← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 35

Sashe 26

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*9:30*
Haidar ya shigo yana waya bai Kula da ita ba sai jin kid'a da yayi ,ya juya ya ganta had'e rai yayi "yace hajara Daga Ina kike ? Wama ya baki izinin fita"?
Wani banzan kallo tayi mai, "malam ni na bawa kaina, ko ka manta ne?kai ko kunya Baka jiba ,za kazo kana neman inda nake ka damu dani ne?
To ka saurara min "
Kamota yayi ya matse Mata baki K'ara ta saka ,ni ka sake ni, gam ya rik'e bakin.
"Ki sani, ko baki aureni ba ni me iya hukunta Ki ne ,karki d'auka wai na damu da Ke ne ,NO kawai d'an cikin Ki nake tausayawa saboda nasan baki da sense ba kisan ciwo kanki ba ,kuma duk randa kika kuma fita wallahi se kin gane bakida wayo".
saikin ta yayi ya shige d'aki.

K'ara ta saki ta wangame baki "eh naji kome zaka ce wallahi duk randa nayi niya Sena fita, kuma wallahi ka sa tsiya kaida tsohuwarka duk sena b'arar da cikin inga ta tsiya".
jin alamar zai fito yasa ta fad'a d'aki ta banko.

*****************

*BAYAN WATA D'AYA*

*Ranar Monday da safe*
*8:00*

hajar ce ta fito sak'ale da jaka sai had'e rai take ,ga cikin ta ya d'an fito ,neman haidar take bata gansa ba ,domin yau zata fara zuwa awo.
K'arar bud'e k'ofa taji haidar ne ya fito shida Mami ya rik'ota zuwa yayi ya bud'e gaban mota zai saka ta ,da gudu hajar tazo ta tsaya ,"waje na ne ka kaita baya" .
Matsar da ita yayi ta dak'ire ta D'aga murya "wallahi Bazan matsa ba" "Ke wai mesa baki da nutsuwa ne? Haba mahaifyar tawa".
Turo baki tayi "haka kawai don anga mutum zai,fita sai Mata ta langwab'e tace ba lafiya, ai sai kabari sai ka kaini, San nan ka kaita daga baya".
Mari zai kai Mata, Mami tace ya bari zata koma ganin hakan yasa yace sai dai hajar taje ta hau adaidaita shikam inde be kai Mami ba Itama kwa ba zai kai ta ba.

Gidan baya Mami ta Shiga tace hajar ta Shiga gaba ,bayan da ya iya haka ya jasu yakai su hospital din.
Tana gaba tana harar Mami, zuwan su asibitin yasa suka fito, afusace hajar ta fito, tayi gaba har da takewa Mami k'afa. jinjina kai Mami tayi suka bita abaya.

Da daddare Mami na kwance kan 3seater sai kuka take ganin irin cin kashin da hajar tayi Mata. haidar ne ya shigo ganin tana kuka yace "Mami badai ciwon ne ya tashi ba"?
Share hawaye tayi "haidar da shine ai da da sauk'i akan cin kashin da hajar ta keyii min"
Numfashi taja "Wai Daga nace ta taimakan har rok'anta da Allah nayi ganin bana jin dad'I ta daman kunun gyad'a, haka ta ce baza tai ba, taimun rashin kunya ,har da cewa wai na sa mata Ido ,wai ita ba baiwa bace".
Bata bar ni haka ba , har sai data Bangaje ni, ta fita.

Fushi mai tsanani haidar yayi ya tashi a fusace nan Mami ta daka tar dashi zama yayi tace "haidar ayau Ina Dana sanin rabaka da salihar matar ka zeey ba abinda tai mun na k'warzabeta gashi ita kuma kullum kyautata mun take bata gajiya,bana mantawa akwai ranar da tayo mun kunun gyad'a, ni bama ni nace tayo mini ba ,ganin Ina sha awar sa yasa tayo mini. haka na watsa Mata Shi ajiki ,Tabbas na San alhakin ta ne ,dama Allah baya barin hak'k'in wani,gashi Ina ganin hajar yar uwar ka, aganina kamar ita ta dace dakai ,ashe ba haka abin yake ba,kuma nasan baka jin dad'in zama da ita".

Kuka ta cigaba da yi haidar na bata hak'uri
" Dole naje har gidan su zeenatu nayo bikon ta, tare da ban hak'uri.... Sorry fans

