Sashe 21
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
ido sai ya kawar. Duk taji babu dadi. Ana Gama lecture wasu suka shigo alamar venue din su ne. Fitowa sukayi, ajin dake hade dashi ba mutane sosai Yana tsaye bakin taga tace Anwar muje Nan naga ba kowa......... Anwar let's snap please Helen ta karaso tare da dafa kafadarsa....... Wani dadi ya ziyarce Shi yace anzo wurin. Ya kalli Bilkisu okay jirani Ina zuwa. Kawai suka Fara hotuna. Kamar jira akeyi sai ko wace ta taso wasu ma wucewa zasuyi ga Anwar da farin jini Nan da Nan hankalin Bilkisu ya tashi ta kasa daurewa ganin yanda suke faman rikeshi wasu na kwanciya kafadar sa. Ta shiga ajin idanun ta duk sunyi ja..... Yafi mintuna talatin tana zaune ta ma kasa tashi suk tana hangensu ta taga. Sadeeq ya karaso maigadon ya naga kinyi zaune baku Fara ba? Eh, hotuna yakeyi yabar Ni Nan kamar sakarai, ta fada a wahale kamar zata kurma ihu. Malami ya shigo yace ku fita zamuyi darasi...... Haka suka fito tare da jingina jikin icce ita da sadeeq har lokacin hotuna sukeyi ko kallon inda take baiyi ba. Sadeeq ko zamu je ka nuna mun Dan Allah? Ta fada Rai bace........ A 'a ki jira ya Gama kinsan halin mutumin....wallahi yau Kam bana so ko da kuwa yazo. Tohhhh..... sadeeq yace kafin ya Kara magana sai ga Anwar din. Bilkisu muje. Ta kalleshi kallon da ya gwammace bugu dashi sannan tace bana so kaje kawai....... Duk akayo musu ratai da ido. Nan da Nan ya hasala don yasan a rina iyakar rainin wayo yarinyar nan ta daukeshi sakarai, Saboda me Baki so? Ya bukata a hasale.... Ina ce hoto ne a gabanka, ko? Ina jiranka mintuna kusan talatin.....Kai ma abokina meye haka. Zanci ubanka sadeeq...ya daka mishi tsawa. Kada Allah yasa taso waya rasa? Don kinga Ina lallabaki naje nayi hoton me ya hana kizo ayi dake? Ko Zaki hanani ne? Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya maka kaima......duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake. Sannan ya kalleta kada Allah yasa kiso ke Kika rasa........ Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka idanun sa sunyi jawur. Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina? Hakan take ta nanatawa cikin zuciya. Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse....... Ta zaro ido fada? Hmmmmm Baki San halin Anwar ba..... Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya shiga.... Yana zaune ya hade Kai da table. Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa, Anwar!.. Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa. Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba abokai . Ta Fara magana a hankali..... Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi .......bazanyi hakurin ba. Ya fada kamar zai mareta. Duk ajin akayi shiru ana kallonsu, Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki? Ni idan naje wurin malamai su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci cikin jama'a?...... Naji kayi hakuri,...... Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri.....gabanta ya Fadi. Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi....... Bazanyi hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi.....kawai yabarta wurin. Na shiga uku ni Bilkisu ta fada. Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa. Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin? Ni Anwar zai dizga? Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu? Me yasa tun farko na bashi fuska? Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har abada. Biji biji take ganin hanya....ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba.....ta bude daki ta fada bisa katifa sai kuka......... Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa Anas na shiga uku nayiwa Bilkisu wulakanci. Ya zaro ido me ya faru.? Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata.....naji me ya faru. Ya Mike kamar mahaukaci.......laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri. Zamu shirya .....ya fice dakin. Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take. Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa. Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no. Sa cikin wayarta. Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi. Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za'ayi C.A Kuma course din da tafi tsoro. Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi. Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though Shima ya Dan fada. Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali..... Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong. Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu..... Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya Mata hauka. Mtsew ya buga tsoki. Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din. Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo. Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi....... Alhamdulillah dama Ina ta addu'ar kada a riga ni. Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai haukace. Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara hasala....... Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya zauna tare da Bilkisu test.......🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Tirkashi.