← Book details Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 35

Sashe 21

Zeenatu Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba yanda mum zatai in Banda zuciyar ta dake k'una Kamar zee ace za aiwa kishiya har Yaushe akai auren,tabbas ni Bazan hana sunar annabi ba. domin Shi ya halarta,zan dage da addua Allah ya basu zaman lafya
Haka suka yini suna hirar nan cikin jimami mum ta bugawa Zee waya tai Mata nasiha ,mai ratsa jiki.

*Bayan kwana 7*

Yau kwanakin da mami ta d'aukar wa haidar ya cika yana zaune wayar sa tayi kara, mami ya gani ya d'auka kazo Ina son ganinka, gabansa ne ya fad'i akasalance ya tashi,Zee ma haka,Shiga yayi yaga mami da umma mahaifiyar hajar akan kushin Ga hajara a k'asa a gefe.

Zama yayi ya gaidasu mami ta kalle Shi "to haidar yau ne dama mukayi alk'awarin ayanzu inason ji daga gareka ,Kafin nan bari muji ta bakin k'anwarka"

Mami tace" hajar kina son haidar zaki aure Shi"?
Sunkwai da kaai tayi na gulma "eh mami na amince".

Murumshi tayi ta juyo Ga haidar to "Ina jinka ka amince ne"?.
nan ya gyara zama" mami don Allah ki hakura da auren nan ".
Kalas ta ce tare da d'aga hannu insha "Wallahi Wallahi nan da wata d'aya za a daura aure".

"Inde kana son gani da kyau to ka bini na riga na gama magana".

Tashi yayi kawai a kasalnce ya Shiga mota ya figa tafiya yake kawai saida yayi nisa ya tsaya hawaye na tsiyaya.
Zeey kam ganin har dare bai dawo ba yasa ta Shiga damuwa sai 10 ya Shiga da gudu ta tareshi "habiby na Amince kayiwa mami biyayya banso ka Shiga fushin Allah" .
Rungumeta yayi "Allah yayi miki Albarka ,zanyiwa mami biyayya Amma Alal hakika bana son hajara da aure ,banso yi miki wata tazo matsayin kishiyar ki ba"

"Kaddara ce habiby in Allah y hukunta ba yanda zami taimakon sa tayi yayi wanka yaci abinci suka je sleep.

*bayan kwana 2*

Kowa da irin tasa k'addarar tabbas baka isa ka ketare ba ,mutuwar Aure K'addara ne ,domin Aure rai gareshi duk lokacin da kaga ya mutu to dama Allah ya
tsara hakan.

Afusace hajar ta Shiga side d'in zina da misalin K'arfe hud'u na yamma , ball tayi da jakar Zee dake kan kujearar ta haye tana girgiza Zee kawai bin ta da kallo take haka ta canja tasha ,Zee ta dauka ta canja .
Ganin hakan hajar tace ke dallah yanda kike tak'amar gidanki nima haka don nan da wata d'aya kin zama bora.

Kitchen ta Shiga ta d'akko lemu ta tsiyaya acup ta tasha ta d'aga Shi ta rotsa agun ,zuciya ce ta d'ebi Zee ta wanke hajar da Mari so biyu.

Nan itama ta rama cakumar juna sukayi ko wacce najin kishi Kamar ta murkushe daya😂sai naushe naushe suka ,Zee ta samu sa a ta danna hajar tana duka duk da hajar ta fita jiki.

Da gudu mami ta shigo lokacin Zee ta fasawa hajar hanci mami "tace tabd'i yau wallahi ko kinfi mayya naci sai kin bar gidan nan.

Zee da idonta ya rufe "tace mami ki duba irin abinda ta ke mun yau ta kaini bango" .

"Eh to ke kuma yau zaki koma gidan iyayenki dama kin rikitamun yaro" kuka Zee keyi ,ta tsugunna tana bawa mami hakuri.

