← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 68

Sashe 60

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ya zuki iska ya fesar.... Gaskiya Ina bukatar matata .....ka rufa mata asiri Anwar Dan Allah kaifa da kanka kace zaka bada mamaki...... Kai nifa ba katako bane ko?.
Eh,but at least ka duba yanayin idan ta Sami ciki fa?
Shine me? Ya harareshi, Ina nufin kaga na farko tun a laulayi idan Mai Shan wahala ce an Sami matsala musamman ga karatunta, kaga automatic spill over, na biyu bazata taba fita zargin mahaifan ta ba cewar ita ta sanar da Kai akwai Aure bayan an gargadeta da tayi shiru,na uku karatu da goyo Anwar is not easy akalla.... enough jor.... Ya daga mishi hannu... Amma Zan ringa Dan romancing dinta gaskiya ban iya daurewa..... Romance din zai ringa Sanya maka sha'awa akwai ranar da wallahi zaka kasa controlling kanka tunda kamar yanda ka fada din Kai ba katako bane...... Ya Allah !!! ya fada tare da maida Kai ya kwantar bisa sit, sadeeq meye dabara?
Ina ga mu rage ziyarar su gida , ka ringa tsareta school duk maganar da zakuyi nasan idan kana ganin jama'a bama zaka kawo komai a ranka ba..... Nawaoooo,!!! Ya fada tare da tashi zaune.. gaskiya nidai an kwareni ....
Sadeeq ya kyalkyace da dariya rawar kanka ta janyo maka....... Ya Kai mishi duka, naje nayi.
Yanzu dai ai daga wannan semester din saura daya ko?
Biyu dai....
Ya katseshi ...ya ja dogon tsoki kawai ya kwanta tare da runtse ido. Sadeeq ya bishi da kallo Yana murmushi......
Wai ya mufeeda ta hakura ko?
Ya yatsuna fuska, ance har yau ta kasa shigowa school saboda kunya..... Maganin ta kenan... Ya tashi zaune Yana Yar dariya kasan ni duk wake bani dariya?
Ya ce sai ka fada.
Helen, tunda akayi case din nan Yanzu ko layin da nake zaune Bata bi kasan arna da shegen tsoro....... Suka kyalkyace da dariya.

Bilkisu ta zabga uban tagumi har lokacin jikin ta bai daina rawa ba, kirjinta kuwa sai dakan uku uku yakeyi, *Na shiga uku ni Bilkisu Wai kiss* .... Nikam dama na hakura da Abujan da Yanzu Ina can zamana qalau..
Ta runtse ido lokacin data tuna ya zagayo da hannayen sa bisa kirjinta ya kwanto jikin ta...... Tsikar jikinta tashi Yarrrr lallai akwai damuwa .... Ta bude ido su maza basa da kunya ko kadan....
Haka ta kwanta tana ta juye juye da ta tuno Shi da yanda ya ringa Mata sai ta kudundune jikinta ta boye kanta cikin filo.....
Murjanatu cikin masu aikin gidan ta Kira da sauri ta ce maza ta dumama tuwon jiyan kafin ta fito wanka.....
Yau taga amfanin nikaf, saboda da Babu ita tasan bazata iya kallon Anwar ba.....
Tana shiga ajin anata raba test din da Richard munafuki yayi. Two over ten, three mutum biyu keda 5 su chinayye...... Itama two taci, Anwar ya saka tashi aljihu kawai lokacin da ya buda yaga yaci nine....
Ya kame Baki na shiga uku.... Mutumen nan wallahi mugu ne daman yafi so mu fadi.... Sadeeq na bayanta ya ce nawa Kika ci Bilkisu?
Ta mika mishi 2 ce shegen kaifa? Yayi murmushi three..... Anwar yayi fit ya fizge takardar ya na zagayo ya kalli root dake kusa da ita yace ban wuri.... Ta kwashi takardun ta ta koma sit din da ya taso.... Basai ka fizge ba two ce kai nasan nine kaci don ma baya bada cikon da tabbas ten zaka ci....... Inji waye ya fada Yana murmushi....ta zumburo Baki nidai fiddo naga Ni...... Ya Mika Mata Yana murmushi.... Kamar jira ake taje hannun Bilkisu aka Fara rokonta ta bada ayi snapping.... Ta Mika musu.
Mutumen can na daga mun hankali bana kaunar Dan iska.... Yayi dariya Kuma duk da Haka Baki taba faduwa course dinsa ba ko?
Ta harareshi Amma da yake akwai nikaf bai gani ba tace da hawan jini, da na ruwa ko?,ya kyalkyace da dariya, toh eh Mana,duk sai ya gama tayar Mana da hankali tukun Kuma *E* din nan dai ce ko *D* ..... Ina laifi ai yafi carry over ko?...... Zatayi magana malamin ya shigo..... Ya fiddo waya ya dan Mata magana a hankali..... Shiga WhatsApp...
```kinyi barci jiya?```

Ta maida mishi da ```me zai hana?```

```ni kuwa kasawa nayi saboda tunanin ki```
Ta kasa cewa komai

```kinji```
Ta ce ```Hmmm```

```smiles kin zo mun da tuwon?```

```yana mota```

```ina zamuje naci```?

```ina fa, anan waje ko?```

```Bana son waje is too open let's go to the field or new lecture rooms side I need quite place okay?```

Tayi shiru.

``` kinji ko?```

Ta maida hankali gun lecture.... Ya zunguro ta da hannu ....dole ta rubuta mishi

```naji```

Yayi murmushi.

``` sai Anja mun aji?```

```Ka bar mu muji lecture Anwar```

.....```ke ni ban wani ganewa ki Bari kawai zamuyi tutorial```

```Hmmm```
Malamin na lura dasu,
Yana gamawa ya ce tear a sheet of paper write your number only......

*Mun shiga uku ka ga abinda nake gudu ko?*
Ya sumke Yana Mata dariya.

Kina da black biro?.....
Banda Shi ta fada cikin tsiwa.
To kiyi sauri ki wanka ko na rubuta miki,?
Kawai kayi na kwafa idan Kuma ya tayar Dani shikenan.....
Yayi murmushi....
Ya Fara dictating questions based on what he discussed.
Ta Kara tsure Mata tana magana kasa kasa ... Wallahi kana ja mun wannan semester din..... Yayi shiru Yana murmushi Yana rubutu.
Tana kokarin Jan layi ya turo Mata takarda har ya Gama Daman two questions ne. Ya ci gaba da rubuta nashi Yana layin karshe kawai malamin ya ce hands up...... Amma sai da ya karasa Kai Anwar karshe ne......ta galla mishi harara cewa zakayi kasan abinda ka taka, yayi dariya to meye acikin nan cubweb theory din ke da wahala?
Chapter 60 · 0% Book details