← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 35

Sashe 19

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yawwa Shi nagani ai sai ki tambayi Shi haidar in inya amince haka ita hajar din".
"Yo sai ya wani amince ai kawai idan yana son Albarka yayi mun Biyayya".

Hajar dake kitchen a lab'e ta daka tsalle tana rawa da Juyi,ganin hak'an ta ya kusa cimma ruwa.haka suka yanke shawarar inya dawo Ayi ta ta kare,wan nan ke nan.

Tunda akai Wanga magana hajar ta canja salon yiwa Zee rashin mutunci ,yauma da zeey ke zaune a fararen kujeru ita da sadeey tana karanta Mata novel suna ta dariya ganin yanda jarumar book din ke tinb'ele.
"Ke bani kujerar ki" sadeey ta juya hajar ce sai girgiza take tsam sadeey ta tashi ,zeey ta kalle ta "koma ki zauna".
Hajar tace" ni da kayan wana Amma anunan gadara".
tunkud'e sadeey tai taja kujerar a afusace Zee ta kai Mata maree tace wan nan ai k'arfin hali ne b'arawo da sallama, itama taja kujerar.
Nan suka hau kici-kici tas wayar hajar ta fadi k'asa ta tarwatse,saboda jin haushi yasa ta rarumi Zee nan fad'a ya kaure tuni zeey ta canjawa hajar kamanni .

Mami ce da husy suka fito "ke ba zaku rabu ba" sai da ta daka tsawa san nan suka hak'ura .

Mami "tace Amma ke kam ba ai sirukar arziki ba ki rasa dawa zaki fad'a sai da k'anwar mijinki" .
Hajar dake huci "tace mami wai daga d'aukan kujerar da kanwar ta ke kai yasa ta mareni ,ta fasan waya".

"Lalle kin samu sake ,don k'anwar taki tazo ci ranii shine zaki hana yar gida sakewa to wallahi ki kiyayeni idan Shi haidar dinne ya baki lasisin kiyi abinda kike to wallahi yazo,karshe sai kin rai na kanki ,yau da ace kina da juna biyu ne shine zan raga miki zeey dake kuka tace "mami kiyi hak'uri wallahi ita ke Shiga hurumi na,asali ita tazo ta same mu awajen" .

ko kallon ta ba tayi ba tace hajara su huce suka juya .,haka itama taja hannun sadeey suka shige gida,sadeey tace" wai ya zeey haka ake miki agidan nan ".
Bata ce komi ba itama sadeey shiru tayi da d'aukan aneeyar in ta koma gida zata sanar da mum.

**

Karfe 5 dai-dai saurayin husy yazo hajar tace zata had'a mai kayan motsa baki don salon tsokana gidan Zee ta Shiga ,suna zaune tanawa zeey kitso "ke zan dau aron cups da jugs na glass ,Zee ba tace komi ba zuwa tayi ta d'akko ta fita.
Tana tauna cewgum da harara.

Tsaki zeey tayi tace" banza kawai abinda kike mun insha Allah sai an maki irinsa,kuma ni da haidar mutu ka raba ,don zeey ta riga ta gano hajar na son haidar shiisa ma take wani abun da gayya

Text ne ya shigo wayar Zee kalaman soyayya ne daga haidar murmushi tayi ta Maida mai da reply ,muryar sa ta keji har tsakar kan ta ,jin yana Mata wasu shu'uman kala mai yasa taji kewar mijinta dama yana kusa da ita..I miss u so much,text ya kuma shigowa karantawa tayi da gudu ta shige d'aki tai flat a bed sai murmushi take tana birgima ,dai dai lokacin ya bugo waya nan da nan suka hau hira mai Dad'i take ta manta da duk wani b'acin rai .........

*Writting*
*Queen meemi*

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . *ZEENATU by Queen meemi page35-36*

♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
*®NWA*
*Dedicated to Lubie nd bena*

*After one month*

Haidar na zaune zeey na kusa da Shi ta Dora kanta saman kafar sa ,yana wasa da gashin ta, "babynah gini zan fara don so,nake na d'auke ki daga nan mu koma sabon gidan mu Kinga ko ma bar mami ta sake".

Dad'I ne ya ishi zeey "tace Allah ya yarda,kuma yasa mami ta yarda" ,hajara ce ta shigo sak'ale da jaka a hannu ta shigo falon ,had'e rai yayi "waya baki izinin shigowa" ?? Dariya tayi "mami ke kiranka" ta juya ta fita da murmushi kan fuskar ta ganin ta kusa cika burin ta, direct mota ta Shiga driver ya ja saboda yau zata koma gida ,Ga husy ma ta koma school.

Da sallama ya Shiga zama yayi ya k'urawa tv Ido ganin ana wani film,sakkowar mami yasa yayi murmushi "Barka da warhaka mami".
"Barkade my haidar" ,zama tayi ta kalle Shi "dama wata magana nakeso muyi dakai".

"Mami fadi Inaj inki," gyara zama tayi "aure nakeso ka kara" a firgice ya d'ago kai "mami aure kuma"?
"Eh Shi nake fada"
Dariya yayi "mami Yaushe nayi auren harda zan K'ara wani k'ark'ari fa yanzu wata hudu".

"Nuna min kalar ka, ai wuyanka yayi kauri saboda waccen figaggiyar ta hure ma kunne to ahir d'inka na gaya maka daga rana irin ta yau ka fara shiri ,don aure da hajara babu fashi".

