← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 68

Sashe 48

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe bakwai tana kitchen, daddy ya fito zai je office ya leka... Bilkisu a bani abinda ya sauka na jiyo kamshi ko Anwar din kawai keda shagalin?... Ya karasa maganar Yana murmushi.
Kaiii daddy ta fada cikin Jin kunya....
Har ciki ya shiga Rahina nata fere dankali, saratu na grating kwakwa, ya kallesu yau aiki ya karu ko?
Iyye hada kaza haka?
Ya bude oven.... Ta rufe fuska lallai yarinyar ashe catering school din bai tashi a banza ba...
Menene can?
Wipping cream daddy... Zakiyi cake ne?
Na Gama gashi can ma.... Ya sa hannu ya dauki daya ya Kai Baki..... Um um..ya naji wannan kamar ba irin Wanda ake Mana ba?...... Kai daddy ta Kara fada yayi dariya....
Mommy ta shigo ga break din can fa.... Zo kiga sonkai Bilkisu na hadawa Anwar gara ba irin ..... Kai daddy... Eh Mana.
Ta matso iyyeh lallai Shi yasa baji gida ya Fara daukar harami.... Ta bude tukunya.. hada Kan rago?......
Kai Kai Kai daukon kwano Shi zata zuba mun ja'ira..... Duk suka kama dariya.
Rayuwa irin ta gidan su Bilkisu tana da ban sha'awa......mommy ta kalli Rahina, yau taku ta sameku ko?.... Abinda na fada Yanzu kenan.... Daddy ku je falo Zan kawo muku nidai... Duk suka kwashe da dariya... Mommy tace komai Zaki debo Mana ko sai ankai wa Anwar din nazo na ce Zan Dauka..... Kaiii mommy Wai ya Zan ce baza ku ci ba ????
Suka fita suna dariya hannun daddy rike da cup cake Yana gutsira...
Ya kalli mommy in shaa Allah tarbiyyar da muka ba Bilkisu bazai taba Sanya muyi Dana sani ba.... In shaa Allah.
Ina ta fada akan catering school din nan Kika dage Kinga Yanzu amfanin yazo ko?
Ai na fada ma Kuma wallahi cewa yayi nata yakeso baya son na Yan aiki kaga Idan Bata iya ba zai aureta Yana sonta Amma can gaba matsalar dole ta taso.... Yaron Yana da rawar Kai akan Bilkisu hakan na bani tsoro, ya kasa danne feelings dinsa kin lura ko?
Hada yarinta ke damunsa..... Yes da giyar kudi.
Yama arzikin sa kankanta kawai hankali da natsuwa yaron ke bani sha'awa...da kunya Kuma....yes Yana da kunya of course.
Bilkisu ta shiryo musu komai a tray ta kawo Yana Shan Lipton da biscuit....daddy biscuit Kuma???
To wancen kwalayen biscuits idan bama ci ya zamuyi dashi na ce ku rabar Kun jibgesu.... Dasu mommy zata tafi sokoto ne na dibar Mana namu Yana store... Ohhh ban sani ba ... Ta ajiye ta koma.
Ya bita da ido, abinda ke tayar mun da hankali shine yanda yake son ringa nuna Mata komai da karfin tsiya..... Gaskiya fa.
Yanzu idan ya turo iyayen zuwa taushe zaka ce su kawo kayan baiko?
Eh, ki Bari zuwa dare zamu maganar kiji yanda na tsara lamarin.....
Karfe takwas ya fita office mommy Kuma ta Haye sama domin komawa barci.
Sauri sauri suka karasa aikin , goma saura kwata an shirya komai ta fada wanka.
Ta fiddo Kaya sunfi ashirin ta rasa wane zata saka?
Tabbas Bata son ta saka matsattsu tunda ya tilasta gyale zata saka.
