Sashe 7
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
a rayuwar sa. Ta fiddo wayar tare da tambayar sa password da matric number. Portal din na budewa ta Mika mishi wayar kaga inda zaka Danna..... Ya danyi dariya to bude Mana ai ba komai don kin gani. Ta kalleshi tana mamaki saboda tasan Portal sirrin dalibi ne ba kowa kake yarda ka nuna mawa ba. Ya Kara Yar dariya ki bude ba komi. Ki gane mun Ina da carry over? Ta ce to a sanyaye tana mamakin irin warda da yayi mata farat daya zuciyar ta cike da Jin dadi tare da ganin kimar say da mutunci. Kaiiii....ta fada tare da zaro ido ka Fadi accounting. Sai kawai yayi murmushi nasan za'a rina sai wane? Ka Fadi GST English Shikenan. Nawa ne point dina? Ta duba can kasa tana warware ido..... Okay gashi Nan 2.65. Ta kalleshi, amma Suleiman me yasa ka yarda dani haka?......Au kin San sunana kenan? Ya fada Yana kallonta cike da mamaki, tayi murmushi eh Mana nasan sunan ka Suleiman. Ina fatan ke dai lafiya lau ko? Sai kawai ta budo mishi portal din ta tace kaga nawa. Ya zaro ido kaiiiiiii...... Ta danyi murmushi Amma bana son Dan Allah ka fadawa kowa result dina. Ya Jin jina Kai in shaa Allah Zaki sameni Mai rike sirrin ki, amma Bilkisu kinyi wuta da yawa fa! Ta yi Yar dariya kawai. Allah yasa albarka. Kiban no. Ki dan Allah ko da wani Abu Yana tasowa Kuma idan bazaki damu ba Zan ringa matsowa kina tasar Dani inda ban ganewa. Ba matsala ga number rubuta........ A harzuke Anwar yabar class din tunda ga ranar sai kawai yayi baya da ita ko gaisuwa baya son suyi cikin kankanin lokaci ta Saba da Suleiman ta fahimci Yana da saukin Kai bashi da girman Kai sannan Yana da addini tare da daratta mutane. Ko da ya gane Bilkisu nada kokari sai ya like mata ko C.A zasuyi Yana manne kusa da ita baya yarda tayi mishi nisa. Ko kadan Bata da mugunta duk amsar da ta kakare mishi zata bashi ya kwashe tsaf!. Akwai wani course Mai matukar wahala gashi three credit unit ne Kuma calculation Mai rikitarwa kowa Yana Jin course din. Anwar yayi burus da ita Yana Jin kowa na kokawa Amma ya ki nuna ya iya. Kwana takeyi karatu da salloli, Ranar jarabawar course din ana ta jera layi kawai malamin yace ta zauna can, hankalin ta ya tashi ganin ya cillata gaba don yau baya take son Zama saboda ta Sami taimakon wani. Tana Zama sai taga Anwar ne a gaban ta, ita dai kawai sai addu'a takeyi tasan yau sai Allah da malaman gari. Tambayoyi bakwai be a amsa biyar tambaya ta farko dole ce gata da 'ya'ya har goma. Saura kadan ta kurma ihu saboda duka tambayoyin guda daya ne kawai ta sani itama theory ne ba calculation ba. Idanun ta suka kawo ruwa, taga tunda Anwar ya duke bai dago ba, hall din yayi tsit! Ta yi zugummm, zuwa can kawai ta Fara amsa wacce ta sani. Mafi yawancin malaman dake tsaron nasu duk sun maida hankali wurin Yan baya. Haka ta dunga rubutu Dan Allah yasa ta Sami Koda *E* ne a course din ta wuce wurin. Tana gamawa tayi zugummm kawai tana fargaba. Yadan waigo kadan ganin malaman basa kusa yace kin iya question one naga tana da wahala fa. Tayi kasa da murya wallahi question 4 kadai na iya cikin bakwai din nan ga Shi ta farkon naga 30marks ne. Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa. Habaaaaa.....ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart. Duba daya sai ta kwaso layi biyu. Cikin sauri ta gama shafin tace juya....Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi shirme. Wallahi na gama ka juya kawai. Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba. Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi. Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi. Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido. Kije kiyi submitting...ya fada kasa kasa ta ce toh. Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa. Suleiman kawai take jira ya fito sai kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu..... Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran. Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question one? Eh Mana. Wai da gaske kike? Wallahi kuwa. To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar *Gate* Yana ta faman sauri. Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu. Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya. Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku. Na gode na gode Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka? Naga yanda ake ta kuka dashi Kai komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ). Murmushi kawai yayi yace ba damuwa. Ya wuce kawai. Ta bishi da ido. Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode kaji? Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa. Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan semester din. Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry over daya. Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first class da over all. Bata halarci wurin ba. Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba. Hakan yasa Anwar zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama. Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin su ko wani Wanda ya sanshi. Ashe Suleiman yana wurin. Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu................. ************* *KADUNA RIGASA* Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba. Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar kullum ta shigo tana ta faman Bata rai . Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad ( Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi Yana ci. Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam. Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal.... Kamar Yaya?, Ya bukata. Kamar yanda kaji. Kamar yanda naji? Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa duka wurin ta.....me ke faruwa ne ummi? Tayi shiru! Dake nake magana...me ya faru? Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa Aunty Amira ta koma....... Ke ya daka mata tsawa. Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini? Gabanta ya fadi tayi tsuru tsuru, kinji? Munyi dake Ina Miki gini? Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa? Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba. Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra'ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to wallahi zakiji ba dadi. Mtsew ya buga tsaki ya wuce.......ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba. Kwallah suka zubo Mata. Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta .....salati ta kamayi ubanwa ya aike ki? Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi. Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe. Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba. Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai. Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi'a ba Dan komai ba kada ma akirkiri partyn Amira taji ba dadi. Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota. Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa. Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi sanarwa. Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai............ Ko ajikin sa. Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna. Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba. Nan suka Kara hure Mata kunnen wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci. Kuka takeyi wuiwui. Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi. Ana gama sallar isha'i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba.......