← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 68

Sashe 33

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

gaskiya..... Saura kadan ta dora hannu a ka. Ta ce hmm. Ko bazaki fidda mun ba? Ta daure ta cije ba tare da ta kalleshi ba tace cikin su wacece tafi birgeka? Yayi jimmm, ai ruwan ido bazai barni na tantance ba, wace kike ga tafi? Ta harareshi ban sani ba ta Mike Ina da aiki daki...... Ya gumtse dariya shima ya Mike. Suka jera kamar ta kwasa a guje tabarshi agun takeji....... Kin San rayuwata Ina son mace wacce Bata da tsoro, .....,..ai shikenan bani ciki kawai, ta fada cikin Rai saboda nikam kamar farar Kura nake don tsoro.........Mai kyau, Mai ilimin addini, wayayya, fara Mai dogon hanci, Mai tsawon gashi, Yar gayu.......shin Wai ni Yanzu Ina ruwana kake ta faman lissafo mun kaje can ka Nemo Mana.... Yayi Yar dariya ke nake fadawa irin wacce zaki nemo mun..... Mufeeda kaje na zabar maka mufeeda ita ce keda duk qualities din da ka zayyano...... Ya Kara gintse dariya mufeeda ba Fara bace Kuma Bata da gashi dogo attach........ Har ma ka sani? Ta zaro ido....... Eh, Mana kowa ma yasan haka tana boye gashin ta ne? Mtsew....sai kaje sadeeq ya Nemo maka...... Ke Zaki Nemo. Tayi murmushi ikon Allah dole ne? To ai kece babbar kawar tawa ko? Kema sai in taya ki zabe......Ni an mun miji..... Ya bazga uban tuntube saboda tashin hankali saura kadan ya Fadi tayi saurin tarewa kamar zata taba Shi tace subhanallahi sannu.... Ya Mike idanuwan say duk sun Fara chanzawa daga farare zuwa jajaye..... Da gaske an Miki miji? Ya fada Yana gyara takalmin sa, ta kakaro murmushi ta ce aikuwa dai Ina da Wanda Zan aura...... Bai Kara magana ba har suka je kofar gidan. Ya tsaya kansa juyawa kawai yakeyi, ta fito da Yar karamar leda ta Mika mishi ga tsarabar.....ya kasa Sanya hannu ya karba. Ta kura mishi ido ya sunkuyar da Kai kasa kawai. Lafiya dai ko?, Yayi shiru. Gabanta ya Fadi...... Anwar lafiya? Ta Kara fada a hankali . Ya dago Kai, kirjinta ya buga duk ya wani gigice yayi kicin kicin da rai, ya sunan Wanda Zaki aura? Ta kalleshi........ Wai shine abinda ya sanyaka damuwa...... Ya Mata wani kallo dole ta kawar da Kai saboda ta tsani kallon banza da rainin wayau....... Akan meye zai dameni? Tayi murmushi to naga ka chanza lokaci guda....... Kaina ne yake mun ciwo. Ga tsarabar.....ta Mika mishi ledar. Ya juya ajiye wurin ki Zan karba...... Wallahi bai yiwuwa. Ina ce shine dalilin biyo ni. Ya kalleta nace ki ajiye Kuma bana bukata....... Ta tari gaban sa da sauri Wai me ya faru? Bani wuri in wuce please. Wallahi baka tafiya sai ka fada mun me ya Bata maka Rai....... ( Cikin zuciya kuwa sai dadi takeji watau Anwar ita yake so yake ta gewaye gewaye. ) Ya kalleta sai ya koma jikin bango ya harde hannuwa ya sokar da Kai . Kai nake sauraro ta rike kugu.....ya yi shiru. Ta Fara magana cikin fada fada. Kace in nemo maka matar Aure na zabar maka ni Kuma bani da ikon da Zan ce Ina da Wanda nake so......... Ke ! Ya daka Mata tsawa.... Na ce kada kiso wani? Tayi baya da sauri, cikin razana. Ya matso kusa da ita, da kiso wani da ki tsaya haka bai Dame ni ba, I have nothing to do with that, and it doesn't make any difference to me....... ikon Allah ta fada. Kamar Yana jiranta? Cikin bacin Rai ta kalleshi, Ni ya dameni ne? Ko mufeeda Shi yasa da ta tare ni tamun rashin wayau na Bari sai a gabanka na Mata warning... saboda bana tsoron ka baka gaba na..... Damko kafadunta yayi da hannu biyu ya buga bayanta da bango....... Wallahi tallahi idan Kika Kara........kwallah suka zubo Mata sharrrr ta fashe ta runtse ido. Allah yaso duk ba a dawo sosai ba, kofar gidan ba kowa. Ya runtse ido da karfi ya saketa a hankali...... Ta yunkura zata ruga gida ya tare ta da hannu idan Baki so in Kara taba ki kada ki motsa...... Ta fashe da kuka.... Hankalin sa yayi kololuwar tashi...... Bai San ya Fadi *Na shiga uku ba* Bilkisu...... Tasa hannu ta toshe kunnuwanta.... Kiyi hakuri Dan Allah na gwadaki ne kawai. Ganin yadan matsa baya ta yunkura zata Kara guduwa ya kuwa kamota da karfi ....... Yaya Zan ta Miki magana Baki ganewa? Nace idan Baki so na Kara taba ki kada kice Zaki gudu ko daman kina son hakan ne? Ya fada cikin tsawa. Ta Kara rushewa da karfi....na tsane ka wallahi bana son ganin ka , ka kyaleni. Har cikin kasan zuciya yaji maganar. Ya daure yace ....naji kin tsaneni, kiyi hakuri nayi kuskure bazan Kara ba.....wasa nakeyi. Nima ai da wasa nakeyi ka Fara .......wasa kikeyi ba a Miki miji ba? Ta mishi banza...... Saura kadan ya Kara kamota don ya rungume ya saki wani murmushi: nasan wasa kikeyi Nima. Kawai Ina son ganin fushin ki ne don Shi kadai nayi missing cikin hutu.......kiyi hakuri I'm sorry ya rike kunnuwa. Kinji? Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan Kara ba.... Ta goge hawayen da kasan hijab dinta. Kawai tayi shiru kanta a kasa. Baki da wahalar yin kuka meye na kuka anan Bilkisu....kina da shagwaba ko?. Um? Baki magana? Yau ni Kuma tawa ta sameni an Kara yin fushi Dani...... Dan Allah kiyi hakuri kinji.
Chapter 33 · 0% Book details