← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari garau zee ta mik'e wanka ta feso ta fesa kwalliya ta fita falo sai tashin k'amshi take fuskar nan fiyau ,tana kallon gidan k'arshe ta dire a kitchen nan ta hau k'ok'rin yi musu toye-toye.
Jitai haidar ya sak'alo ta ta baya ya kwanto kansa a wuyanta nan k'amshin jikinsu had'e "my baby good morning "
Lafiya Lau kai fa"?
Same u my choco"
"Waya baki izinin shiga kitchen yau ko so kike ko wahalar min da kanki"?.
" dear gani nai ya kamata" "to ki bari mami zata kawo".

'Yar aikin mami ce ta shigo da flask a hannu ta aje "gashi inji mami wai tana gaisheku.
"Zee tace kice mungode".
Zama sukai kan dining suna break shiya bata itama tana bashi.
Haka suka gama ciyar da junan su, haidar ya kashe phones ensa suka koma aki yana tayata jera ka yanta a wardrobe,haka tun safe suna ask'ale da juna duk inda tai sayya bita.
Wajen k'arfe 8 na dare suna zaune a falo manne da juna haidar na wasa da gashin zee ji yake tamkar ya had'iyeta ,ita kanta zee jin sa take har ranta tashi yai ya mik'ar da ita tsaye ya rungumeta hannunta ya rik'e suka shige bedroom sukayo Alwala sukai sallar nafila ta godia ga Allah.
Hira suka hauyi tun farkon had'uwar su sai dariya suke, A hankali hirar tasu ta koma ta soyayya take zuciyoyun su suka zurfafa ganin yanda suka Lula dausayin masoya tamkar saci babu yasa na fito na rufo kofar......

*Washegari*

Cike da farin ciki,haidar ya mik'e wani soyayuar ta yakeji a ransa musamman in ya tuno daren jiya, zee kwa in Banda kunya ba abinda take yi.
Wajen K'arfe goma suna zaune kan 2seater sunci wanka da kwalliya sai tashin k'amshi suke ,in banda soyewa ba abinda suke.
wayar haidar tai k'ara ganin kiran mami ya d'aga da sauri.
Ba tare da komi,ba tace" kazo ina nai manka",k'it ta kashe a hankali ya mik'e yace "tawan mami na kirana bari na je".
"dea ko nazo muje" ? "Bari na dawo sai ko je".
Oke habiby
Shiga yai mami na kan dining tana Shan kunun gyad'a.
"mami ina kwana".
Kallonsa tai" sannu ango tun jiya ina lura da kai bakaje sallahr asuba ba ko"?
"Mami naje ta k'aramar kofa na fita bata get ba, kuma bada motana na fita ba".
"To ya dace ace yau 3 days kenan ace matar ka ba tazo ta Gai dani ba"
"Ayi hkr mami tace zata shigo nace ta bari sai gobe"
"Yayi maka kyau haidar.
To dama husy ce ke so ka bata no en Amaryar ka, ta buga tata akashe yanzu ma tai mun waya kasan jiya tabi Su Anty kano zatai holiday kamin exams nasu,ya fito".
"To mami za atura Mata".

"To kadai gyara tabbas zan kiraka da asuba ka dunga fita don wan Amaryar taka da alama kanai -naye ka zatai"
Kai mum zee fa good girl ce, tashi yay ya fita
.....
Ku dakacen my fans ,kuci gaba da kasancewa da Queen taku don ganin wainar da za a toya

*Written*
*By*
*Queen meemi*
*Queenmeemi.WordPress.com*

.
[9:18am, 02/11/2016] meemi basheer: *ZEENATU by Queen meemi page29*

♠. ♠. ♠
♠. ♠. ♠
♠. ♠.
*® NWA*
*Dedicated to Lubie nd bena*

*15,Oct 2016*

*Queenmeemi.WordPress.com*
*Like Queen meemi group of novel @ facebook*

Jin arar bu e k'ofa yasa Zee ta mi e da magagin bacci toilet taje ta wanko fuskar ta ,zuwa tai ta bu e ganin Mata tai rututu suna shigowa Sun kai su goma sai Masha Allah suke cewa sannu da zuwa tai musu duk suka zauna kan kujera suna kalle -kalle .
Zee tazo ta tsugunna ta gaidasu wata tsohuwa tace "yarinya ni nan k'nawar kakar haidar ce, wan nan k'anwata ce haka dai taita lussafosu Zee kam murmushi kawai take.
pure water na leda ta kawo musu da lemo , ta zauna suna ta a hira wata ta tab'e baki.
"ruwan leda" wata tace Dariya suka sa zeena jikin ta yayi sanyi ta Shiga kitchen tana kiciniyar D'ora girki wata k'arama acikin su ta Shiga kitchen in sai kalle- kalle take "karfa ki b'ata lokacin ki tafiya zami"
Aki ta Shiga, wata daga cikin matan ta kalli aya "ai naso ace hajara ce ta shigo daular nan ai da bare gwanda an gida" .
d'ayar tace" ai da sake kede barni kawai".
Haka Zee ta akko musu turare da su mai da kudin mota, bayan fitar su ta koma aki ta kwanta .
Wajen Karfe 3 haule ta Shiga side en zeena , tana gyara flask en abinci a dining .
"Anty Zee wai kizo inji mami".
"haule kice gani nan zuwa". haka ta tashi ta akko hijab inta ta Shiga.
mami na zaune kan 2 seater tana waya sai data kare then ta juyo gun Zee tace "ke zeena dama baki da tarbiyya? ace 'yan uwan mijinki su zo Amma ki ka sai musu tarbar arziki ,sai ruwan leda , ina swan water da mijinki ya aje? ko sai 'yan uwanki sunzo zaki basu ehe"?
Zee da zuciyar ta ta gama b'aci ta ago.
"hajiya haka suka ce mik"i? Wallahi lemu da ruwa na kawo musu lokacin ban ora girki ba fa na tashi zan ora sai wata ta cemun wai kar na ora yanzu zasu tafi, da zasu tafi har su sabulai da mai na basu Allah ya gani nayi musu tarbar arzik'i".

