← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 35

Sashe 1

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.
. [9:24pm, 01/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page 1*
♠ ♠ ♠ ♠ ♠ ♠ ♠ ♠ ♠ ♠ .

®NWA * BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

*dedicated to bena &Lubie*

*Notes :Banyi wan nan littafi Dan cin zarafin wani,ko wata ba acikin littafin wani abun true ne wani Kuma na k'aga da kaina ne don ya k'ara armashi ,banyi don cin zarafin wani ko wata ba ,duk wanda yaga yai dede da lyf nasa Arashi ne*

**********

Sunday 13 ga watan July 2010 K'arfe goma da rabi 10am dede ta fito sanye d'aure da d'aurin k'irji ta d'ora karamin hijab da alama wanka Zatai, kitchen ta shiga ta fito ta d'anyi tsaki inda ta k'wala kiran .... "Sadiq! Sadiq! Wai kana inane "? Tsayawa tai tana huci da mirrow ahannu tana duba afuskarta Saboda kurkum en da ta saka ,tsaki tayi tai side en d'akin Sadiq ta shiga ta buga gadon da Sadiq keta sharara bacci. " Ah lallema bacci kake kwasa ko to wallahi sai ka tashi", sadiq ta fad'a da k'arfi ,tashi yai zaune yana mik'a tareda mutstsike Ido Alamar baccin bai sake shi ba,"haba ya zee me yasa sei mutum na bacci kizo Kina tashin sa? haba ay wan nan bayi bane" yai tsaki, "ah lalle Sadiq wuyanka yayi kauri to ka tashi kayo cefane don yanzu 11 don kaga mom da sauran 'yan gidan basa nan shine zaka kwanta ko so kake Ni naje gaka agida"? .

****** ***
"to Ni kad'ai ne agidan? ina Faty ita taje man seni da kika raina to wallahi baza Ni ba,kinsan dai Yau weekend wallahi ko kinfi Mayen k'arfe naci Yau ranar Hutu nane haka kawai kinsa kai na na ciwo kin wani saka Abu afuska kamar aljana" duka ta kai mai ya kau ce "wallahi saduqu Yau baka da kwano agidan nan sai dai kaci walk'iya " tashi yay ya nuna ta da yatsa "kifa Dena cemun saduqu idan bara ki ce mun Sadiq ba Ki shiru". " Anfad'a saduqu wallahi yau baka da abinci agidan nan ,Allah ya soka Yau 'yan fad'an basa kaina kasan de halina ,Yau cike nake dam da kud'I shi'isa zan saurarra maka ,don rashin kunya ina ya yarka muna sa'insa dakai" haushi ne ya ishe shi don ya tsani atada shi a bacci duk sai yaji wani iri, "malama Ki fita kona hamb'arar dake almasifatu kawai" dariya tai tace zaka gane kurenka ne Yau. . ********* fita tai ta banko mai k'ofar suk Dan yaji haushi ,wanko fuskarta tai abakin famfo ta shiga d'aki ta d'au mirrow ta duba fuskarta taga tai fes murmushi tai ta zari mayafi ta fita siiyan kayan miyaan....kad'an kenan Daga ZEENATU . . *© Queen meemi* .
[9:24pm, 01/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page2*
.
♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠.
. *®NWA*

. tafiya take da sauri sauri don ta siyo kayan miyan ta dawo da wuri ,bayan tayo cefanen munay da Aneesa kawayen ta na islamiyar su adede bakin bishiya suna hira ,munay tace" Aneesa kinga zee dama abinda Abu mai kitso tafad'a Gaskyne"? Aneesa tace" nifa ban San maganar ba ,nan munay ta janyo kunnen Aneesa ta rad'a mata dagowa tai "ke Dan Allah tab ,bari mu mata Magana ,Munay tace zeenat ,zee dake sauri Sam bata lura dasu ba jin Ana kiran ta ta juya arba tai dasu ahhh" manyan k'asa dama kuna nan" kallon juna sukai suka jun-jina kai. .

