← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 35

Sashe 14

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami kuwa bayan haidar ya sanar da ita gidan da zai,saya wato gidan da zai zauna .
Nan tace tunda ga su da part ba kowa aciki ,a nan gidan mai girma Kawai ya hak'ura yazo d'ayan part en Wanda gidan in ka shigo Shi bayan parkin space babba , to sai part in guda 2 d'ayan shine Wanda su mami suke ciki, ayan Shi kuma dama arufe yake to nan mami tace haidar ya shiga, dama agyare yake tunda ba zama akai aciki ba .
Shidai haidar ya fiso ya tafi da Amaryar sa wani gidan ba nan gidan nasu ba , saboda yanda yake so su munji soyayyr su ,baiji Dad'i ba Amma ba yanda ya iya tunda hakan mami take so, kuma ba yanda zai yi tunda bashi da wadda ta fita dole ya bita kuma.

Haka aka fara a gyaran side en duk wani kayan more rayuwa haidar siyowa yake amak'ala .

A b'angaren zee kuwa abubaw Sun kacame Mata ga shirrin biki ga exams duk ta rame Abinci ma da k'yar ta keci duk Alhinin auren take Dan ma su Aneer da munay na tayata.........

*Written*

*By*

*Queen meemi*
*Queenmeemi.WordPress.com*

.
[9:18am, 02/11/2016] meemi basheer: . . . *ZEENATU by Queen meemi page26*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠. ♠. ♠.
*®NWA*
*dedicated to Lubie & bena*
*11oct 2016]*

Lokaci sai tafiya yake tare da burukan Mutane Wanda ke cikin farin ciki ya koma bak'in ciki haka Wanda ke cikin bak'in ciki, dama rayuwa bata tab'a zama d'aya haka lokacin bikin su zeena ya k'ara to dama duk abinda aka sawa rana sayya zo.

Saura kwana goma bikin su zeena ,yayin da gidajen biyu kowa sai shirye-shirye suke. zeena kuwa suna tsaka da exams ta dage sosai saboda wan nan ce damar ta ta k'arshe, yau ma agajiye ta dawo, bayan tai wanka suka tafi gun tailor Kai d'inkin fitar biki.

Sunje bakin titi itada Munay taji kanta na Sara wa, nan ta dafe munay tace "zee ki koma gida Ni zan je wai bakiga yanda kika rame bane? ga exams ga shirin biki".
Zee "tace to ya zan munay dole nai kuma gashi inaso nai karatu gobe".
pls" Kije jikina ba k'wari"
Munay "tace to zee".
Haka ta koma gida,mum na tsakar gida ta shiga Kawai juya ta d'auke ta ta fad'i k'ass da gudu mum ta zo ta d'ago ta tana shafa fuskarta.
"Zeena kina samun hutu kinji tunda Allah ma ya had'aki da k'awayen kirki ki bari su aiwatar da komi: ke kuma sai ki zauna tunda ma kun kusa final exams ".
Sai da nutsuwa tazowa zee san nan ta tashi suka shiga aki,mum" tace kinga ma gobe mai gyaran jiki zata fara zuwa Tanai miki. daga school ba inda zaki Kara zuwa".

*After 1 week later*

Yau su zee ke final exams tun safe sai 3 suka fito, tana fitowa ta hau kuka saboda next week ta zama matar wani balalle ta kuma ganin school mate nata ba,haka sukai musayar numbers da frnds nata san nan ta basu iv na bikin ta duk Sun mata Alk'awarin zuwa.

Cikin farin ciki ta koma gida tsayuwarta a Adai-data sahu haidar na tsayawa Shiva a motar sa ,murmushi yayi "congratulation my Queen Amaryata, yau kin k'are school sai kuma wata ".
Murmushi Tayi "Angona ke nan Naga har ka fara k'yallin angon cin" .
"nikam ka ganni sai ramewa nake" .
"bakya cin abinci ne babyna amma tunda kin gama exams pls ki dai na fita".
bu e motar sa yayi ya akko ice cream da shawarma ya mik'a Mata ahankali ta karb'a "pls dea kije kici in kuma ba haka ba wallahi zan shigo gun mum na baki da kaina".
harara ta daka mai da murmushi, "bashi kika auka dea".
aguje ta shiga cikin gida murmushi yay bita da Shi .
Dama ganin ta yazo yi sai Kawai ya shiga motar sa ya figa gurin frnds nasa don,rabon iv.

***************

Gyaran jiki ake wa zeena tunda aka fara ko nan da can bata fita, kwana 2 kenan da farawa da yake Allah ya yita fatar ta mai kyau ce. nan da nan tai sulb'i ta K'ara haske ga wani asirtaccen kyau da take zuwa bawa gashi duk inda ta xauna ta tashi kamshin turare zaka ji tana yi gashin shima yana Shan gyara,haidar kam tun san da suka had'u bai sake ganin ta ba saboda bata fita ko nan da can.
Aneesa da munay ne keta zirga -zirga sai kuma sadeey dake taya su.

Yau shine ranar da za a fara biki ,zee ce cikin shiga ta Alfarma hannun nan yaci zanen fulawa bak'I da ja haka k'afarnan Tayi balain kyau, kamar ka sace ta ka gudu da ita, fuskar nan sai sheki take true colour enta ta fito rad'au Masha Allah.

An gudanar da kamu lafiya
Washegari da juma'a akai walima nan ma fa ar irin kyan da zee tai b'ata lokaci ne Anty bara ta gyara ta sosai domin itama ta zo dangun su na ensa da kusa nan ma haka aka gudanar da walimar ansha hotuna zeena da k'awayen ta da 'yan uwa.
Haka akayi aka watse.