wani ban zan kallo mami "Tayi tiryan-tiryan kin sako magana to wallahi ban lamunta ba kin gane inde kina son zama lafiya dani to ki girmama an uwana". Zee ta ce" Allah ya baki hakuri".

*******
tashi ki oran faten doya asalub'e Zee ta mik'e tana tunani wata aya da aure har an fara takurawa an aramin tsaki Tayi haka taje ta hau girki sai wajen 3 ta gama san nan ta aje a dining ta tafi side enta.
Sanin haidar sai 5 zai shigo yasa ta kuma ora wani girkin.
Tana zaune taci wanka tai kwalliya suna waya da mum haidar ya shigo da gudu taje ta rungumeshi "oyoyo swrht I miss u".
peck ya bata a wuya "me too my choco".
Aki ta kaishi ta tayashi ya rage Kayan sa yaje yayi wanka ,k'ananan kaya ya saka dining ya fito ya zauna cin abinci inda yake ta santi suna dariya ,dai-dai lokacin wayar sa tai K'ara mami ce akan layi ahankali ya auka "kazo ina son ganin ka".
"to mami"
Hira suka cigaba dayi wajen Rabin awa sai Ga haule ta shigo " wai hajiya na kira "
Jikin Zee ya bata akwai wani Abu ta basar tashi yayi ya fita.
Da sallama ya Shiga hajiya ta kaimai harara " zama yayi.
"Hajiya gani".wato haidar matarka tafi arfin ka ko sai yanzu ma ta baka izinin tawo wa kirana ko"?.
"Mami ba haka bane".
"yanzu ace 'yan uwana suzo tai musu wulak'anci sai wani ruwan leda haba adinga Sara Ana duban bakin tulu mana,ya kamata kai Mata fa a amatsayin ta na matar ka ".
Kan haidar dake sunkuye Shi a fa in zaman sa da Zee bai ta a ganin ta da bad hali ba .
"kayi Shiru baka ce komi ba".
"mami zan Mata".
"yawwa har fad'a nai Mata Amma take neman tai min.rashin kunya" ,ransa ne ya baci .
Ya tashi ya futa ransa a had'e ya Shiga binsa da kallo Zee Tayi .
"lafiya habiby naga ranka aba'ce abinda ban ta a gani ba"?
"Yanzu Zee abinda ki kaiwa su kaka kin kyauta kenan karki manta an uwana ne ace ruwa Shi zaki basu ,san dan mami tai miki fa a Kiyi Mata rashin kunya"?
"To wallahi ki sani duk sonda nake miki akan mami zamu iya batawa".
Idonta ne ya ciko da hawaye ta taso ahankali ta kwanta kan cinyar Shi ta kwantar da kanta kan kafa arshi ta Shiga raira kuka.
Bai hanata ba Amma kukan na Shiga ransa ,ta ago tace "habiby har Ababa ni bazan wula anta 'yan uwanka ba, sunzo na kawo musu ruwan leda ganin swan ba sanyi na hado musu da drink ina zaune suka sha muna hira na tashi zan dafo abinci suka ce na barshi sauri suke, taja numfashi.
mami ta Kirawoni bayan tafiyar su tana mun fa a ban musu tarba mai kyau ba".
Allah ya huci zuciyarka Allah shine masanin gaskiya .
"bai ce Komi ba ya tashi ya Shiga beadroom nasa ".
Binsa tai da kallo itama ta tashi tana kuka ta shige aki tai flat akan bed tana kuka.

Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta Shiga kitchen ta hau clean en sa ta fito ta zauna ta kunna tv tana kallo Sam ba kallon take ba , bata son bacin ran haidar ,a hankali ta doshi a kinsa har ta bu e sai kuma ta koma da baya ta Shiga nata...

*_Writting_*
*_Queen meemi_*.

.
[9:18am, 02/11/2016] meemi basheer: . *ZEENATU by Queen meemi page 28*

♠. ♠ ♠
♠. ♠. ♠
♠. ♠.
*®NWA*
*Dedicated to Lubie & bena*
Chapter 15 · 0% Book details