*************

gaisawa sukai inda Aneesa tace" wai ni zeenat mijin naki tafiya yai ne naganki agida wajen 2 month fa" ?,munay dake zungurar Aneesa kar ta Jan gwalo musu masifa nan kwaa zee ta aje Kayan miyan agefe ta gyara zaaman mayafinta "to magulmata ay dama tin sanda naji kun kirani nasan da gulma abakin ku ,to Dan k'aniyar ku meye ruwan ku da rayuwa ta idan ma kaso auren nai bata shafeku ba banzaye nade fi wanda ko lalle ba' a tab'a saka suba",Aneesa da yake tafi tafi munay fad'a ta kalleta ke dallah zee saurarra kinji mun ambaci kaso aure harda zakina cemana muna fukai ,tabbas maganar Abu mai kitso gaskiyace ashe anji kunya"ji kake tas tas zeena ta kai ma Aneesa maree tare da nuna ta da yatsa "Ni ba kanwar laasa bace kin san bana barin ta kwana karki manta zeemasifa Nake domin kinfi kowa sanina a school ban san gulma Kuma wallahi Abu mai kitso zata rena kanta munafukan banza da wofi ta kalli munay ta Harare ta ta d'au kayan miyanta tai gaba ,tana tafiya tana huci haka ta shiga gidan su Lokacin Sadiq ya biyo Faty zai daka bangaje zee tai take zee ta kamota ta d'uma mata dundu tahau ta da bala'I kuka sosai Faty Keyi "Kiyi hkr ya zee ya Sadiq ne ya biyoni zai dake Ni don na ta sheshi Daga barci ya ban Hansin zan sayo book " . . ************* "dallah malama yiwa mutane shuru kin san de saduqu mugune in yana mayen baccin nan nasa Ni matsa kiban gu karna huce akanki don raina abace yake" ,sanin Halin yayar tata yasa ta matsa. Aje mayafinta tai ta gyara kayan miyan duba agogo tai taga 12 tayi tsaki tad'ebi kad'an Daga kayan miyar zata jajjaga sanin idan tajira marked'e har 3 sai tai muusu ba agama ba ga blender ensu ta lalace ,sharp -sharp tai markad'en ta D'ora jallof rice ,sai wajen 2:30 ta gama ,bayan tayi wanka ,ta zuba musu itada Faty suna ci afalo sunsa film en D'an ibro suna kalla.

********

Sadiq ne ya fito Daga d'akinsa ya shiga kitchen ya d'au fillet ya bud'e flaks ya d'ebe abinci taf ya juya zai d'au spoon Faty ta shiga d'aukan cup da gudu ta juya "ya zee Sadiq ya hanani d'au ka da sauri zee ta fita ta shiga kitchen en ganin ya cika fillet da abinci yasa ta d'auke "wallahi saduqu baza kaci abincin nan ba" juyowa yai "wallahi sai naci ay bake kika kawo abincin ba " dan bani na kawo ba aini na girka nan nace kayo cefane kak'i " juyewa tai a flks ta d'auke takai can cikin d'akin mum nasu ganin ba sarki sai Allah ya fita yana tsaki ,yana k'wafa kofar gida yaje ya zauna , wajen 4 ya koma gidan ya gansu sai sharar bacci suke silalawa yai ya d'auke flask en ya iba ya aje a kitchen yaci ya fice .