Da kyar ta dauko wata doguwar riga bubu na boyel peach an mishi kwalliya da *Stones* blue. Dinkin ya bude sosai, ta yi simple kwalliya ta shafa light pink na lipstick..... Rahina ta kwankwasa Mata kofa... Aunty kizo.
Inji waye? Ta fada tana gyara lagen gyalen... Uncle Anwar ne gashi can na bude mishi falo.... Ki ce Ina zuwa..
Ta Kara feffesa turaruka a jiki.... Ta juya ta Kara juyawa a madubi sai Kuma ta danji kunya tayi murmushi ta fita tana takawa dai dai cikin plat shoe light blue kalar gyalen.
Tana bude kofa sai kawai ta kwashe da dariya ganin sa bisa dining table Ya Fara cin abinci.... Na shiga uku Kai baka bakunta ne Wai??????
Ya kyalkyace da dariya inayi Mana gashi ni nake zubawa kaina? Idan bana bakunta ai zanje ciki na Kira ki zuban ..... Ta galla mishi harara Kai baka da aiki sai ci..... To ai yunwa ba kanwar ubana bace ko?
Ta kyalkyace da dariya ya akayi Kika San Ina son kan rago?
Ta ce hmm, ya lunkuma harshe a Baki Yana um...um...um please budan can menene?
...... Wai Kai baka ko irin Jan ajin Nan?
Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Zaki Sanya na kware wallahi.
Daukon lemu Mai sanyi ni bana Shan tea wannan sai ku Yan gayu..... Ta Kara hararar sa.... Ya kamata na Sanya wa hararar nan doka duk lokacin da kikayi ta ......
Ta Mike kawai ta Isa inda fridge ta bude wane kala Zan kawo maka?.... Peach daukon peach dinnan Amma fa roba biyu Ni daya bata Isa ta.... Ta Kara dariya ohh Allah gamu gareka....
Ya Miko Mata chips da egg Fara ci Nim zanci irinsa..... Kana da cikin Zane ne?
Yayi murmushi Amma kajin nan dasu Zan tafi fa don sai dare Zan dawo.... Zaka dawo Ina?
Anan.... Ya fada Yana kallonta.. ke na dawo Abuja fa sai an koma school nida Kano......ta zaro ido duk kana me?
Ya nutsar da idonsa cikin nata yace duk Ina zuwa Ina ganin ki... Tayi kasa da Kai tana murmushi.....
Kill babba abinda kike son ji kenan ko?
Tun karfe nawa Kika tashi yau?
Ta Dan zumburo Baki ban koma barci ba tun asubah..... Nima haka ya fada Yana murmushi. Ta harareshi kana meye?
Ina kallon agogo na kagara 10 tayi kamar na Miki waya na ce na mayar dashi eight..... Ta yi Yar dariya yabi kuncinta da kallo..... Kinyi kyau sosai fa.
Ta ce hmmm.
Ni na yi kyau? Sabbin Kaya na dunka saboda zuwa Nan fa.... Ta kyalkyace da dariya Kai na bani yau to me nace?
Ya Dan Sha mur naga kamar Baki fahimci hakan ba.... mtsew ta ja guntun tsoki.
Yayi Yar dariya ya Mike Yana goge baki da tissue taso idan bazakiji ba muyi magana ba dadewa zanyi ba Zan barki kiyi barci sai na dawo da dare ko? Ya na maganar Yana tafiya tare da janyo hannunta..... Ohh Shi baya Jin komai ya Kai hannu ya tabani ni Bilkisu??.
Ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita.... Ya akayi Kika bar kayan can anan? Daddy yace ki mayar mun?
Ta daga Kai alamar eh,
Kin fada mishi in sonki?
Nan ma ta daga Kai?
Duk da haka bai karbi kyautar ba?
Ta ce eh,
Sunyi yawa?
Eh,
Yayi murmushi to Yanzu me yace?