Haidar ne ya shigo ko zama bai yiiba mami "tace kazo ka sallami yarinyar nan don. Wallahi yau se ta bar gidan nan"

Bai gane me ya faru ba Haka ya tambaye su ko wacce ta fad'a mai ,.
nan ya b'allawa hajar Mari "ban hanakii shigowa ba".mami tace" lalle haidar bansan an shanyeka ba sai yau, to wallahi ka zab'a komi ko Zee".

"Mami don Allah ki hak'uri karki Kashen aure" .
"Idan ma na kashe wani zan ma" kuka yake yayin da Zee ma keyi.

"Idan nice ma haifeka ka saki yarinyar nan in ba haka ba wallahi senayi maka baki ka b'alb'alce.

Zee ta d'ago ta kalle Shi habiby kabi maganr mahaifyar ka don ka ga dai dai .

"Zee Ina son ki, Bazan iya rayuwa without you ba" kuka tasa.

"Mami tace inajiranka,".
Kallon Zee yayi" Kije gida zan zo , ba haka nake so ba ,so nake inji kwalemar saki" .
kuka ta saka "yau haidar ka nunan iya kata".
takarda ya d'auko ya rubuta saki d'aya hannun sa ke rawa .

"Bani ta kardar" mik'a Mata yayi ta karb'a ta karanta tareda murmushi.

Gud'a hajar tayi .tayi wa Zee gwalo.
nan mami ta mik'awa Zee takar darr sauka fice .
haidar ya tsaya "Zee ki gafarceni har abada Ina sonki ba ason rai na bane Kinga de duk agabanki abin nan ya faru,din Allah karki tsaneni wallahi Zee har bada INA TARE DAKE."

ba tace komi ba ta kalle Shi haidar "I will never forget u in my life & I will miss u everyscan.

D'aki ta Shiga ta sawo hijab zumbulele tafito tana hawaye direct fita tayi haidar ya bita ko wai waye bata ,yi haka ta fita daga ai nihin gidan,haidar Kamar jela sai binta yake ,jefa k'afar ta kawai take ,wani adaidaita sahu ne yazo wucewa ,tsayar da Shi tayi ta shiga ya ja ,nan ta tusa hijab d'in bakin ta tana kuka ,shikwa haidar ganin adaidaita sahun yaja kawai ya zube kan gwiwoyin sa yana kuka tamkar k'aramin yaro.......

*

*Story & written*
*Queen meemi*

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . *ZEENATU by Queen meemi page40-43*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠. ♠. ♠

*Oct 10,2016*

*Queenmeemi.WordPress.com*

Da sauri ta Shiga gida mum na yiwa faty tsifa gunjin kukan tane yasa ta dago,ta kalle ta ta dafe kirji !ganin yanda take gurshek'en kuka.
"Ke meye"?.
mum ta am bata tare da mik'ewa tsaye faty ta mik'e mum ta tashi ta kamota ta zaunar kanta ta D'ora kan cinyar mum tana kuka da shesh-sheka sai da tai mai isarta ,mum da tai tagumi tace "idan kin gama kukan sai ki gayan dalili".

Matse Ido tayi "mami ta saka haidar ya sake ni," dafe kirji mami tayi,"lahaula Waka k'uwata illabillahi
Yanzu zeena akan K'arin auren da zaiyi sai da kika tashi hankalinki ya sako ki",dafe goshi tayi inda hawaye ke zirara afuskarta.

"Mum wallahi ban tashi hankalina ba", nan dai ta kwashe duk irin zaman da sukai tare ta gaya Mata ,numfashi taja "mutuwar aure ba Dad'i ballantana irin naki da k'ar-k'ari watanki shida (sis month) Amma har ya mutu, yi hakuri zeena da sanin Allah kinji duk abinda ya faru Kaddara ne,Ita kuma uwar mijin naki da tai silar komi Ai Allah baya bacci,duk abinda mutum ya shuka Shi zai girba".
Zazzabi ne ya rufe zee magani mum ta bata tasha ta D'an kwanta take bacci ya kwasheta,da wasu rikitartun mafarkai