**********

wajen 6 mum nasu suka dawo nan gida ya har gitse, zeena sai bala'I take kan Sadiq tad'au abinci saida mum ta bata hkr hira suke tayi sadiya me bin Sadiq sautsayi yasa ta zubarwa da zee humra enta, duka tai mata kuka sosai sadeey keyi mum na zaune a kan tabarma tai tsaki wai" ke zeena mesa Baki da hak'uri ne? Kome akai miki Saikin rama haba Baki da Aiki sai masifa ba zafa kizo Ki takurawa yarana ba mesa l Baki zamanki agidanki ba". Fitowa tai ta turo Baki da hijab tace Allah" mum Yau raina ab'ace yake" mum ta kalleta tace "haka de kurlum kice ranki ab'ace kide dunga Sawa zuciyanki ruwan sanyi ,ruwan alwala ta d'auko ta tsuguna tanayi "haba ayi mutum ba hkr "haushi ne ya isheta ta saka takalminta tai waje tana huci............... *©Queen meemi*
[9:24pm, 01/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page3*

. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠. ♠.
.
*®NWA*
. bayan fitarta bata zame ko ina ba sai gidan Abu mai kitso Sallama take ta dokawa kallon gidan tai ta tab'e Baki ,Sallama ta kuma dokawa Abu tafito Daga d'aki" Aa zeena ce Yau hala de yau kitson kike so wan nan uban kan naki me yawa da tsawo dama yaci ace Kina kitse shi Amma naga ke Baki son kitso". Hannu ta d'aga wa Abu alamar tai mata shuru ,kujera 'yar tsuguno ta d'auka ta zauna ta kalli Abu ta turo d'an kwalinta gaba. "Abu idan kin gama soki burutsun naki sai Ki tsaya na d'ora Daga inda kika tsaya,yanzu Abu abinda kikai ya dace kenan meye ruwanki dani wai zakina cewa nakaso aure harda gayawa su munay da gurmanki da komi ay wallahi badon ina jin kunayarki Dana miki tatas kin san Ni bana ragowa domin Ni zafi ce kana mun zan maka don haka akula don haka sai anjima", sakato Abun tai ta tab'e Baki tashigo d'aki domin tasan itace da lefi.

************

8:pm Zee na zaune tana gyara kayan business nata data keyi ,k'irrr wayarta tai k'ara dubawa tai taga me kiran tsaki tai ta basar wajen 3 times Ana bigowa Amma Batai pickin ba wayar aka kuma kira ra d'auka afusace "malam ko naci wani Abu bam baka ba zakana kirana kasan banida sauran wani issues dakai yanzu don haka leave me alone" Daga can akace pls" zee kiyi hkr balaifina bane ba kema kin sani baran iya rayuwa babu ke ba zee ta,pls ",tsaki tayi haidar na gayama ka k'yaleni kabi wani Sarkin" kit ta kashe wayar "ayi mutum da naci" .

*************

Sadiq ne ya shigo d'akin ganin kudi ahannun zeee yace "ah ya zee hannunki da kyau zama yai gefen ta yad'au wata powder Alin yana juyawa "nawa wan nan "?d'agowa tai ta kalleshi "600hundred me Zakai dashi kai ba mace ba "? Dariya yasa lalle" ashe haka kike cin kud'in mutane yanzu wan nan abar har 600 hundred tab Ni de in kin sai dan 200 gata "wait Sadiq wai me zakai da powder? "My fiancy zan sai dawa tana gogawa afuskar ta idan naje zance"dariya ta fara harda su tafi ,mum ce ta shigo d'akin Yau zeena da Sadiq ke shiri ,mum" ashe Sadiq nada budurwa da sauri ya toshe bakin ta ,Allah mum k'arya take k'arami dani zan budurwa abin ne yabaw mum dariya tace" ai Batai k'arya ba tunda yanzu zamani yazo don rashin kunya sai kaga yaro yaje gun wadda ta girmesa zance", "sosai ma mum ,harda cewa zai sai da mata tana shafawa afuskarta don yagani yaji dadi. "Allah mum k'arya take sai sunne kai yake ,kallonsa mum tai tace Banda de shirme yanzu karatu ne gabanka ba harkar Shime ba ,da gudu ya fita zee ta fashe da dariya.

****************
Chapter 1 · 0% Book details