← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 68

Sashe 25

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ayi hakuri da kadan🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣1⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

****************
*KADUNA RIGASA*

Ranta a bace amma Sam hankalinsa baya kanta sauri sauri yakeyi daman tun da ya iso an shigo Mata da tsarabun da yayo.
Gabanta ya fadi, wannan rawar kafar ta mecece?
Ta daure ta dan boye fushin ta, kafin tace : Wai lafiyar ka kuwa?
Yau ka dawo sai Yanzu ka shigo nan Kuma kana ta wani sauri sauri........ Nan da Nan guiltiness ya kamashi, ya Fara Yan kame kame..... Nan da nan ta gano bakin zaren tayi murmushi ko hada gajiya halan?..... Ya kakaro murmushi gajiyar ma ce gaskiya.
Gaskiya ne.
Ta Mike , mu kwana lafiya kaje ka huta......wuf Shima ya Mike Daman jira yakeyi yayi waje Yana fadin Allah ya tashe mu lafiya.
Ta bishi da ido kawai, lallai namiji akala ne, ta kuta zaka gane kirenka ka gama kwanakin ka dawo...amma zanje in ga kalar wainar da ake toyawa.
Ummi nada tsawo Kuma doguwa ce tafi Amira .
Ita kuwa Amira irin Dan jikin Nan gareta Mai kyau da tsari, kallo daya Kai kace ummi keda Yara biyu ba ita ba.
Tana gyara jikin ta don ko tsakanin Ahmad da almustapha shekara biyar ne.
Ta bashi kamar mintuna arba'in kafin ta saka bakar jallabiya matsattsa tabi jikinta da turaren da ya fi so ta nufi sashen sa don ta San Yanzu suna can.
Ta danna karaurawa, ummin ce ta zo ta Dan leka.....ta kalleshi tare da yin Yar dariya *Yaya Amira* ce.
Oya bude ya fada Yana kishingide Yana Shan kankana.
Ummi na sanye da dogon wando jeans ya matse ta da Yar matsattsar Riga kanta ba kallabi ta yi kitso shuku Wanda ta daure da katon ribom saboda karancin gashi .
Ta kalli ummin sama da kasa sannan ta danyi murmushi sorry for disturbance please.....laaa ba komi karaso ciki.
Ya tashi zaune Yana Yar dariya Amira Yaya?
Tayi Yar dariya.....zuwa nayi in ji ka siyo mun book din nan kuwa dazun na mance in tambayeka......ohhh yes, Yana mota Bari na dauko Miki........ya yunkura..
A'a barshi kawo key din na dauko Yana ta wajen Ina?
Wurin Mai tuki jikin kofa Yana Nan....Ummi dauko key din.
Ta Mike.
Ya Kura Mata ido, Yana son tayi shigar doguwar Riga, wannan kamshin zuwa akayi ayi mun kwalele?
Good and fine, ta ce cikin zuciya, sannan tayi murmushi ta ce hmm kawai.
Kinji?
Gobe zanje kasuwa Dan Allah da safe ba dadewa zanyi ba, Zan biya gidan Salma.....me akeyi gidan salmar?
Ta dan mishi warrrr da ido, zumunci......duk sai ya diririce, Ni Zan kaiki ko?
Ta Dan Kara farrr da ido tare da Yar dariya, lokacin da Zan fita bana tunanin ka tashi cos by 8 nake son zuwa kasuwa Kuma Kai ba ma'abocin son zuwa kasuwa bane.....Zan biki please.
Saura kadan ta tuntsure da dariya yanayin yanda yayi maganar. Ta danyi murmushi.....Ummi ce ta fito da key.
Ta mike Bari na dauko book na.
Ya bita da ido Ummi ta dankara mishi harara Amma Sam bai lura ba.
Bude tabar kofar tana dawowa Bata shigo ba ta tsaya bakin kofa....ga key din Ummi, ....wuf ya Mike Bari na karbo.
Tana daga waje ya hada da key din da hannun ya rike in fito goben muje?
Nooo, kaga Ummi zata ji haushi kayi hakuri ka bata full time dinta don nima turn Dina.....ya murza hannun da karfi.
Tayi Yar Kara, ya dawo Yana dariya...... Ummi kamar zata fashe amma ta daure ta cije duk da haka sai da ya danga chanji amma sai kawai ya share.
Butique ta tafi, ta siyo rantsattsun English wear sabbi hada three quarters wando da skirt da crazy jeans.
Har ta dawo wajen Sha daya bai fito ba.
Ta fada wanka Yara sun tafi islamiya tahfeez, ta kulle kofar ciki tabar Mai aikin ta kitchen tana fita ta kofar baya.
Amira nada gashi sosai, kanta kananan kalaba ne duk sun zuba bisa bayanta wani sky blue crazy ta saka da wata crazy riga Mai hannu daya nononta kawai rigar ta rufe kasan ta Kuma bazace, ta cikin Bazar kana hango cibinta.
Kamshi kawai ke tashi gidan.
Sha biyu saura ya fito, motar ta kawai ya gani yasan ta dawo.
Ya nufi bangaren nata don agaisa.
Tana Jin motsin sa ta ruga daki ta dawo rike da littafi kamar me karatu ita a dole bataji shigowar sa ba.
Mutuwar tsaye yayi ya kusa sarkewa da miyau sai kawai taji Yana tari.....ta dago Kai da sauri irin ta razana din nan.......

*****************
*Federal University dutsinma*
Chapter 25 · 0% Book details