Sashe 20
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana son buga tsalle ya kasa , kanshi ya kumbura jinshi yake Babu kamar sa, ya gyara kwalar rigarsa sannan ya kalleta sama da kasa I warned you several times but u refused to listen to me, idan takamar ki *Hauka* ki sani Nan school din akwai *iyayenki*.........Shima yasa Kai yabi bayan Bilkisu. Wuri ya dauki ihu.......mufeeda tayi tsaye ta kasa motsi tana sonyin kuka Amma ta daure kada ta Kara zubda ma kanta abin magana...... Yasan wata sabuwar rigimar ce, tana niyyar Zama Aisha tace me Kuma ya faru naji ana ihu? Ni da waccen sakaran fa, ta tareni jiya suna mun wani kuri na banza akan Anwar shine na kaita gabansa nayi Mata nawa gargadin ta gane cewa ni ba tashi nake ba........wa? Aisha ta bukata tana zaro ido.....dai dai lokacin da ya karaso tayi kamar Bata ganshi ba tace *Anwar* Mana. Me nayi? Ya bukata tare da tsareta da ido, Wai ke me yasa bakya Sona da kwanciyar hankali? Ta kalli Aisha tana Yar dariya kinji fa? Sannan ta kalleshi, Da sunyi mun tsinannen duka jiya ai Ni Dana shiga tashin hankali ko? Ya zaro ido, duka? Ta balla mishi harara wallahi tallahi duk ranar da ka janyo mun duka wajen ajabon Yan matanka a school dinnan har Kai sai sunja maka bala'i don security office zanje nayi reporting......ya kyalkyace da dariya Yan matan nawa ne ajebo? Ke meye naki da zasu dake ki? Ban sani ba kaje su baka amsa........ya Kara dariya matsa in zauna.....da sauri ta matsa ganin Yana kokarin Haye Mata kafa.......kana da hankali Anwar? Wani lokacin Ina taba hauka,, ya fada Yana dariya. Aisha Mike Kai wallahi bazan biye muku ba Bari in koma baya inyi karatu. Ita da yunkura zata tashi yayi saurin rike habar hijab dinta ya mayar da ita ta zauna....... Ba inda zakije wallahi. Wai ke me yasa kin rainani? Idan kina son abu gardama banayi sai nine Zaki ..........zaniyi me? Mutane fa na kallon mu ya sunan abinda kayi? Aisha ta girgiza Kai ta wuce tana murmushi. Tasha mur, karatu zanyi ko ka tashi ko Kuma Ni na tashi.......babu daya ciki. Kiyi abinki bazan dameki ba. Gobe ne birthday dina me Zaki bani gift? Tayi murmushi kai dai ka cika roko wlhi. Zan siyi ledojin pure water na ba Yan class suyi maka wanka, Tabbb, ai bazan zo class ba gobe saboda hakan. Wasa kakeyi ...... Allah kuwa. To shikenan ka huta. To meye Zaki bani? Ta kalleshi cike da kosawa to meye Zan baka ne? Gift!, Yace Yana Yar dariya. Ta Sha mur, ka Fadi abinda kakeso Zan baka. Zakiyi mun special girki, sannan ki kaini shopping.......... Ta kyalkyace da dariya. Yabi kumatun ta da kallo Yana son dimple dinta ainun. Shikenan Zan maka what next? Karfe nawa zanzo? Da safe kafin na tafi class kaga gobe har 6 Ina school.....no is too early. Bayan magrib dai......... Bana fitar dare sai dai kazo 2 kafin muyi lecture 4........ Hmmm shikenan ya fada ba don ransa yaso ba sai don gudun kada tace duka ta fasa. Tare suka shiga test din ka kujerarta ga tashi. Ta kanga mishi fuskar computer din Yana tashi yanayin nata. Sai gashi suna gamawa taci 20/20 Shi Kuma Yana da 18/20. Tayi ta tsalle tana Murna. Sun jero sai dariya takeyi tana Jin dadi, ta kalleshi yau wace rana naci CBT 20 last session wallahi naci da yawa 11 ko 12. Murmushi kawai yayi. Ta hango su Aisha shikenan bye bye wanna go thank you till tomorrow. Ya juyo zai magana tuni ta tsallaka tana sauri so takeyi kawai ta Basu labari. Ya danyi tsoki kawai ya wuce. Nawa kuka samu? Aisha ta yatsine fuska 13, khausar tayi tsoki Ni 10....... Wallahi saura kadan na shiga cikin department dinku Kinga ruwan Yan 7,8 da 9? Ta zaro ido wallahi Anwar yayi mun duka na cinye........duk suka zaburo 20?. Cike da Murna tace wallahi kuwa. Ohhh Allah ya kashe ya Baki inji Aisha. Ai yau nayi sa'a Kuma wallahi ba layi daya muka hau ba. Yana tsaye shagon Abdul ya hangosu. Kamar ya kwada musu Kira kwatsam sai ga Dr Dan Musa ya tari gabansu. Bilkisu see me by 2 in ma office........okay sir. Ta ce kawai suka wuce. Wahalalle naga ubanda zai gani. Baki zuwa? Inji khausar, Eh, kullum aikin kenan kuma ba wat maganar arziki ba kame kame. Anwar ya bishi da harara lokacin da yazo zai gitta. Bayan sallar la'asar ta tafi dakin su Jennifer sukayi mata kwatancen gidan zainab wowo wacce keyi wa Yan makarantar cake. Ta iya cake sosai na biki da birthday ga sauki. Aisha ta rakata. Mata Mai fara'a ta amshe su hannu biyu biyu. Sannan suka ce cake sukeso na birthday Amma na maza. Tace ba matsala. Ko na nawa kike so Zaki samu. Kuma karfe nawa? Akwai Wanda Zaki ba yakai man goben wajen 1:30 haka? In shaa Allah bani number da za a nemeki da ita. Sukayi musayar number ta biya kudin babban cake na gani na fada. Bayan sun fito ta kalli Aisha Zan surprising din sa ne. Suka biya super market ta siyo manya manyan lemuka carton daya *na grapes* Hmm kawai Aisha ta ce tana murmushi. Ta harareta, Fadi ta cikinki Mana, *there's nothing ooo just wanna surprise him and show my gratitude on what he has done for me Sha* I knew, inji Aisha tana Yar dariya. Karfe shidda na safe ta tura mishi text ```Happy birthday Anwar wishing you more dollars in your account, you are an amazing person stay blessed``` KO minti daya ba'ayi ba yayi reply ``` Thank you my personal person``` Murmushi kawai tayi. Shi kuwa ya karanta text din yafi sau dari. Ko wa ka gani a class da ledar pure water saboda Shima haka yakeyi wa mutane Amma ba Anwar ba alamar sa, ko su sadeeq Basu San cewar baya zuwa class ba. Bilkisu kadai tasan haka. Sadeeq ya karaso kusa da ita hajia Kira Mana Anwar please... Tayi murmushi yace yau bazai shigo school ba. Aji ya dau surutu suka ce ko hostel ne yau sai sun bishi. Kamar yanda sukayi alkawari da zainab sai ga cake...... Cake abinda ka cake sky blue yayi kyau karshe an nado Shi a leda cikin kwali. Sai kamshi ke tashi. Flowers din sunyi kyau Mai Rose ne da wasu design cake din ya tsaru. Tana kwance daki ya kirata. Yana jiranta bakin hanya. Ta ce toh, sanye yake da round neck shirt orange Mai ratsin fari a jikinta an rubuta *You are mine only* a gaban rigar. Dark blue jeans ne wandon da facing cap Fara anyi rubutu orange *Mine for ever* daga sama. Kunnensa like da ear piece. Kanta a kasa tana tafiya a hankali. Ya