← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bubbuga bayanta yake sai da suka Dad'e a haka San nan ta zame jikinta, tana share fuskar ta kayan nata ta cigaba da had'awa sai da ta gama tsaf San nan ta d'ago haidar ya buga uban ta gumi "tawan wai me zaki da jaka ne ".
Cikin k'unar rai "tace zan tafi gidan masoya wato gidan iyayena ,yau aka shaida za aima aure ni kuwa dana zauna na ganka da wata gwanda na tafi gidan mu".
Damm! K'irjin sa ya buga ta Shi yayi ya kamo ta direct kan cinyar sa ta zauna "zeeta ki mini uzuri ba laifi na bane, jiya a binda yayi ta nuk'urk'usa ta kenan,baby ke nake so karki barni baza ai auren nan ba duk yanda zan Bazan yar da ba saboda ke kad'ai ce zabina ZEENATU Ina sonki son da bana ganin Kowacce mace zeena kina mun abubuwan dana keso to mai zai sa nai miki kishiya.
Zee mami ke da wan nan k'udurin don Allah ki zauna dani karki tafi nafi so ki kasan ce kullum kina tare dani saboda in bake Bazan iya ba".

"My habiby nima Ina tare da kai, Kayi mun alkawari wata ma hudu ace za ai mun kishiya ,donni nafi kowa bakin jini"

Sorry my baby d'aukan kayan yayi ya zazzage ya Maida su cikin wardrobe ,har wani D'an zazzabi Zee take ji, ganin hakan yasa haidar yaje restaurant yayo musu take a way ,da kyar take ci saboda d'acin data ke ji azuciyar ta ,abinda yake nuk'ur-k'usar Zee saboda ganin yanda mami ke Mata Sam ta rasa dalili .

*Bayan kwana 2*

Haidar da zeey sun manta da maganar auren da mami ta bijiro musu da Shi,soyayyar su kawai suke haka suka kuma lik'ewa tamkar mayen Karfe .

Mami Dake zaune a falo ta had'e rai tana jijjiga ,haidar na gefe husy na zaune gefen k'afar ta .
"Ban isaba ko? to wallahi na baka nan da one week muddin baka zo min da zancen ka Aminta ba to kasa aranka zaka Ga abin mamaki wallahi".
haidar ya dafa kansa jikin sa har rawa yake abubuwan sun Cakud'e mai "mami ko ni ta b'angarena beci ace na K'ara aure age D'ina ayanzu ba" .
Husy ta kalli mami yanda take ji tamkar ita za aiwa kishiya saboda Allah yayo ta da kishi ko wata taga zai ai wa kishiya sai taji haushi.
"Mami don Allah kiyi hakuri da zancen auren nan wallah tausayi Anty Zee ke bani ,duk abinda ma nai Mata watannin baya hajara ce ke zugani Amma wallahi yanzu tana ban tausayi Dan ba kiga yanda ta rame ba.
Wallahi mami duk da hajara sis D'ina ce Amma da kawai ki bar zancen auren nan tunda Kinga shima yaya haidar d'in baya so.

Gwab'e Mata baki tayi "yimun shiru shasha shar banza 'yar 'yar uwar tawa zai ce baya so to duk kunci gidan ku, wallahi idan kuka Ga ba ai auren nan ba wallahi sai in bana raye" .
Tashi haidar yayi "ni mami fa bana son ta".
kallon sa tayi "ni kake gaya wa haka take tasa kuka nan hankalin sa ya tashi ya zauna mami kiyi hakuri don Allah .
Kallon sa tayi wallahi sati d'ayan Dana baka inde ya cika to wallahi ko ka ki,ko kaso a babu ruwa na ,take ta tashi tayi d'aki nan husy ta Matso "ya haidar am so sorry komi zai dai- dai ta".
Kallon ta yayi sis "mayya sa mami ta daina so na? ,meya sa mami yanzu ba ta son farin cikina"? .
"Duk don saboda Zee batai Mata bane ba ,kayi hkr yaya dole mu bita ahankali tunda mahaifiyarmu ce".

Bayan kwana 2 gidan ya riki ce Sam mami batawa haidar magana gashi kullum sai Zee tasha zagi,yau ma Zee na zaune ta gama had'a kunun gyad'a sanin mami na son Shi ,hakan yasa ta d'auka ta tafi kai Mata .
Bayan ta gaishe ta ta ajiye kunun ,mami ta ya tsine fuska "ke d'auke wan nan shirmen naki kona watsa miki a jiki".
Zee "tace mami don naga kina k'aunar sa ne".
afusa ce ta d'au kunun ta watsa Mata a jiki, K'ara Zee ta saki ta mik'e tsaye . jikinta na rawa saboda zafin ya shige ta.
mami dake huci "wallahi yanda kika hanani sakewa Daa d'ans kema ba zakiji Dad'i ba shu'uma kawai, wai ke ki sisina ko " .
Da k'yar Zee ke taka k'afar ta ta fice daga gidan ta Shiga side din ta ta gyaraa jikinta ,wajen duk yayi jajawur alamar zai tashi Ga radadi daya ke Mata ruwan sanyi ta d'akko ta zuba agun san nan ta samu sa Ida.
Cigaba tai da kuka ta d'auko phone dinta zata bugawa mami ,gargadin da tai Mata lokacin da za a kawo ta ne akan rik'e sirri da yawaita hak'uri yasa ta aje ta fasa kiran.
"Na d'au Alk'awari ba Wanda zai San abinda nake ciki , Bazan gayawa yan uwana ba ,tabbas da can nayi k'uruciya da rashin hak'uri ,ashe haka hakuri yake da wahala, tabbas wani abin ke kore wani , gashi tsananin son haidar ,gashi yasa mun zan zama dashi hakuri yazame mun dole,na gode miki mum da kika jajirce ganin na koyi hakuri gashi yanzu na riske Shi a zaman aure na insha Allahu zan jure duk wani k'alubale".
haka tayi ta magan -ganun ta da kukan tamkar tana gaya wa wani, tashi ta shige daki ta kwanta baccin karfi da yaji ya zo Mata Wanda bata shirya yin sa ba ,tunda bata Dade da tashi ba..... ...