Ta yi kasa da Kai yace ka turo iyayen ayi magana.... Ihu ya daka kawai sai ya Mike tsaye ya janyota ya Bata wani hot hug.
Ta zame ahankali ta zauna tana murmushi....... Dan Allah kizo na you hugging dinki...
Ta galla mishi harara ya zauna Yana dariya *Amma fa nazo da sa'a* .......kawai ta jiyo motar daddy alamar ya dawo.... Gama daddy Nan ya dawo.... Gooood ya fada tashi kije kice Ina son magana dashi.....
Ta zaro ido.... Meye zaka fada mishi?
Zan rokeshi yabar Miki kyautar nan bazan koma da ita ba.... Kai Anwar daddy fa baya son gardama.... Haba?
Allah.
Yayi murmushi jeki ce Ina magana...... Tashi kada ya shiga ciki please.... Ya mikar da ita...
Yana kokarin shiga ta fito daddy ka Kuma dawo? ..... Bilkisu kice ma Anwar securities din nan ya Basu damar Zama Mana tsayuwa ai babu dadi ko?...... Shine yace Wai zaiyi magana da Kai.... Ya kalleta da sauri Yanzu?
Eh, okay Zan biyo ta Nan Ina sauri ne nayi mantuwa.....
Police din da suka rako Shi suka bude mishi kofa ya shiga ta dayar kofar.
Ta dawo, yace na fito?
No. Zai biyo ta.... Ya banko kofa Anwar lafiya dai ko? Ana jirana office.... Da sauri ya sauka kujera ya zukunna.... Yayi saurin Mika mishi hannu taso inji menene???? Ya rike hannun sukayi hanyar fita.... Ya Kara kallonsa menene?
Ya kasa magana kunya duk ta kamashi.... Ya tsaya chak ya fuskance Shi...Anwar!
Ya Dan rusuna daddy Dan Allah abar Mata kayan bana son na koma dasu..... Ya kura mishi ido... Amma kasan sunyi yawa ko?
Ayi hakuri Zan kiyaye next time Amma now abar Mata don Allah.
Ya Kara kallonsa sosai sai Kuma yayi murmushi... Shikenan Amma bana so ka daina kaji ko?
Ya rusuna na gode Allah ya Kara lafiya da shekaru masu albarka...... Aminnnmm ya Rabbi.
Ta fada maka nace ka Aiko?
Ya Kara sunkuyar da Kai In shaa Allah zasu zo gobe... Yayi dariya
gobe yayi sauri zuwa asabar dai ko?
Ya noke Yana murmushi.... Shikenan sai na dawo ana jirana ......
Ya dawo Yana murmushi tana zaune.....ya karasa Yana fadin yace ki dauki kayan shikenan ko?
Ta kalleshi da sauri.
Yayi dariya rokonsa nayi, ya Kuma amince ... Ta ce hmmm.
Na ce mishi Zan turo gobe yace sai zuwa asabar....
Ta ce hmmm kawai... Yanzu Kinga Ina da hujjar cin uban Suleiman ko?
Ta zaro ido.... Dan Allah ka bar maganar sa, Zan fada mishi an Mana baiko...... Ban yafe ba Kika Kuma magana dashi ..... Ta zaro ido..lallai idan aka koma school akwai chakwakiya.
Ya Mike Zan tafi sai na dawo anjima kinji ko?
Ta ce toh itama ta mike, daukon kazar da wancen cake din dasu Zan tafi.
Ta sungumo mishi suka jera ya fizge gyalen tare da shafa gashin ta yaja.... Nayi sa'a fa domin Ina son yalo yalon gashi..... Rufen gashi ko na saki kayan Nan su zube... Da kin sake wasu wallahi.
Ya Kara shafa gashin Yana murmushi sannan ya mayar Mata da gyalen... Ta banka mishi harara... Kana da matsala wallahi hakan haramun ne... Astagfirullah na daina.
Ya fada Yana dariya...
Chapter 48 · 0% Book details