saki ajiyar zuciya kadan idonsa na kanta har ta karaso..... Murmushi ta sakar mishi kafin tace happy birthday once again. Godiya! Ya fada Yana latsa waya Shi adole ba kallonta yake ba. Ta harareshi dai dai ya Dan dago. Yayi murmushi ko amsar Bata Miki ba? Yayi kyau karshe....ta fada a zuci a zahiri Kuma tayi shiru kawai. Muje.......tace tare da yin gaba kadan. Ki jira muyi hoto Mana..... Da wa? Tabb Ya Dan Sha mur, dake ko bazakiyi ba? Eh, tace tana Kara ci gaba da tafiya. Yaji haushi sosai. Are you serious? Ya biyota. Ta Dan waigo *did I look like a joker?* Dan Allah kizo muyi pic Bilkisu........ Ta zaro ido Wai da gaske kakeyi? Sai ta danyi dariya kawai ta sunne Kai.... Ya ja tsoki, don ya karanci kunya takeji. Suna Isa shagon ta ce me kake so? Ya Sha mur Yana fushi duk abinda ya Miki. Tayi kamar Bata lura ba ta amso meat pie da soya milk drink na cikin kwalba Mai tsadar guda goma. Ta fito, gashi sai me? Ya karba da hannu daya dayan Kuma Yana latsa waya. Yace shikenan thanks. Duk taji ba dadi kamar tace suje to suyi hoton Amma gaskiya Bata iyawa. Suka jera zuwa bakin hanya sai fushi yakeyi. Zaka koma hostel ne? Akwai abinda Zan Miki ne idan na tsaya? Zan baka sako ne muje da mashin din a bakin gidan mu ka karba....... Ki je ki kawon Ina Nan. Har lokacin fuskarsa ba fara'a. Ta langabe Kai Wai Anwar fushin na menene? Mtsew kawai yaja guntun tsoki. Kaji? Oh my God , me kike so Yanzu Wai? Muje ka karbi sakon. Jeki gani Nan zuwa. Har zata Kara magana sai Kuma ta fasa ta wuce don itama ta Fara kulewa. Tana niyyar shiga gida taji tsayuwar mashin, da sauri ta waiga sai kawai tayi murmushi ganin shine ya Dan harareta. Tayi ciki tana dariya. Kwalin lemun ta Fara fitowa dashi tasa agaban mashin din sannan tace Ina zuwa ku jira. Ta dawo da cake din ta Mika mishi ga cake kaci sosai........ Da sauri ya kalleta. Tayi murmushi. Kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yace da Dan mashin din muje......... Kamar tace dawo muyi hoton Amma bakinta yayi nauyi. Haka ta shiga gida sukuku............ A hostel party sosai akayi yaji dadi abinda tayi mishi Yana son Allah ya kawo ranar da Shima zai Bata mamaki. Amma rashin yin hoton nan ya Bata Masa rai matuka, ya Fara gajiya da halin ko'inkula da ta keyi mishi, yanda Yan Mata ke rokonsa akan suyi hoton dashi Amma shi yau yabroki mace suyi taki amincewa *dame Bilkisu ke takama?* Wajen Sha biyu ya tura Mata text *Thanks for the cake* sai da safe ta gani. Bata Sami halin reply ba. Yana zaune ta shiga class din Koda suka hada ido tayi murmushi Shi Kuma ya daure fuska ya kawar da Kai. Gabanta ya fadi, ranta ya Fara baci menene abin Jin haushi daga tace bazatayi hoto dashi ba? Ya taba ganin tayi hoto da wani ko wata? Ta ajiye books dinta ta Isa wurin sa. Ina kwana? Ya dago Kai tare da cire ear piece. Ya kalleta Yaya? Fuskar sa ba yabo ba fallasa, Zamuyi macro after this lecture please if you are free........ It's alright. Ya fada a takaice. Ta juya ranta ba dadi. Yan aji sai zolayar sukeyi jiya yaji tsoro baizo class ba kada a mishi wanka yana ta dariya da yazo zasu hada