← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 68

Sashe 68

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 2 min read

Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Muna rokon Allah ya karemu daga cututtukan zamani.
Abinda muka karanta Allah yasa mu amfana da lesson din ciki na Shi mutunci Riga ne, ya kamata mu sani kunya na daya daga cikin abinda ke daga darajar mace a duk inda take.
Kwadayi baya Kai mutum ko Ina sai tushen wulakanci da Kuma nadama.
Mai kudi da talaka duk bayin Allah ne, masu kuci da ke nuna Basu iya rayuwa tare da talakawa ku sani rayuwar dasu bazai rage ku da komai ba sai dai na ku Kara samun daukaka, mutuncin ku zai karu, zaku Sami lada a wurin Allah. Akwai fa'idoji da dama masu amfani akan Haka. ..... Abinda na hakake a labari shine Jan labari ba shine ba, matukar sakon da kake son isarwa zai je to a layi biyu ma ya wadatar...... Kadan Mai albarka yafi Mai yawa yuyuyu.
Rubuta batsa, maganganun banza da rashin kunya ga labari ba shine ke kawo wa mutane kwarjini ga labari ba. Ma'anar labarin , tsabtar sa da Kuma kyautata rubutu saboda Allah. Duk abinda muka rubuta zamuyi depending din sa a wurin Allah. Ya Allah kada ka kamamu da laifin da mukayi bisa ga tunanin munyi da kyakkyawar niyya. Allah ka yafe Mana ka shirya Mana zuri'a.
Qalubale ga itaye, ku daina tura yaran ku makaranta ba tare da binciken abinda sukeyi ba, ku ringa Kai masu ziyarar bazata Kuna saka ido ga yaranku musamman mata, mazan ma abin kula ne Yanzu.
Yan Mata ku sani bin namiji ka nuna kana sonshi bance haramun bane Amma ku sani kunya ma cikon Imani ce, duk abinda musulunci yazo dashi muna daukarshi da muhimmanci .
Allah ya sada mu da alkhairi.
Wanda labarin bai mawa ba sai yayi hakuri.
Sai mun hadu a wani sabon labarin bayan sallah idan Allah ya kaimu.

*Zainab wowo*💖
*MAMAN AL'AMYN, AMINATU AND ABDALLAH*a
Chapter 68 · 0% Book details