← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 35

Sashe 31

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau ne aka shiga satin bikin zee da yake ma ambasu Hutu shiisa abiin yazo Mata da sauk'i duk wasu d'unkunan ta yana wajen su anee su zasu kai sun dai Nace sai sunyi event ko d'aya ne ,Anty bara kam yar sokoto ta d'akko tundaga kano aka fara gyara zee tana zaune suna hira ta fara fitowa ragad'ad'au ma'aruf ya bugo Mata waya yana tambayar ta yawan kud'in data keso na lunch nan ta had'ashi da anee Anty Bara Ke kiran sadiq Dan yazo ya sayo lemuka zee tace Anty "Ay tun last week ya tafi school kin san ya shiga KUST wudil" Anty bara tace "maaha Allah nayi Mai murna ,ashe badashi zany kaiki d'akin ma 'aruf ba" zee tace "wallahi nayi missn sadiq abokin fad'a na".

Thursday suka fara biki duk daba auren fari bane nan dai akayi lunch police band na buga kid'a su anee an cashe ga frnds nata na school sunyi kyau sai selfie suke gwanin sha 'awa zeey tayi kyau tamkar flower an taru sosai akaci aka sha aka watse washegari Friday akayi lecture inda ummu samha tayi magana akan muhimmacin aure da zaman aure da hak'uri acikin sa nan ma kafin magrib an watse.

Washegari ta kama Saturday wato ranar d'aurin aure zee ta had'u ta had'e da yake ta D'an Kara k'iba kad'an sai tafi kyau duk inda tayi walwali take k'afarta da hannu duk an mulmule Shi da k'unshi an yarfa Mata kitso mitsi-mitsi tamkar ka sace ta ka gudu an d'auro auren a masallacin jumma'a jama a da dama duk suka dawo gidan don cin abinci

fateey ce ta shiga gidan da su zeey Ke tattare da k'awayenta tana haki "ya zeey wallahi bada ya ma'aruf aka d'aura ba! anee da munay suka mik'e zeey tace "to dawa aka d'aura" falfalawa da gudu tayi "Nima bansani ba"...

"to masu karatu ku biyo ni don jin wanga wan nan sauyi da aka samu".

*story writte &edited*
*by Queen meemi*
[3:52pm, 18/11/2016] Queen💋Meemi: . *ZEENATU byQueen meemipage 85-86*
â™ . â™ . â™ 
â™ . â™ . â™ 

*NWA*

*Queenmeemi.WordPress.com*

*dedicated this page to oll fans of ZEENATU*

kuma dawo wa fatee tayi tace"ya zee nifa banma sani ko gaske ne ko ba gaske ba, kawai de naji kamar maroki ba ya ma'aruf yake ambata ba",munay ce tace "Ke tsaya" fita sukayi tare ganin sabuwa na k'ok'arin shiga gidan su zee yasa munay ta tsaida ita "sabuwa wai bada ma'aruf aka d'aura ba"? sabuwa tace "eh man kinga ikon Allah ko",sai dai bansan dawa aka d'aura ba "dankari" munay tace wayar ta d'auko Layin ma'aruf ta latsa daga can ya d'auka "ya ma'aruf me nakeji haka wai dagaske ba da kai aka d'aura ba"? "eh mana" munay tace "to maiya sa ya ma aruf"? nan yace "in kinzo gida kyaji dalili" a salub'e ta koma gidan da suke zee na kwance ta tashi "dagaske ne"? "eh mana wallahi Yanzu ya ma'aruf Ke gayan" dafe kai tayi tasa kuka "ni to dawa aka d'auran aure na shiga uku" lallashin ta suka shiga yi Amma kamar zugata suke dai-dai lokacin Anty bara ta shigo,nan ta kama zee tace "muje gida mum nason ganin ki", san nan ta kalli su Anee tace"ku jirata".

Bayan sunfita direct falon dad ta shigar da ita dad da mum ne a zaune dad yace "zeey zauna anan" nan ta zauna tana kuka mami tace "rabon kwad'o ko yana sama sayya samu,ikon Allah yafi ga haka ,an d'aura aurenki da haidar ba ma'aruf ba" d'ago kai tayi da sauri tace "mum garin yaya Bayan haidar baya kasar"? mum tace Nima dai bansan dalili ba dai dazu babanku Ke gaya mini.

dad yace "baba Alhaji abokin kaka shine yazo ya Sameni da maganar duk da ina jin nauyin sa, Amma haka nace an gama magana da wasu sai dai hakuri,to Bayan yabar nan direct gidan su ma'aruf yaje ya tattaushe su baban ma'aruf yace bashine da auren ba nan ya kira mami sukaje gun ma'aruf mami har dasu kuka dan ya bari a d'aura da haidar tace ya kamu da hawan jini gashi yabar ma k'asar duk Dan saboda Ke haka dai aka had'u dad da baban ma'aruf da baba Alhaji da mami nan ma kukan tayi tausayi yasa maaruf yace ya janye shine fa aka daura da haidar,hatta kayan lefe yace yabar miki Amma Nace aa dole ya anshi abinsa anjima Bayan an kaiki za a kaimusu lefen su,zeey tace "Allah sarki ma'aruf" nan ta tashi ta fita no d'in ma'aruf ta buga ya d'auka ,kuka ta saka "ya ykai haka" nan ya hau bata hkr yace "zeey ki k'addara dama bani ne mijinki ba, bansan lokacin danace na hak'ura ba ,sai kuma Yanzu zuciya ta Ke tuk'uk'i da Dana sani domin duk wanda ya sameki ya more, Amma babu komi haka Allah ya k'addaro ina maki Fatan alheri" k'it ya kashe wayar tabi wayar Tata da kallo cike da mamaki, haka ta koma su Anee sunyi cirko-cirko nan ta zube ta gaya musu tana kuka.

