fina bane" D'aga mai hannu dady yayi dama banga laifin ka ba Amma sai dai ka sani idan biko kazo zee bazata koma ba" Daga haka yai wucewar sa.
K'urawa k'ofar gidan yayi da Ido San nan yaja mota ya tafi.

Fuskar nan tamkar an aiko mai da sak'on mutuwa ya Shiga falon Mami ,tana zaune itada hajar suna hira ,ganin sa yasa hajar ta kashe Ido an d'ame jiki sai wani barbaza Ido take ko kallo bata ishe Shi ba .
Mami "tace to kaga duk abububwan da suka faru a yanzu ne zaka San kayi aure so nake afara maganar bikin nan kasan lokaci na wucewa".
"Yanzu Mami baza ai maganar dawowar zee ba" .
Hannu ta D'aga mai kaini na bar wan nan maganar an raba ka da k'wallon mangwaro Dan ka huta da k'uda Amma kai sai bibiya kake, k'walawa hajar kira tayi.
Cike da karairaya ta fito "Mami gani".
"To ga hajar,nan kaje ku fara shirye- shiryen yanzu so nake ka kaita ta zabi kaya Wanda zaka sa Mata alefe".
Had'e rai yayi be ce Komi ba ,ya tashi ya fita .
Mami tace "yaro ana so ai ma gata kai kana shirme ga hajar dam b'asheshiyar yarinya Amma ka zauna kana walagigi kan wata zee".
Tsayuwa tayi a ajikin motar sa tana hira a waya ya fito ,dosar motar yayi yana waya ,direct gaban motar sa ya Shiga ya kunna.
D'ago kan sa yayi " Ke bar nan" .
juyawa tayi "ai kaji me Mami tace dai".
Fito wa yayi ya kai Mata hauri da gudu ta matsa ,Shiga motar sa yayi ya figa
Tana tsaye tayi k'wafa wallah duk randa guy din nan yazo hannu na, zai gane baida wayo,tsaki tayi ta Shiga gida.

*After 1week*

********

Zee kam ta zama salihar k'arfi da yaji tun sanda ta dawo take zazzab'I ,yauma data tashi jikin ba D'adi sai. Amai da take kwararawa.
Ga yawan kuka tana zaune bayan maganin da tasha ,wayar ta tayi ring ganin new no yasa ta d'auka .
Tsaki taji anyi a ciki "nice hajar dama na bugo na gaya miki ne bikin mu da tsohon mijin Ki , saura sati 2 nayi winning akanki sai kuma kibi wani sarkin haidar nawa ne yanzu"
Zagi zee ta k'unduma Mata yayin da kishi da k'unar zuciya Ke cinta .
"tace karki K'ara kirana na tabbata haidar baya sonki duk Ki gama azarb'ab'inki ,Matar shige kawai....

Aje wayar tayi ta fara kuka take zazzabi ya rufeta ,tashi tayi kawai jiri ya d'ibeta ya ta fad'i akan cikin ta.

Yar K'ara ta saki mum ta Shiga aguje ta ganta kwance ga jini na bin k'afar ta ,mamaki mum keyi,shigowar sadiq yasa tace yayi sauri yaje ya naimo mai mota bai Dad'e ba sai gashi da D'an adaidaita ya taro suka ciccib'e ta sai NAGARTA HOSPITAL nan aka kar b'eta ganin yanda jini Ke bin k'afar ta yasa suka rufa akanta.

Bayan hours doctor ya fito nan mum ta bishi yayi Mata bayanin ta yi 'barin ciki na one month sakamakon firgici data Shiga.

Mum ta kallo doctor "ai doctor Inaga Ita kanta bata San tana da shigar ciki ba, gashi har ya zube, ni kaina sai yau.Nama fahimci hakan ganin yanda take amai ".
doctor "yace to madam kin san akwai cikin daba ba a gane shima da wiri wasu sai ya kai 2month suke ganewa"
Drugs ya rubuta, San nan yace mun bata gado sai gobe idan ta D'an samu hutu sai a sallameku

Sadiq kam gida ya koma Dan kawo wa Mami abinci, tunanin kiran haidar yayi sai kawai ya danna kiran sa,Haidar na zaune a d'akin kb suna Maida zance inda kb Ke dad'a bashi kwarin gwiwa,daukan wayar yayi ya Kara a kunne
" Helo zee bata da lafiya ta samu miscarriage yanzu ma tana asibiti Nagarta" bai,jira mai zai ce ba kit ya kashe.

A kid'ime ya tashi ya fice motar sa ya fafara ya Shiga direct nagarta hospital yaje mum na zaune yaje ko kallon sa ba tai ba sai daya kuma gaisa ta San nan ta amsa .
" Mum naji ance ta samu b'arewar ciki". Eh hakane dafe kai yayi abinda Mami Ke so da tayi hkr ta barmu a tare da tuni Ita zatafi kowa farin ciki.
Hawaye ya share ya tashi ya fita yace zai dawo, gida ya zarce shigar sa falon mami yaji hajar na waya.
"Ai in gaya miki yau mukai,waya na ci Mata mutunci ,wai Sun na gaya Mata magana mai d'aci ,ai zee tana bani matsawa" .
Duka taji ta ko Ina saida yayi Mata lilis San nan ya tsaya,lokacin Mami ta fito .
" Kai haidar me tai ma yana haki Mami tabbas itace silar b'arewar cikin zee wallahi".
"Au ciiki gareta, Ita bata samu lokacin da ake so ba.ai sai kayi hak'uri tunda zaka auri hajar irin haihuwa."
Kuka sosai take nan Mami ta Jawota tana bata hak'ur.
Fita yayi ya Shiga side din sa ,ji yake Kamar ya had'a kayan sa ya bar garin,ga tsananin kewar zee fake nuk'ur-k'usar sa, shawarar kb ya tuno na yayi hkr yaiwa maminsa biyayya insha Allahu ba zai tab'e ba..

