← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 68

Sashe 47

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Assalamu alaikum*
Masoyana Ina alfahari daku.

Nazo da wata tsaraba, hausawa na cewa kula da Kaya.......

1. Ina wacce ke fama da karancin ni'ima?
2. Wacce ke fama da budewa tana son jinta a matse da ni'ima sosai?
3. Ko kinsan yawan zubar da ruwa wani lokacin matsala ne? Wacece keson taji ta adai adai?
4. Wacece mijinta baya gamsar da ita?
5. Suwa ke fama da infection?
6. Akwai matan da har yau Basu San dadin Aure ba sam Basu Jin sha'awa ko kin San dalili?
7. Wacece keson ta gyara nonon ta da jikinta yayi luwai luwai?
8. Ina wadanda mijinsu baya gamsuwa dasu?
9. Wacece kullum sai tayi amfani da lubricant saboda karancin ni'ima?
10. Ina wadanda miji ke musu gani gani da hargagi kullum?
Akwai supplement masu kyau na dukkannin matsalolin aure daga zainab wowo, direct order ne muna turawa ko wane gari Amma Kano, Abuja da katsina zaku sameshi free delivery in shaa Allah. Masu bukata su tuntube Ni. Darajar annabi da alqur'ani serious buyer nake bukata Dan girman Allah na rokeku. Ga number ta 08089973394 in shaa Allah.🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
2⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

👉🏼💞💕💕 *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*🥰😍😘.

*Wannan page din na sadaukar dashi ga dukkan masoyan wazai furta*💞💗
Shi yasa yau na saki biyu don kuji dadi farincikin ku shine nawa wallahi.😭😭 Ina son ku😍😘🥰 kullum sai nayi kukan dadi.

**************
*ABUJA NIGERIA*

........ Ya tallabo bayanta ta dawo ta tsaya dai dai Amma ta kasa yarda su hada ido, *INA SON KI BILKISU* Yau na *FURTA* Abinda kike son ji..... Ta Kara kasa da Kai jikinta har lokacin bai daina kyarma ba....Wai mafarki takeyi ko kuwa da gaske ne?
Ya rungumota ta sunne Kai jikinsa.... Ya Kara Rada Mata... *ina son ki* tsikar jikinta ta tashi Yarrrr..... Duk wannan haukan da Kika ga inayi sonki nakeyi, Shi yasa na kasa boye kishina gareki...... Nasan kin fahimta Yanzu Kuma kin Sami amsar fadawa su daddy ko?
Ya dago fuskarta....ta koma da sauri.... Ya kyalkyace da dariya yau Kuma jikina ake son Hawa?
Kin wahalar damu da yawa, kina kawo rigima kullum because you want me to say it.... Ni nasan kina Sona I knew it...Kuma ko Baki furta ba nasan kina Sona wallahi....... Ki daga ni na tafi... Ya fada Yana dariya.
Kinga duk laifin ki ne, da kinsan zakiji kunya da hakuri kikayi muka tafi a Haka bakiji komai ba..... Ta zame a hankali ya mayar da ita da sauri, kafin ki gudu Dan Allah gobe kada ki Sanya mun hijab din nan kuma kiyi mun girki da kanki Zan zo around 10:00am kinji ko?
Ki ce b lefe na kawo ba, hasafi ne saboda Ina son ki.... Ta zame yayi saurin rike hannun ta ki jira na Baki kudin dinki Mana ..... Ka barshi nidai... Bakya so?
Ta daga Kai..... Da gaske bakya so?
Um, tace a hankali.
Yayi Yar dariya kudin ke Baki so ko Ni?
Kudin ta fada tana sim sim da Kai.
Yayi murmushi Ni kina Sona Kenan?
Ta yi alamar fizge hannunta.... Ya rike gamm. Kice inji Mana kina Sona?
Ta yi kasa da Kai ji takeyi kamar ta bude kasa ta shige ta huta.. ...ya Kara dariya sosai ohh ni Anwar Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu?
Ai Dana San wannan kalmar ce zata sa in Sami saukin tsiwa da tuni na Gaya Miki saboda na Dade Ina dakonta.......
Idan daddy ya Baki zabin auren mu kice kinfi so ayi kafin mu Gama school....... Lokacin ne ta banka mishi harara da sauri ta kawar da Kai.
Ya Kama dariya ya figi hannunta zo kiyi mun rakiya naga alamar nema kikeyi ki gudu ciki ko?
Ta biyoshi a hankali yasa hannu ya fiddo rafar kudi ya ajiye hannun kujera idan kin shigo ki wuce dasu na dinki ne....na gode. Ta fada a hankali. Tayi murmushi ya ce my pleasure dear.
Ta Dan harareshi ya tuntsure da dariya shin na Riga na *FURTA* ai to boye boye name?.
Suka fito tayi saurin fizge hannunta ya Kama murmushi Yana fadin ke dai Yar kauye ce...... Allah yayi?
Sadeeq ya taresu.
Allah yayi sadeeq yau kwana ta saka ni sai da na *FURTA* Ina son ta...... Sadeeq ya you firgigi ya ce waoooh *Anzo wurin kenan*.... Duk suka bushe da dariya ita ko sai murmushi takeyi kasa kasa...... Munafuki ai duk Kaine tun farko kayi ta wahalar da ita... Shin ai nadai FURTA gobe Zan dawo *Zance* ya bangajeta da kafada ko Bilkisu???
Ta galla mishi harara suka kwashe da dariya.....
Kiyi mun tuwo goben.... Ya shiga mota tana tsaye har suka fice gate din....
Wai da gaske ka furta kana sonta?
Wallahi kuwa, sadeeq rigimar Bilkisu bana iya daukar ta, ta tsareni lallai sai tasan wanene Ni...... Saboda me zaka boye Mata Wai?
Ai na fada.... Amma fadar sai ta tsorata Kuma. Na rasa me take so, Kuma Wai ita ya zata fada a gida wace amsa zata bawa su daddy....na ce kice *Ina son ki* saura kadan tayi penting .....suka bushe da dariya...... Amma ka Mata gatsal! To ya zanyi da ita? Kaga yanda ta nemi ta firgice mun?
Banza finally ka furta dai.
Yayi dariya *Anwar ya furta* naji tsoro yarinyar Ina son ta saboda class wallahi.....gidan sa dake *Minister's hill* suka nufa.
Mommy..... Mommy ta Fara kwada Mata Kira tana Hawa sama.
Tana faman shirya jaka ta shigo dakin, mommy Anwar fa ya kawo Kaya da yawa ..... Wane irin Kaya?
Ina daddy?
Sunje sallah kasa.
Wane irin Kaya ne ya kawo.
Jikunkuna ne set hudu.... Ta kalleta da sauri jakunkuna? Na menene????
Ta sunkuyar da Kai ta sunga Mata kudi Kinga Wai su Kuma nayi dinki...... Duk Akan me?
Ta Kara kasa da Kai, ya ce tsaraba ce ya kawo mun.... Saboda???...... Ta Kara katseta da sauri.
Ya ce Yana Sona ne???
Muje naga kayan, bazaki ce mishi daddyn ki ya hana karbar kaya ba?
Wallahi duk abinda na kokari in sanar dashi bai yarda mommy.
Wohohoho ta fada tare da rabka salati...... Amma kin San daddyn ki zaiyi fada ko?
Mommy Anwar Shi ne *Hamza bushara*..... Mun sani. Ta ce a takaice ta zaro ido Kun sani mommy?
Yes, ta fada tare da wucewa tana fadin jekiyi sallah nasan fada ne yau duk sai mun Sha ni da ke.....
Ta falon ya shigo Yana ganin kayan ya kwala ma Bilkisu Kira.
Ta fito da gudu gudu.....