*Writting*
*Queen meemi*

. .
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . . . *ZEENATU by Queen meemi page39-40*
.

♠. ♠. ♠ ♠. ♠.
♠. ♠ . ♠
*®NWA*

*I Dedicated this page to Autarhajiya,Antysis,Anee, ummul fadeela &salamatu faransa thank for d care*

*Queenmeemi.wordpress.com*

Dama ita Rayuwa bata tab'a zama dai -dai yau fari gobe tsumma,duk yanda kake tsammanin rayuwar ka yanda ka tsara ta,kana tunanin hakan zai kasance to kayi kuskure yanda Allah ya tsara maka haka zaka bita,dole hak'uri ya zamo babban jigo arayuwar mu , hakuri baya tafiya abanza kuma mai hakuri Shi kan dafa dutse har yasha roman sa.

***********

Zee dake tsaye bakin gate tana jiran zuwan Anty bara domin tayi Mata waya tana kan hanya itada sadeey .zumud'i ne yasa ta kasa hakura taje k'ofa ta tsaya.motar mami ce ta Danni kai driver na tuk'i hajar ce ta fito bayan ta tsaya driver ya ciro Mata Jakarta ta shige ciki.

Adaidaita sahu ne ya tsaya Antybara suka fito shigar su gate din gidan zeey ta rungumeta tana murna part din ta suka shige ruwa da kunun aya ta kawo masu suka sha da yake 11 ne shiisa bata D'ora girki ba zama sukayi suna hira Anty sai bin Zee da kallo take.
"Zo nan Zee".
juyowa tayi tazo ta zauna "Anty Yasu boy sultee"? .
"yana boarding school".
"wai ni Zee baki da lafiya ne ,naga kinyi fiyau kinyi zuru-zuru"?.

Dariya tayi "nayi rashin lafiya ne Anty" haka sukai ta hira,bum aka falon hajara ce ke girgiza harara ta kai musu ta shige kitchen ta d'auko ragowar kunun data gani a gidan sanyi tayi waje.

Anty ta jinjina kai "oh ni bara yau naga gadara, ke Zee wan nan wace ta shigo ba sallama ta shige kitchen ta dauko Abu"?

Nan Zee ta tab'e baki kad'an ma kika gani Anty yar uwar su haidar ce wallahi haka take mini kullum .
tuno da auren ta da mami tace haidar sai ya yi yasa ba tai aune ba hawaye suka zubo Mata da gudu tayi d'aki.

Ahankali Anty ya tashi ta kwantar da baby data ke goyo ta bita d'akin.

Flat ta ganta kwance kan bed tana kuka zama tayi ta d'ago ta "my Zee Meya sameki ne ,?wai meya faru gaya minn".
shiru tayi ,Anty ta kuma tab'a ta "Zee ta .
Idan baki gayan ba wa zaki gayawa tunda dai daga gani akwai matsala".

Taso wa tayi ta rungume Anty "tace Anty basa sona tunda nai aure Banda kwanciyar hankali uwar mijina bata k'aunata kullum kyautata Mata nake Amma bata gani ,ita wadda kika Ga ta shigo cosin sis din sa ce ,to haka take mun gadarar nan ,yanzu matsalar mami tace wai sai haidar ya aureta saboda wai ni har yanzu ban samu ciki ba"

Hankakin Anty ne ya tashi tace "yanzu ,kina cikin matsalar nan Amma kikai shiru ba Wanda ya sani sai kace ba kida mafad'i, Ah lalle na yarda Zee kin zama silent yanzu ,kuma kinyi hankali".

Tashi tayi ta na kai kawo gaskiya banji dad'in wan nan abin ba, kina yarinya ace wan nan matsalar ta faru dake ta zaman aure Ga kuma kishiya ,sai dai ba zan zama uwar banza ba .
Zee abinda zan gaya miki ki K'ara hak'uri kinyi kyan kai daba ki kai maganar komi dangane da zaman aurenki gida ba ,tabbas haka yana da kyau ,ki dage da addua Allah shine masanin abinda ke fili da b'oye yawaita zakiri da hailala yana gusar da bak'in ciki karatun Qur ani ya zamo abin dubawar ki ,ki Maida komi ba komi ba Allah shine mai sakayya Ga duk Wanda Aka zalunta".

Taji dad'in nasihar Anty haka ta fito suka Shiga kitchen don D'ora sanwa,ba yanda Anty zatai Amma tana cikin damuwa idan ta kalli Zee da kishiya.

Sai wajen la asar ta tafi tana dad'a jaddada Mata ta K'ara hakuri.

Bayan zuwan Anty gida mum na falo tana ninke kaya,Anty ta zauna mami ta kalleta "har kindawo daga gun 'yar taki'? .

Murmushi tayi "lafiya Lau take kam" Amma sai dai niko ta sanar miki da zancen K'arin auren mijinta

Dafe kirjii !tayi bazata taji maganar nan dai Anty ta gaya mata duk abinda Zee ke ciki
Allah sarki Zee nayi Mata jinjina Anan Godia Ga Allah da yasa har ta iya boye hakan Aa ta zama mai hakuri.
Chapter 20 · 0% Book details