← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 68

Sashe 24

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

ki, tunda ya Baki hakuri Nima na Baki sai ki......yaushe ya bani hakuri? Wallahi bai bani hakuri ba. Mutane nawa ya Aiko Miki? To ai mutane kace Shi in person baizo ba ta Yaya Zan San cewar ya gane kuskuren sa? ...... Yanzu idan yazo da kansa ya Baki hakuri Zaki hakura ku koma normal?...... Tayi shiruuuuu.... Me yasa Suleiman zai Sanya ta kwana. Kinji? Dan Allah Ina son Anwar yaci albarkaci na ki yi hakuri Kinga Yanzu idan ya dauke hannunsa ga kowa tabbas an Sami matsala Kuma kece sila...... Ni? Yayi murmushi, kiyi hakuri Bilkisu Yanzu dai, Dan Allah kiyi hakuri. Ya Gama daureta ta ko'ina, tafi mintuna hudu bata ce komai ba. Ya Kara kallon ta, Ni zakiyi ma wannan alfarmar ba kowa ba kiyi hakuri. Kwalla suka suka zuba Mata...... Ta mayar dasu da karfin tsiya sannan ta ce shikenan ya wuce...... Ya zaburo, kin hakura? Eh, amma ka sani saboda Kai...... Na sani wallahi. Na sani Bilkisu na gode na gode words cannot express my gratitude. Suka jero tare ya rakata har bakin gida sannan ya tafi. Hostel yayi ma tsinke, kamar daga sama suka ganshi karon farko da ya taba zuwa dakinsu. Anwar na kishingide Koda Suleiman man din ya shigo ya maida ido ya rufe kunnen sa like da ear piece, ba wani music da ya kunna duk Yana jinsu, Sadeeq ya fadada murmushi wannan babban bako ne sannu da zuwa Suleiman. Ya ce yawwa tare da Mika ma kowa hannu Banda Anwar. Ya kalli sadeeq muje in ganka...... Suka fita tare. Anas ya kaima Anwar duka Amma Kai Dan iska ne wallahi. Yaron nannya shigo don wulakanci shine ka rufe ido Dan ubanka..... Mtsew yaja tsoki kawai. Ya kalli sadeeq, na shawo Kan mutuniyar ku, ta hakura ta ce komai ya wuce sai ka fadawa Anwar din saboda kasan........ya riko hannunsa duka biyunKace wallahi...... Yayi murmushi wallahi kuwa. Amma Suleiman mun gode Allah yabar zumunci dama inata zullumi ranar juma'a za ayi econometrics gashi yayi burus da kowa.....Ya Mika mishi hannu suka Kara gaisawa sannan yace mun gode fa bari naje na mishi albishir .....ya koma daki da sauri. Kallo yayi ma sadeeq ya watsar. Ni kakeyi ma wannan Dan iskan kallon? To Suleiman zuwa yayi ya fada Mana ya shawo Kan Bilkisu tace ta hakura zaku koma normal.......zumbur ya Mike... Are you serious???? Ya galla mishi harara na ban sani ba kaga wulakancin da kayi mashi da yazo ko kallo......forger about that please ta hakura???? Anas yaja dogon tsoki sai kaje ka fada Mata ka kusa mutuwa..... Ya kyalkyace da dariya a'a ka manta mutuwar nayi. Eh Mana, Kuna ta wahalar da kanku a banza....... We are just friends jor what are you talking about??? Ai maganin sa Bilkisun, nifa yarinyar ta bala'in birgeni wallahi ta nuna mishi ita din ta daban ce......Anas ya fada Yana Kara doka mishi harara. Ya lumshe ido ya koma ta baya ya kwanta...ku yau kuka San Bilkisu ta dabance ko? Duk suka dunkule hannu suka Kai mishi duka ... sadeeq yace asirinka dai ya tonu munafuki.....ya Kara bushewa da dariya. Washegari suna da exam 3, karfe biyu ta fito library jikin wata bishiya bisa kujera ta Kira Suleiman...... Hello ka shigo? Eh, kina Ina ne? Ina ta wajen library wallahi na kasa game wannan last part din, zo kamun dalla dalla please..... Okay Ina zuwa. Ashe tun karfe tara suna tare da Anwar Yana koya musu a class, ya kalleshi cikin kosawa.......Yaya? Dariya yayi kafin yace, last part din nan ne bata gane ba take so na nuna......tashi muje ya Mike..... Anas ya kalleshi Dan uwarka mu Kuma fa ? Ya dalla mishi harara ku gane ...yayi waje. Daga nesa ta hangosu , tayi saurin boyewa bayan bishiya sannan ta saka wayar ta Airplane mode. Tana kallonsu sai safa da marwa sukeyi amma ta boye. Har kusan uku saura kwata sannan ta hangosu sunyi hanyar class din da zasuyi jarabawar......... Watan Suleiman kiranshi yayi ko? Ta buga tsoki. Lokacin da ta Isa har sun zauna invigilators sunzo, ta shiga...idon sa na kanta, Koda wasa Bata yarda ta kalli inda yake ba, Suleiman na bayansa ya Dan gyara alamar ta zauna sai kawai ta wuce kamar bata lura ba. Ana gama jarabawar, tayi saurin submitting tabar shiyyar. Suleiman na fitowa ya kamo hannun sa, kaga ta tafi ko? Murmushi kawai yayi. Abu kamar wasa har saura exam uku su gama amma Bata yarda sun hadu ba. Ya Sami Suleiman kamar zai mishi kuka yace shifa bai gane ba. Dole ya sameta yace Dan Allah tayi hakuri ta saurareshi. Tasha mur, au ni zan sameshi bashine zaizo yaban hakuri ba?...... Ohhh toooo kiyi hakuri zaizo, ta wuce abinta tabarshi wurin saboda yama bata haushi. Suna rabuwa ya Kira Anwar din yace tace Shi baida bakin bata hakuri ne? Gaban sa ya Fadi.....Anya zai iya tunkarar ta Yanzu Kam har ga Allah tsoron ta ma yakeyi. Haka ya kwana dardarce, ko barci kirki ya kasayi da ya tuna sai ya yi firgigi ya tashi zumbur. Jarabawar ta safe ce, farar shirt ya saka Mai kwala tana da ratsin ja, da farin jeans sai jar facing cap. Agogon hannun sa kirar *Rado* baka . Ya rufe ido da makeken glass dinsa Baki. ( Anwar akwai kyau da iya wanka ). Ba abinda gabansa keyi sai faduwa Anya zai iya mata magana? Duk inda ya gitta sai an kalleshi ya wanku iyakar wanka sai kamshi ke tashi. Yana tsaye jikin taga ya hangota sun taho tare dasu Aisha sai faman dariya sukeyi. Ya bude littafi kamar Yana karatu amma ita kawai yake kallo.....tana matsowa kirjinshi na Kara bugawa.....kafin ta iso har invigilators sun iso, dole ya shiga hall din ya zauna. Yana Zama tazo zata wuce yasa kafa tun daga nesa ta hango abinda yayi sai kawai tabi dayan layin. Ya rigata fitowa, Banda faduwar gaba har Yar kyarma ya Fara lokacin da ya hango tana fitowa. Ta zukunna gaban Helen tana fadin .....duba mun wannan shin sune characteristics din nan?....... Kamar daga sama taking yace *Bilkisu*........ Gabanta ya bada rasss!!! Maganar ta makale Mata.......ya Kara kiranta a hankali Yana tsaye bayanta..... *Bilkisu*...........Zainab wowo ce✍🏼😄😄💖
Chapter 24 · 0% Book details