**************

Da k'yar haidar ya koma gida ko kallon inda kofar gidan yake baiba, motar sa kawai ya Shiga a Afusace ya fice .
gidan su kb ya zarce sai kuma wata zuciyar ta canja mai ra'ayi kwana yayi ya canja hanya tatarar gudu kawai yake tafiya mai nisa yayi bai tsaya ko Ina ba sai gidan gonar mahaifin sa daya ci gado.
Bayan ya Shiga ya fito ya tsaya ya tak'urawa korayen shuke-shuken dake gurin Ido ,ya Dad'e a haka San nan ya bud'e mota ya d'auko robar paro d'aya ya kunce ta kwara akan sa yarda Ita yayi yad'an daki kansa.
" mami ya kike so nayi Ina sonta banso auren na ya mutu ba ,mami bana son hajar ,iluv u zee ta" Kamar mashayi haka yai ta sumbatu
Shiga can ciki yayi ya d'au darduma ya kwanta a kai ya k'urawa sama kallo ,Sam bai damu da duhun daya k'arato ba.
Tashi yayi ya Shiga wani k'aramin gida dake cikin gidan gonar already yana da key ya bud'e ya Shiga yai zaman sa zuciyar sa na tuk'uk'i da zafi , wayar sa ya d'auka ya kira number din zee switchoff yaji ,wulli yayi da wayar,Kamar ya kurma ihu idan ya tuno Sun rabu da Zee din sa.....

Ran dandy idan yayi dubu ya tashi lokacin da mum ke gaya mai mutuwar auren zee takadar da Zee ta bata ta bashi .
"Ina zeena din"?
"bacci take zazzabi ne ma yarufeta na bata magani ta sha".
"Amma abin nan da mamaki aure 6month a sako mini yarinya ni ban tab'a sani akwai matsala acikin zaman su ba ganin bata tab'a kawo k'ara ba".

Mum tace "ay tayi kyan kai daba tazo ta gaya mana ba da tuni ran mu ya baci kuma abin yazo yafi haka".
Dady yace ba hujja nace data fad'a ai da ko tayaya an samar Mata mafita, Amma ba komi komi muk'addari kuma
duk abinda mutum yayi Shi za ai mai ,wallahi ba zan nemi yaron nan ba sayyazo da kan sa ,yarinya k'arama an mai data bazawara"

Mum data gara zama tace "Sai hakuri K'addara ta riga fata".
"Yanzu ya kamata ta tashi Ita zeena saboda dare yayi" dai -dai lokacin ta fito nan suka bita da Ido gaida dady tayi .
"Ga alama nan duk ta rame koda na San zeena nada fad'a da rashin hak'uri tabbas nasan wan nan Ita aka k'wara bawai don bin baya ba".mum Ita de hak'uri take ta bawa dad ganin yanda ya harzuk'a.

Haka su sadeey da sadiq sukai ta jimami nan ma sadeey ta ware baki ta fad'i duk irin abinda akewa zee lokacin data je
Dad yace" 'yata bazata koma ba kuwa ,koda sunzo biko domin Ina sonta"
A ranar kowa na jimami duk basiyi baccin kirki ba zee sai juye-juye take saboda Sam ta kasa jin dad'in baccin saboda yanda ta Saba jinta jikin haidar duk setaji wani iri.
Kuka ne ya kubce mata kewar haidar ke nuk'ur-k'usar ta da soyayyar sa ga wani kishi da ke cinta ,gefe kuma haushi yake bata duk da tasan ba shida laifi......

*Godin gareku masoyana aduk inda kuke nima Ina k'aunar ku ,Allah ya barmu tare .luv u oll*

*Story & Writting*
*Queen meemi*

.

.
[10:13pm, 01/11/2016] ‪+234 814 783 0740‬: . . . . . . *ZEENATU by Queen meemi page44*

♠. ♠. ♠ ♠. ♠. ♠. ♠.
*®NWA*

*Queenmeemi.WordPress.com*
Chapter 21 · 0% Book details