*Story &Writting*
*Queen meemi*

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . . *ZEENATU by Queen meemi page45-46*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠. ♠
♠. ♠.
*® NWA*
*28 Oct 2016*

*Queenmeemi.WordPress.com*

Washegari da sassafe haidar ya tashi yaje ya sayo su fruit da yawa ya tafi nagarta hospital Ahankali ya bud'e d'akin ya Shiga zee ce zaune ta jin gina da fillow tana Shan tea, ganin sa yasa ta k'ware mum tace kiyi fa ahankali ,Sun gaisa da mum ya tambayi jikin zee .
Ita kam Sunkwai dakai tayi, yayinda 'kirjinta Ke bugawa ji take kamar tai hug d'in sa
Tsayuwa yayi ganin lokaci ya k'ure yasa ya d'ago sukaa had'a Ido da zee ya sakar Mata murmushi ,murmushi ne yaso sub'uce Mata sai ta basar don bata San yin dariyar," ya jiki zee"? .
Ahankali ta dago ,"tace da sauki".
Sallama yayi musu ya fita.
Mum ce ta tashi ta rik'e zee suka Shiga toilet ta fito wanka zee tayi ta fito tasa kaya ,shigar doctor d'akin ya je ya d'au file dinta ya duba ya d'an d'ago ya tambayeta, nan ta amsa mai da bata jin ciwo sai jiri da take ji .
"Karki damu kan Anjima zaki dawo narmal" nan ya rubuta musu sallama ,wajen 1 suka tafi gida Kafin yamma zee tayi garau.

*************

Direct haidar gun aikin dad yaje nan ma duk akan maganar komawar zee ne Amma dady ya bud'awa idon sa Toka yace shikam bazai wa zee dole ta koma ba ,Amma idan Shi ya Janyo hankalin ta to ,asanyaye haidar ya tashi ya tafi gidan su kb .
Wak'a Ke tashi a laptop d'in kb ta guzarish yaraf haidar ya zauna kb ya d'ago "ya aboki".
Haidar yace" kaide bar ni nasan me nake ciki ,matsalar dad din zee yaki bari ayi zancen dawo warta gashi banso iddar ta ta fita .
Kb yace" to kai na farko Mami ta amince ma kadawo da Ita"?.
"Aa kb
kwai nine"
"Lallai haidar kafara shawo matsalar ka da Mami kawai idan zamanka da zee bai k'are ba zata dawo.
Kuma kasan dole dad d'in ta yaji ba dad'i "
"Ya zancen auren naka da hajar".
K'aramin tsaki haidar yayi "kana son B'atan rai".
"to ya zakai dole kaiwa mamanka biyayyaa"

Shiru yayi na 'yan mintuna sukai sallama ya tafi.

*Bayan 2week*

Yau ake yinin hajar gidan ya cika da Mata sai kid'a Ke tashi hajar na zaune ad'aki Ita da k'awayenta sai dariya suke .
Wata ta kallo hajar tace "Amma fa kina da sa a kin auri Wanda zuciyar Ki Ke so".
tab'e baki hajar tayi kun san kwa gwagarmayar Dana sha ,kan na same shi ,sai da na fa rabashi da wan nan banzar matar tasa" ,tafawa sukai ai wata tace "ai dama Ke k'alatacciya ce".
"to ya San ranki".

Washegari aka d'aura auren hajar da haidar ji yake kamar ya mutu saboda bak'in ciki, fitowa yayi Daga d'aki don dama yace bazashi d'aurin auren ba jin gud'a acikin gida hantar cikinsa ta kad'a .

Hajar ya gano taci kwalliya Ita dasu husy ko kallo bata ishi Shi ba ,zuwa yayi ya d'au kayan sa kala 2 ya watsa a mota ya fafareta ya tafi gidan gonar sa don samun sa Ida.

*ZEENATU page47- 48*

*******

Kuka sosai zeey Ke kwasa tun safe data tashi jin amsa da sadiq ya bata na an d'aura auren haidar da hajar, kishi Ke nuk'ur-k'usar ta,da haushi

"Lalle zee kina da Aiki" cewar Mami,"na gaya miki Ki Maida komi ba komi ba ,kiyi hakuri kowanne bawa da irin tasa jarabawar,Kije kitchen Ki d'au abincinki kici".

Tashi tayi tana share hawaye ,sallama akai ta amsa magajiya ce wata mak'ociyar su ta shigo",Aa zeena saukar yaushe" murmushi tayi suka gaisa ,binta tayi da kallo ta jinjina kai.

Gaisawa sukai da mum take sanar Mata haihuwar k'anwarta,gulma na cinta ta basar ta tashi ta fita.

*******
Chapter 22 · 0% Book details