← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 68

Sashe 37

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 3 min read

Aisha kadai ta tarar dakin a zaune ta tasa Kaya gaba tana kallo.
Ko takalmi bata cire ba ta fada bisa katifa....... Aisha na shiga uku.
Wai ya akayi ne? Fada kukayi da Anwar din bayan fitar ku? Naga alamun kinyi kuka Shi Kuma sai babbata Rai yakeyi...... Aisha Anwar yafi ciwon ciki.... Ta kwance Mata zance kaf!
Ko kadan Aisha bata razana ba. Sai tayi murmushi tace, ni wallahi nasan Anwar Dan manyan mutane ne. Haba kiyi tsam da Rai ki kalleshi da kyau ya Miki kama da mazauni kauye?
Ko fatar jikin Anwar Kika kalla kinsan ana rayuwa cikin A/C da Jin dadi.
Bari in Baki karamin takadiri ki kalli yanayin shigar da yakeyi duk kayan Anwar tsadaddu ne daga manyan kamfuna manya manya irin su *Gucci, M&S, C&K* ke gasu nan. Ji takalmomin da yake sawa..... Haba mutane, Ni wallahi nasan karya ne ace duk sadeeq ke musu sai dai na yarda shikeyi ma sadeeq saboda ko dressing yanayin dauka a jiki ma ba daya ba Koda kuwa iri daya suka saka .
Ji lokacin zuwan su daddy ke baki lura bane Amma wallahi wani taku da Anwar keyi nasan yaron yaji bariki wallahi.....
Ke ni al'amarin sa ya Fara bani tsoro Aisha...... Hakuri zakiyi sonki yakeyi Kuma ya kasa *FURTAWA* kawai idan ya Miki kina sonsa Ina Baki shawarar kada ki Bari wata tayi Miki shigar kutse sannan kada ki yarda ki nuna kin San inda ya dosa ki barshi har ya gaji ya *FURTA* idan da gaske yakeyi.
Koda yake wannan hauka haukan da ya Fara tabbas saura kiris ya *FURTA*....... Aisha bana iya wa Anwar har ga Allah..... Ba Kya son sa?
Ta tsare ta da ido...... Tayi shiru ta kasa magana.
Kinji?
Idan bai Miki ba ki fada mishi ya rabu da ke, naga dai yanda Yan Mata ke neman kashe kansu saboda Shi Amma ke ya zabe ki kamar tumun dare Zaki..... Understand me please.
I'll never understand you. Namiji kowa da kalar soyayyar sa, Anwar miskili, gadararre, Wanda ya Raina kowa kije kina bada labarin da kike bani Yanzu wani sai ya mare ki saboda cewa zasuyi karya kike yi amma Ni ganau ce ba jiyau ba.
Amma ji yanda yake Miki rawar kafa.
Wallahi Yanzu dan ana farkon dawowa ba mutane Amma tabbas ni nasan wannan semester din akwai daru za 'ayi kallo. Sai ki dage..... Abinda ke tayar mun da hankali kenan wallahi.
Tayi dariya zai tare Miki nasan dole ya..... Wani abun ba agaban sa zai faru ba Aisha.... Yanzu ni ya zanyi da wadannan Kaya ni Bilkisu.... Ci zamuyi. Yanzu fa aka dawo.
Ai wallahi mun gode......... Wayarta ta Fara Kara.
Ta kalli Aisha Anya Anwar zai barni nayi abin kirki wannan semester din?..
Tayi dariya ta kwashi biscuits da wasu tarkace tace keni sai da safe...... Taja Mata kofa.
Ta kanga wayar a kunne ba tare da tace komai ba...
Ko har wayar ma an Sanya Mata doka?.
Ya fada Yana Yar dariya.
Hmmm, kawai tace.
Ke na gaji da hmm, dinnan da kike neman ki ringa kawoshi bana son sa ki bude Baki kiyi mun magana kinji ko?.
Toh, tace a hankali tana murmushi.
Da gaske ba Kya so Ina zuwa wurinki?
Eh, tace da sauri.
Saboda me?
Ta runtse ido anya mutane sun San Anwar kuwa da ake mishi shaidar baya magana?... Kinyi shiru. Ya katseta.
Haka Nan,
Baiyiwuwa ki fada mun dalili ko Kuma gobe ki ganni...... Dokar daddy ce, sannan zuwan naka zai rinka haddasa mun fitina tsakanina da Yan matanka, idan Kuma aiki yayi nisa Zan Sami raunin karatu...... Zuwa gidan naku?
Eh,
Fine. Zan daina zuwa shikenan ko?
Eh, ta ce tana murmushi.
Idan Zan ganki muyi magana Kuma fa?
Chapter 37 · 0% Book details