*Washe gari*

Yau daya kama asabar rabar ne dubban jama a suka shaida d'aurin auren ZEENATU DA ALIYU HAIDAR bayan Mata suka zarce da yinin manya aka ci akasha mai kid'an kwarya na bidirin ta .

Wajen K'arfe 8 angwaye da Amare suka tafi dinner inda nan ma fad'ar kyan zee da haidar kamar ka sace su ka gudu Allah yayi halitta sai dai mi musu,fatan zama lfy
Haka akayi aka watse dai dai Karfe 10.

Washegari shine ranar da aka mik'a zeena gidan mijinx ta Karfe 6 na yamma zo kuga yanda zeena ke kuka harda Amai sai da aka canja Mata kwalliya,nan ta k'an-ka'me mum sadiq da su sadeey faty har,da boy Khalid Wanda ba a dad'e da Haifa ba .
Dak'yar aka sata mota su munay da Aneesa suka rufa Mata baya saboda sabo har kuka sukai.

Tamfatsetsen gidan ta aka shigar da ita inda direct wajen mami aka mika ta. inda yake Cike da 'yan biki Nasiha akai Ma zee san nan aka Mik'a Amanar ta gun zee ,bangaren ta aka kaita part enta Mutane suka watse aka barta da ita dasu munay kafin angwaye suzo ,

Auren yak'in Mata ... Bari na dakata anan kafin zuwan angonta

*Written*
*by*
*Queen meemi*
*Queenmeemi.WordPress.com*

.
[9:18am, 02/11/2016] meemi basheer: . . *ZEENATU by Queen meemi page27*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠ ♠. ♠. ♠
*®NWA*
*Dedicated to Lubie & bena*

Haka suka zauna sai hira suke suna K'ara kallon akin ganin yanda aka cika Mata Shi da kaya munay tace kinfa more zeey ga handsome husband ga gidan ki mai kyau" Aneesa tace ko kin manta ba ita ka ai bace a gidan "?
Ita dai tana duk'un-k'une tana kuka motor ango ce da abokansa suka dira hayaninyar su ita tasa su munay Shiru direct aki haidar ya shiga nan su Aneesa sukace Ango kasha kamshi.
"to ko zaku ce k'awar taku ta fito falo za a gaisa"
Ahankali ta mik'e haidar ya bita da ido yana murmushi haka su Anee ma suka au mayafan su suka fita.
Shak'iyanci sosai abokanan ango ke mai kb daya kafawa Aneesa ido tun shigowarta falon don tai mai.
Shafa hab'ar sa yai to" Amarya ga ango nan Allah ya bada zama lfy ya kad'e fitina ya kawo 'yan 3" .
Haidar na tsaye "oya kb time fa ya cika 'ibrhm yace lalle anyi abun kai haidar"
Haidar yace" naji gwauro" haka sukai musu nasiha ibrhm ya rufe da addua .wani taf keken kwali suka aje Cike yake da kayan make -up mayuka da su lemuka da kud'i ha fa kayan sayan baki nan.
Haka suka tashi su Aneesa ma sukai Mata sallama da k'yar ta sake su jikin ta har zafi ya d'auka kamar mai zazzabi.
Bayan tafiyar su tana falo tana kuka, haidar ya rufe gidan ya shigo ya zauna gefen ta.
"wan nan rana itace ranar da nake jira Allah na godema daka mallakan farin cikina".

Tashi tai ta shige aki ta kwanta kan gado saboda jin kanta da tai yana ciwo. ahankali ta tashi cikin jiri saboda tun safe bata ci Abinci ba, sai aukin kuka.
Jiri ne ya kwashe ta saura kad'an ta fad'i k'as caraf haidar ya rik'o ta yayin da ya k'urawa manyan idanuwan ta kallo, girar ta ya shafa da lips enta ,d'ago ta yai ya rungumeta yana jin wani iri ajikin sa tamkar mai jin sleep.
Ita kam lafewa ta kumai ajikinsa jikinta ba K'wari gam -gam ya matse ta.
san nan ya saketa ya d'auketa cak ya kwantar da ita akan bed jikinta ya tab'a yaji zafi zauuuuu.
Toilet ya shiga ya murd'o ruwan zafi a wata yar roba ya auko Sabon towel ya fito bakin gadon ya zauna yasa towel en cikin robar ya Matso ruwan ya matse ya dannna Mata a wuyan ta .
Kar-karwa jikin ta yake take ya tashi ya cire Mata. rigarta haka yai ta dad-dadna Mata, yana Mata tausa ,magani ya auko panadol ya bata tasha kallon sa take Cike da so da k'auna, har wata kunya da ta shige ta ganin yanda idanuwan sa suka k'an-k'ance yana Mata wani wahalallen kallo.
Bayan ya gamai Mata ya akko fresh milk da gasasshiyar kaza yana bata a abaki .
"Pls my choculate kici mana ,jikin ki fa rawa yake saboda rashin cin abinci, ya tsine fuska tai "dear na koshi fa".
Ganin ya damu yasa taci kad'an tasha fresh milk en tanaci yana danna Mata jikin ta ,cikin k'an-k'anin lokaci taji kwari a jikin ta. already dama tai sallahr ta haka tabi lafiyar gado.
Sai da yai nafila san nan yakwan ta abayan ta ya sak'alo hannun sa ya Matso da ita ajikin sa, take bacci ya sureshi da wani Dad'i da yake ji aran sa ganin zee kwance kusa dashi.

************
Chapter 14 · 0% Book details