← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 68

Sashe 49

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yana tafiya ta saki ajiyar zuciya tace kaiii Anwar case ne.
Ita da mommy suka bude jakunan.... Tsoro yasa suka mayar suka rufe..... Ta kalli Bilkisu yaron nan sai ya kusa haukata ki idan kukayi Aure...
Tayi jimmm... Kawai.
Tare da Sadeeq ya dawo..... Tana shigowa yace koma ki sako hijab........
Ikon Allah sadeeq ya fada tayi saurin juyawa.... Banza wallahi kwakwa ke kawo ka marar zuciya..... Naji kome zaka ce kai ne ka jawo ni dole na biyoka kuma na gama zaman zuruu...... Ya yi murmushi.
Abinda Zan Rama?? Kai kishin naka ma da bashi da aji..... Ya Kara kyalkyace wa da dariya, kishin har akwai Mai aji?
Ya mishi banza.....
Ta dawo rike da mango juice a cups..
.... Bilkisu kinji sadeeq Wai kishina baida aji kin yarda?
Ta ce hmm, kawai ya Miko Mata sim card ungo Ciro mun layinki.... Ta zaro ido...
Yasha mur yes dole ki canza layi ..... Dashi fa nake jin alert....wane bank ne?
Access bank. Ta fada cikin fushi.
A nan Kika bude account din ko sokoto?
Ta bishi da kallo.... Anan Abuja... Kawai ya dauki waya...hello , yes nine lafiya.
Zan turo ma wani account number please ayi blocking din sa zamu bude sabo amayar da komai can.... I don't know buh I'll ask her...
Ya kashe meye account number din???
Sadeeq kaga rigimar da Anwar ya kunno ko?
Ya danyi murmushi zamanki lafiya ki canza don tabbas kishin wannan zai janyo ma bank din matsala..... Tayi zugummm....
Ya figi wayar kawo na canza Miki..... Zan dauki no. Su Aisha.... Zan saka Miki duk no.s din kawayenki Mata Amma wallahi Kika yi saving maza sai......... Kana ganin Ina kula maza ne... Ta fada a hasale.... Ya dalla Mata harara su ai suna kulaki ko?
Ta Bata rai.... Sadeeq ya jiyo zaku Fara ko?
Hakuri zakiyi dashi fa halin sa ne ba yarda Kika iya... Ni bana son wannan zargin da yake mun... Na daina ya hakuri shikenan ko?
Tayi shiru. I'm sorry please. Shikenan ta fada tana hararar sa.
Yayi Yar dariya.....
Firar rigima rigima soyayya soyayya don ma sadeeq nasa Baki idan sun nemi rikicewa.....
Ya ce zai tafi Kano gobe zai dawo asabar Amma sai dare zai shigo bayan Baki sun tafi.
Ta masu rakiya ya hanata karasawa waje ya ce ta koma kawai....

Daddy ya buga ma kanen sa sokoto cewar yazo don su tarbi Baki, ya Kira yayan mommy da aminan sa biyu ministers.
An shirya gaggarumar tarba.
Misalin karfe Sha biyu suka karaso.
Abin mamaki ba kudi kawai suka kawo na neman Aure ba hada halawa da goro da biscuits.
Bayan an gama gaisawa aka ci abinci aka Kara gaggaisawa kowa ya gabatar da kansa, iyayen Anwar biyu ne daya kanen maman sa daya Kuma aminin mahaifinsa ne sai wasu dangin babansa daga kauye saboda baya son da yawa asan abinda yake ciki kamar yanda Hajiya ta gargadeshi. Daddy na gefe kanin sa ya Fara magana....
Alhamdulillah munji dadin kasancewa daku ayau ya Allah yasa wannan yaza alkhairi garemu Baki daya....
Mune da jin dadi hakika Hamza ya kawo mu gida na mutunci masu karamci Alalh yasa wannan yarinya tayi Hali irin na iyayenta....duk aka amsa da aminnn.
Ga Kaya mun kawo na neman Aure da kudi dubu dari biyu ya Allah yasa muga ranar da zamu taru haka da sunan dauruwar auren su, aka ce ammmmeeenn...... Alhamdulillah daddy ya katse Shi.
Duk aka kalleshi... Da sauri.
Kamar yanda na yanke shawara nida mahaifiyar yarinyar Nan da dangin mu, Ina ga a wannan haduwar mun Isa mu shaida Aure saboda haka na yanke shawarar wadannan kudin zamu karbe su matsayin sadaki goron Kuma aba kowa ya shaida Amma bisa ga sharadi..

Bana son yaran nan su San Haka har sai bayan sun kammala karatu tukun....
Masha Allah Masha Allah duk falon ya dauka nan da Nan aka Fara Shirin daurin

Aure kowa ya bada wakili..... Cikin mintuna da basufi ashirin ba aka ce faaaaatiiihaaaa.....😄✍🏼

*Zainab Dahiru wowo*💖💖😆
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣3⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.

***************
*ABUJA NIGERIA*
Chapter 49 · 0% Book details