munay kam rik'o ta tayi "tace karki damu duk danima naso ace anyi da yayana don zumuncin mu ya d'ore Amma Allah bai yiba Yanzu kawai ki fiskanci gaba dama can haidar naki ne ,kin fidda rai dashi gashikuma ya dawo"

k'arfe 6 dai-dai aka zarce da zee tamfatse-tsen gidan ta wanda haidar ya fara ginawa mami ta hanashi Yanzu da kanta tace a kaita can d'in,gida ya tsaru kamar ka sace kasa ajaka abin mamaki mami ce agidan ita da husy zuwan su zee da sauri ta rungumeta tana welcome back my douter anan ma saida ta kuma neman afuwar zee ita kam tace ba komai kowa ya tafi akabar zee husy dasu Anee .

mami ce ta tsaida kb tace to kb "kaga haidar baisan am Maida auren sa da zee ba ,to nasan ka sai ka gaya Mai karka gayamai saboda ina son yimai suprise ne, don bakaga fad'i tashin danai kan adawo Mai da ita ba ,so nake yanda nasa ya rabu da ita gashi na dawo Mai da ita kaga na wanke kaina,haidar yayi min biyayya wallahi",kb yace "mami muna godia kuma insha Allahu Bazan gaya maiba" "yawwa kb sai de kagaya Mai ya dawo gida ka dai son yanda zakai Mai" kb yace "masha Allah mami godia muke ,dad'i ne yayi wa kb yawa ya fafari mota itama mami tashiga nata motar driver yaja .

to makaranta Baku tambayeni labarin hajar ba ?.
kodai Baku tambayeni ba insha Allahu komi zai gudana daga taskar yar mutan kano,karku bari abaku labari.

*story writte & editted*
*by Queen meemi*
[5:57pm, 19/11/2016] Queen💋Meemi: *ZEENATU by Queen meemi page 86-87*

â™ . â™ . â™  â™ . â™ .
*NWA*

*Queenmeemi.WordPress.com*

zee na zaune sai kallon d'akin take Anee tace "su zee manya gaki kuma kin dawo wa haidar",munay tace "kuka ya k'are" husy ta dafa zee ta ce "naji dad'in dawo warki zee domin ya haidar kullum sumbatunki yake" ,su Anee su ka k'yalk'yale da Dariya munay tace "ai sai su had'iye juna Yanzu" zee ta d'aka Mata duka tashi sukai suna zagaye gidan sama da k'asa ne duk abinda Ke a k'asa shike a sama ko ina zam -zam da kaya kiran magrib da akai yasa su Anee sukai haramar tafiya nan zee ta rik'esu su tana kuka "Banda kamar ku a k'awaye kun zame mun 'yan uwa Allah ya barmu tare ya kaimu aurenku kuma" jikinsu asanyaye suka tafi da yake dama kb ne zai Maida su haka gidan ya zauna daga zee sai husy ita zata na tayata kwana kan haidar ya dawo,hira suke tayi nan suka dad'a saita guraren sunayi suna hira wajen 8:pm driver ya kawo lafiyayyen abinci daga gidan mami wan nan Ke nan.

kb dake zaune da laptop agabansa suna magana da haidar ta email nan yake ce Mai "shegen sama ka dawo gida kaga abin mamaki haidar dake zaune a farfajiyar hotel d'in da yake ya yinda k'afa fuwansa Ke cikin swiming pool d'in gefe laptop ce a ajiye, ya Maida Mai da sak'o ai na kusa nida bawo sai baba tagani" "kb yace matarka da babynka na jiranka tsaki haidar yayi "na bada amaanar su gun mami",kb yace "kai zancen gaskiya kawai ka dawo idan ba hakaba ta wuceka pls wallahi da gaske nake" haidar yace "ok ka saurareni next week" kb yace "oh no yayi yawa kawai ina laifin jibi,haidar yace dad'ina dakai naci kb" " no problem by the grace of GOD wenesday ina Nigeria" kb yace "okey ko kaifa Ana gaya maka kana kubcewa" haka dai suka gama hirar.

hajar dake tumbotsai ta had'a kaya akwati ummm Ke ce Mata gana "hajar ko fa Arba'in bakiba ya zaki koma Bayan mami ma ban gaya Mata ba,zumud'in me kike Bayan saura 10days ki arbain d'in",hajar tace "barni umma wai ni za'aiwa cin kashi wan nan zee d'in za'adawo da ita to wallahi koni ko ita duk munafurcin mami ne" kau! kakeji umma ta kaiwa hajar Mari kuka tasa "Allah umma Yanzu bakya sona" umma tace "ai dole kin canja hali, agabana kicewa yayata munafuka wallahi hajar ina ji miki na dama, sai kuma ki bari Alhaji ya dawo kya tafi" cike da jin haushi taja jaka k'irrr ta fita Mai taxy ta tara shiya loda akwatinan ta a cikin jaka tana rik'e da baby umma na kiranta ko kulawa batai ba yaja suka tafi.
Chapter 31 · 0% Book details