Sashe 17
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read
*****************
*KADUNA RIGASA*
```Wuya makarantar kare``` sunan wani littafin ```ZeeDee```
Ummi ta bala'in shiga hankalinta.
Ranar yabar gidanta, tun la'asar ya mata sallama kagare yake magariba tayi don Yana son Zama da Amira itama.
Gidan ya dauki kamshi tana ta soye soye da gashe/gashe,
Sai dai taga mutum bayan ta. Zabura tayi cikin tsoro.
Ta turbune fuska wallahi ka bani tsoro.
Ai gara haka, Ni jiya ba korata kikayi ba na kwana masallaci......Kai kajiyo. Ta katseshi.
Eh nasan cewa kishi ne yasa kikayi mun haka ....Ni na jiyo tunda na Kara Aure ko?........
Bana son irin wadannan maganganun ya kamata zuwa yanzu ka fahimceni.......naji...naji, shikenan.
Yanzu dai kawon abinda ya samu yunwa nake ji ....ya juya zuwa falo.
Dambun naman kaji, meat pie, doughnuts, da lemun kwakwa ta Fara kawo mishi. Yana Gama ci ya tafi isha'i, lokacin da ya dawo ya tarar da farfesun hanta, hunhu, Koda da tunbi.
Yana son sa sosai, saboda yanayin yanda takeyin sa:
*Farfesun hanta,hunhu,Koda da tumbi*
Bayan ta wanke su da kyau ta zuba a tukunya sai ta kawo albasa Mai yawa (musamman Mai lawashi), tafarnuwa,da citta sannan ta Dan zuba Maggi onga na sachet ( gari ) Shi kadai. Bata zuba ruwa sai ta dora Kan wuta low Yana heating a hankali kamshin kayan zai dakesu sosai ya danyi dry sannan sai ta zuba jajjagen tarugu da albasa again ta tsaida ruwa ta rufe.
Lokacin da ya dauko dahuwa ne ta zuba sauran Maggi da Dan gishiri to taste tare da curry kadan. Idan ya hade sai maganar ci.
Tana zaune gefen sa, suna ci tare, Ahmad ne ya shigo da gudu anyo mishi wanka,
Kai lafiya?
Abba gobe Aunty tace kowa yaci gayu zamuyi class picture.....
Shine zaka fado haka ba sallama daga Kai sai boxers? Ta fada tare da balla mishi harara....sim sim sim ya juya zai koma.
Ya kalleshi naji Ahmad in shaa Allah gobe gayu zakuci je hassu ta baku abinci kaji ko?
Yace toh ya juya.
Kin cika zafi yaran nan yanda suke tsoron ki koni basa tsoro haka meye abin fada ga shekaru irin nasa ma abinda yafi haka yi zaiyi.
Hmmm, kawai tace.
Ya finciko ta......zo in koya Miki yanda ake ba miji amsa idan yayi magana ba hmmm ake cewa ba.........dai dai ita Kuma ta turo kofa ashe bude yabarta lokacin da ya shigo.
Yana kokarin Kai bakinsa ga nata sukaji an turo kofa itace tayi saurin zamewa tunanin ta ma ko Yan aiki ne.
Tuni idanun ta sun gane Mata.....me ya kawo ni?
Wace kaddara ta aikeni?
Na gano ma kaina Ni Ummi........gabanta ya dinga halbawa da karfi da karfi.
Ita Bata karaso ba, Bata Kuma juya ta koma ba.
Gashi ya rike Amirar gammmm yaki saki, sai kichiniya takeyi amma ya riketa tamau . Dole ta hakura ta kalleta, ki karaso daga ciki Mana Kika yi tsaye bakin kofa.
Bai dago Kai ba Yana ta wasa da hannun Amirar yace idan wani abu kike bukata me zai hana ki Kira waya?
Shiru dai tayi har ta zauna bisa kujera tana facing dinsu amma ta kasa Kara maida idanu ta kalli takaici.
Tayi shiruuuuuuuuu, sai Kuma kwallah sharrrr, duk motsin da takeyi idon Amira na kanta saboda tana ta mamakin zuwan nata.
Ganin zubowar kwallah yasa ta zunguro shi,
Ya maida Kai gefe Ummi lafiya dai ko?
Ita kanta tasan kukan da biyu takeyin sa, kasa ta sauko ta Fara magana a hankali,
Aunty Amira kiyi hakuri Dan Allah Akan abubuwan da suka faru sharrin shaidan ne, in shaa Allah hakan bazai Kuma faruwa ba......Ayya Ummi ba komai ya wuce.
Ta fizge hannun ta bari in zubo Miki abinci......um um na gode ta mike.
Ina zakije toh? Ki zauna muyi fira.......ya Kara hade fuska ya tsuke.
Ta Dan tabe baki , a'a barci nakeji da wuri sai ko zuwa gobe haka.
Har kofa ta taraka, kafin taja kofar.
......... Gaskiya abinda kakeyi ko kayi Abban Ahmad wallahi baka kyauta ba, Shi ido ba mudu ba yasan kima.
Ka rikeni gaban Ummi ai wannan cin fuska ne.
Ya kalleta sosai.......makaho idan Yana Kashi in har ba'a zungureshi ba to bazai gane ana kallonsa ba.
Yarinyar can abinda take nuna mun tun kafin in aureta dole in bita in Mata yanda takeso ita bazata bi ra'ayi na ba.
To Ni da ita wake auren wani?......duk da haka Yanzu kaga.....kiranta mukayi?.
Inba kilibibi da tsugudidi ba me ya kawota Yanzu?
Ba a haka......ke naji.
Tayi murmushi.... Ita Amarya ai Bata laifi.
To wannan dai tanayi.
Naji dadin zuwan ta yau din wata kilan ta Dan Sami darasin kula da miji idan ita din Mai hankali ce.
Ya Mike idan kin Gama sallamar Yara Ina jiranki.
*Ummi* taci kuka kamar ranta zai fita, tabbas ya kamata tayiwa kanta karatun ta natsu. Ashe ita sunan tana Aure Amma har Yanzu Bata San meye Jin dadin Aure ba, ta goge hawayen da ke shatatowa, dole in kwantar da kaina inci arziki in barshi inda yake saboda tabbas idan naki abinda yake so nice Masha wuya.............