← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 68

Sashe 56

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ta dunga kunduma ashar tare da Shan alwashin gobe sai ta ji dalili.
Bakwai suke da lecture ta munafuki Richard, akayi sa'a Aisha ma nada 7am
Suka fito abin mamaki har an goge motar...
Ta kalli Aisha wallahi kunyar hawan motar Nan nakeji Aisha..... Meye na kunya?
Kuma ba ga nikaf kin saka ba?
Kai nasan yau na gama shiga uku makarantar Nan..... Ke muje ni ki ajiye ni kada na makara ta bude motar ta shiga ... Ko Zaki ja mu....??? .... Ni??? Ta daki kirji.
Anwar yau ya mayar dani kauyen mu kike so ko?
Ba yanda ta iya dole ta shiga tare da bata wuta suma suka tayar da mota suna jiran ta fita su bita ( securities biyu ),, ta fita gate din a hankali tana Hawa titi ta chilla da gudu saboda sun kusa makara. Suma suka rufa Mata baya.
Duk da safiya ce duk tsiraren mutanen da wuce sai sunbi motar da kallo.....
Kai Anwar karshe ne, shida sadeeq kasa suka tako, a bakin gate ta wuce su, ya kyalkyace da dariya Sadeeq yarinyar can gudu take da mota fa...
Dan ubanka mu ba ka hana mu dauko ba?
Ya Kara dariya suna ta sauri....
Ta tsaya Aisha ta sauka saboda ba hanyar su daya ba ita ciki zataje Aisha Kuma nan farko farko.
Tana zuwa kowa yayo ma motar chaaaaaa..... Chinayye ta gane ta da gudu ta makale tana fadin Bilkisu oyoyo.....
Ya akayi Kika ganeni?
Ta fada a hankali , haba ya bazan gane ki ba?
Wai kinyi Aure?
Inji waye?
Eh Mana ance you are married woman now....no, not yet. But am engaged... With Anwar??.... Shigowar sa yasa ta Kyaleta, ya rufe idanun sa da facing cap abin mamaki kawai ya wuce baya yaki Zama kusa da ita.
Suleiman ya shigo sai kawai ya chanza layi ya koma can baya saitin Anwar din.
Sai mazurai yakeyi cikin facing cap.
Mugun na shigowa sai cewa yayi test... Hankalin kowa ya tashi, ko ajikin Anwar,
Nan da Nan Bilkisu ta Fara kyarma.....
Question biyu ce, ba Wanda ya sani Anwar kadai ya amsa da kyar Bilkisu tayi attempting ta biyun sai kuwa su chinayye.
Yana fita ya taso da sauri... Kin amsa?
Ta zumburo Baki Ina na sani?
Bakiyi ba kenan?
To me Zan rubuta?
Ya buga tsoki this man .
Nan da nan Yan class suka Fara kallon kallo.
Shi kuwa Suleiman Richard na fita shima yabar ajin.
Ya zauna bisa table Yana kallonta, budo in Miki bayani ya saboda gaba... Ta Mika mishi book din, duk nikaf din ta ishe ta ba yarda zatayi ne.
Ya Fara Mata bayani a hankali ya lura sai mutsu mutsu takeyi yace Wai ya akayi?
Nikaf din nan ta isheni wallahi Dan Allah in cire?
Ya danyi dariya cire Mana .
Ta kalleshi da sauri da gaske ko gatse?
Sai kawai yasa hannu ya cire mata..... Dai dai shigowar mufeeda.... Ta tabbata wallahi, kutumar uba... Anwar da gaske An daura muku Aure da wannan banzar..... Ji kake tasssssssss! Fassss.....ratssssss duk illahirin hankalinta ya bace ta gigice ta kidime shima ya razana ainun ganin Bilkisu tsaye tana wanka Mata wadannan marukan.............na rantse da Allah Akan *Anwar Zan iya kisa* don Haka ki kiyaye... Body guards suka gani cirko cirko nan da nan Yan ajin suka fara direwa ta taga saboda firgici.......✍🏼 Ayi hakuri da kadan.

*maman Abdallah*💖

*uwa Mai bada mama mom ( Maryam adamu tikau maman amannas) mom you are the best I love you so much Mom*

Wadanda ke cewa ba ni ke rubutawa ba a fada wa Mai rubutawa ta ci gaba da kokari Nima Zan dage wajen sharing.....😄✍🏼🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣6⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.

**************
*Federal University dutsinma*
Chapter 56 · 0% Book details