D'ago kai yayi "mami don Allah ki janye maganar nan wallahi Banda ra ayin mata biyu".
"to ni kuma Inada buk'atar jika don naga alama matar ka bata shirya haihuwa ba ,ace wata hud'u yarinya bata fara laulayi ba, to bari ma kaji tun farko yarinyar batai mun ba don haka aure babu fashi ko kak'i ko kaso"

Kan sa ne yaji yana sarawa "mami pls kibar maganar hajara wallahi Sam yarinyar bata da kunya" .

"Aure de babu fashi idan kuma zaka nunan ban haifeka ba to Ga fili Ga mai doki,kuma nan ta wata biyu ba fashi" sama ta haye
tashi yayi ya fita ya tsaya dai-dai bakin kofa ya k'urawa sama Ido "mayya sa mami ta canja mun tun San da nai aure ,kwafa yayi dole ya saita wa hajara kamanni .

Wak'a take tana soya cincin ta baya ya rungumo ta my Zee ,juyawa tai tayi dariya "habiby ,bai ce komi ba sai sai Dan sakin jiki da yayi a bayanta , juyawa tayi "habiby yana Ga Kamar Wanda baka da lafiya" .
Baice komi ba ya kalleta ya cakule Mata kumatu "baby ba komi".
fita yayi ya Shiga motar sa tafiya mai nisa yayi ya tsaya ya dafe kai "oh mami pls ki janye" tsaki yayi ya d'auko wayar sa ya nemo layin hajara ,kashe murya tayi ta dauka "ke ni sa anki ne"?
Tace "me nayi kuma"?
"ke kika sani ,to wallahi ki janye duk wani k'udiri a ranki domin ni ba sa anki bane baki daga cikin tsarin matan da nake so ,if not wallahi zaki ga true colour dina stupid girl kawai" kit ya kashe.

Tashi tai zaune ta fita "umma wai yanzu ni ya haidar zai ciwa mutunci kan maganar auren nan".
umma "tace ki yi hak'uri bi komi a sannu dole dama afuskanci hakan ,inde yazo hannunki ai shike nan" ,nan ta had'e rai wallahi akan matarka zan huce.

Sai wajen 9 ya Shiga gida mami na sama ta d'aga labule ,dariya tayi "yaro man kaza wallahi dole ka auri yar uwarka".

Rungume shi zeey tayi habiby Ina kaje wallahi Ina ta jiranka kamo ta yayi ya ja hancin ta, na Dan je wani waje ne".
dariya tai "tace zo muje kai wanka kallon ta yayi no dear kawon abinci inajin yunwa after sai nayi.
d'akko flask tayi ta zuba mai white rice da miyar kifi da vegetables,tare da kunun aya mai sanyi ,ganin ya sa abincin agaba yana kallo ta taso "habiby kaci mana".

Ganin hakan yasa ta d'akko ta fara bashi abaki yana ci suna hira har ya cinye.

Tashi yayi ya shige d'aki yayi wanka yayi sallolinsa ya kwanta saboda jin kansa na ciwo, jin alamar bud'e kofa Sai yayi sauri ya juya ,kwanciya tayi ta bayan sa "habiby yau tabbas akwai abinda ke damun ka pls gaya mun."

"Baby ba komi kaina ke sarawa" ,tashi tayi ta d'akko mai magani ya sha da kyar de sukayi bacci kowa da irin tunanin sa.

*Washegari*

Mami tasa akai kiran zeey Shiga tayi da sallama mami ta kalleta ,"dama nasa a kiraki ki ne saboda in shaida miki karkiji Abu daga sama ,ni nan mahaifiyar haidar na bashi Mata ya aura kuma ba wata bace sai hajara ,saboda ke naga tunda ya aureki muke can jaras dashi don haka dole ya auri yar uwar sa".

Kukan data ke k'ok'arin had'iyewa yasa ya fito ,da gudu ta fita ta tsaya tana haki,"me nai ma matar nan? Ina dai dai gwargwado ganin na kyautata Mata duk bacin ranta bana so ,haka haidar dai dai gwargwado muna zaune lafiya,don Ban samu ciki yanzu ba har me wata hud'u shine za a San Ido",durk'ushewa tayi agun tana kuka ,tabbas basa k'aunata .

Mami ce tsaye a kanta tayi shirin fita ,"au ke naki salon kishin kenan tun d'azu daga miki zan cen aure kina nan kina kuka ,ko tare aka haifo ki keda da haidar ku?, to kisani mijin mace hud'u ne".

"Dan Allah mami kiyi hkr ,in wani abin nai miki , sai na gyara","baki min komi ba kawai inaso yayi aure ne" ,mota ta Shiga driver ya ja.

Tunda ta Shiga d'aki take kuka, bata tab'a ganin amaryar da wata hud'u da aure ace za ai Mata kishiya ba ,kayanta ta fara tattarawa tana kuka haidar ne ya shigo gidan jin alamun kuka yasa ya Shiga d'akin ,idon sa ne ya kai kan kayan da take had'awa ,Janyo ta yayi juyowa tayi ta kalle Shi ,rungumeta yayi nan ta kuma b'arkewa da kuka sosai ......

*Writting*
*Queen meemi*

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . *ZEENATU by Queen meemi page37-38*

♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
*®NWA*
*Dedicated to Lubie nd bena*

Queenmeemi.WordPress.com
Chapter 19 · 0% Book details