*Story Writting & editing*
*By*
*Queen meemi*

.
[9:38pm, 05/11/2016] Kaleesat basheer: . *ZEENATU by Queen meemipage 63-64*

. . . .
*®NWA*
mik'e wa yayi ya kamo hannun Mami "Allah Mami".
Juyi yayi "iluv u so much Mami" ,dariya tayi son na cusguna muku kaida zee abaya , nasa ka k'untata haidar ka yafen".
hannunta ya kama "Mami kin cancanci komi ,ni komi kikaimin Banda kamar Ki duk duniya naji dad'i da kika so zee,kidena ban hak'uri, har,abada Bazan tab'a biyanki abinda kikai mun ba tun Ina yaro, zan cigaba da miki biyayya inde abun bai sab'awa Sharia ba koda kuwa bana so"
"Hawaye ta share Allah yayi maka Albarka haidar" Amin yace.
Gyada zama yayi "Mami Inaga husy kawai ta dawo nan jigawa cuz bana son rashin ta a Kusa da Ke ,sai ai Mata Transfer uni ta nan"
Mami tace "Aa k'yaleta Naga tafi san can d'in kawai saidai ta koma zuwa duk week end, tunda ba wani nisa muke ba kano da jigawa".
"Ok Mami yanda kike so haka za ai".
Burum hajar ta shigo rik'e da ciki haidar ya buga Mata harara,nan ta ce cikinta na ciwo ya bata kud'i zata asibiti .
Banza yayi da ita saida Mami ta sa baki.gyara tsayuwa tayi dama nan kayo Ina ta nemanka,ko kallo bata ishe shiba.
ya d'akko dubu biyar ya mik'a Mata arene, amsa tayi.
"Yanzu dubu biyar za tai min kuwa"? . Ko kallonta baiba saima haushinta daya keji ganin irin abinda taiwa Mami ,gashi Mami ta hanashi d'aukan mataki,karamin tsaki yayi ya fita..
Tuwon samobita ta gani agefe yaji manshanu nan ta d'auke ta fara ci mum tace "to fitsararriya Nawa ne" .
"Mami sede Ki hak'uri don d'an da kuka k'wallafawa rai yana buk'ata ".
fita tayi Mami ta tafa hannu "oh ni na janyowa D'ana jangwam ,dama ciwon k'arya ne,gashi ko kunya ta bata ji".nan ta jinjina kai ta tashi jin k'afar ta tayi nauyi tayi bedroom.

*Zeenatu*

Tafiya take a Kusa da department d'in su munay da Aneesa , jiran su take ga rana Ana dokawa ,zee tace wallahi yunwa nakeji,yau lecture ta kwad'a ni gashi sunk'I fitowa da wuri,nan Aneesa ta tawo, zee "tace Ina munay"?.
Aneesa tace" tana zuwa yanzu, ke nifa school d'in nan tafara fita araina kullum malamai sita kwad'a mutane".
Zee tace "to ya za ai dama haka karatun yake" munay ce ta tawo tace "ku sorryn ku handout d'ina na karb'o gun lollipop kinsan ta yanzu sai ta b'atar.
Dariya suka sa suna Tafiya suna hira dai-dai lokacin wayar Aneesa tai K'ara ta d'aga, "oke nawan gamu nan" .
Munay tace "hala dai hubby dinne"? Aneesa tace ya San ranki shine mana".
Bakin titi suka tsaya Zuu mota ta tsaya fitowa kb yayi ya matso Aa my Aneee nan ya bud'e Mata gaban mota, kallon su zee tayi ta ce "ku shigo".
D'ago kai zee tai suka had'o Ido da zee kb yace "OMG! zeenatu ,kanmu bisa wuyanmu ,Kullum muna bada hak'uri".
murmushi tayi "ai niba komi nasan komi muk'addari ne".
Anee tace" kin San Shi ne"? kb yayi carab "yace Haba matar haidar ce da muka rasa".
"Abokin haidar ne kai ashe"?.
"eh mana amini kuwa tun muna yara"
Haka dai sukai hira har suka ya kaisu .

********

Ihu zeey tasa mum daga d'aki tace"ke meye "?
"Mami wallahi duk jewels da makeup set d'in nan duk an saye am very happy" mum tace "ai haka ake so zee,.
Yawwa d'azu iyayen ma'ruf suka zo kina school".
Gaban ta ne ya fad'i tace" Mami me sukazo yi" tace "gidanku suka zo yi" .
Shiru tayi bata ce komi ba mum tace "to sunzo kan maganar kune keda ma'ruf kuma an dai-dai ta har sun aje kud'in zance duk da Ke bazawara ce Amma ma'aruf ya dage sai ankawo ,Kinga ikon Allah ko zee? ai wani hanin ga Allah baiwa ne".
Zee da idon ta ya ciko da hawaye tace "Mami ayni ban sani ba"?.
Mum tace "ke karki maidamu k'ana nan mutane mana? ,bafa mi miki dole ba tsaf dai sai da babanku ya tambayeki shekaran jiya ki kace kin amince, kina son ma 'aruf".
Zee tace "Mami bafa haka nake nufi ba" .
Mum tace" ah to".
D'akin su ta shige, ta latso wayar munay ,tana d'auka tace "dalla malama ashe ke kin San yau za ai maganar mu, shine kikai shiru ko?duk kuka binne ni ba Wanda ya gayan ko yayan naki"
Munay tace" nima ban fa sani ba".
zee tace "to d'azu dai ankawo kud'I ,kinji sai kace wata budurwa".
ihu da murna munay tayi tace "to dalla meye marabarki da budurwar. wata budurwar ma tafi ki shekaru da girma ,nan tace "bari na fesawa Anee".
zee tace ni zaki kashen dodon kunne, duk in cikan kunne".Dariya tayi suka kashe a tare.
haka dai suka gama hirar su suka kashe.

*Story Writting & editing*
*By*
*Queen meemi*
Chapter 26 · 0% Book details