Wadannan kayan fa? Ta sunkuyar da Kai, Anwar ne ya kawo su daddy.
Na menene?
Ya ce tsaraba ce kada yazo hannu biyu....
Saboda me?
Tayi jimmmmm kafin ta ce *Wai Yana Sona ne* yanayin yanda ta Fadi maganar kamar Yar koyo mommy ta shigo ya kalleta Kinga Kaya?
Hada kudi....
Ya kalli Bilkisu ke kina sonsa?
Tayi shiruuuu kinji mamana kina son sa?
Tayi kasa da Kai kawai.... Yayi murmushi kina son sa kenan.
Ki mayar mishi da su kice bana karbar irin wannan kyautar idan har da gaske yakeyi ya turo iyayensa.... Ta dora hannu saman Kai.... Daddy bayar Dani zakayi haka da wuri ta kurma ihu tana kuka.
Ya yi Yar dariya, to tunda kin Sami Wanda kike so me ake jira..... Nidai kada a turo...ke bama son rashin wayo.
Turowar an fada Miki Yana nufin za'ayi Aure?
Hakan zai nuna idan da gaske yakeyi sai a ajiye magana.
Ta danyi shiru alamar ta gamsu.
Ya wuce Yana girgiza Kai Yana murmushi,
Mommy ta kalleta tana hararar ta, wannan koke koken ba komai zai janyo Miki ba sai raini wurin Miji. Komai ke sai ki bare Baki saboda kina ruwa ruwa.... Mtsew ta ja tsoki.
Wannan rawar Kan da Anwar keyi inba auren ba meye zai kamance ku?.... Mommy..
Yi min shiru, Ina ce Nan Kika diririce Kika firgice saboda yayi fushi da ke ko?
Ta zumburo Baki kaiii mommy....... Ke arrr kilibabba.
Ta wuce , ta Mike ta bita da gudu mommy yace zai zo gobe by 10... Sai kije ki fadawa su Rahina don su shirya mishi kin dai San ba Mai sauko Dani da safe ko?
Mommy cewa yayi ni Zan girka baya son nashi...... Sai kawai tayi dariya tace yaron nan hooo.
To ya kyauta ma kansa sai kiyi asubanci saboda na sanki da shegiyar nawa da duminiya, Bilkisu za a Fara wa miji hidima..... Kai mommy ta bita tana shagwaba....
Ta kyalkyace da dariya. Ai munji dadin zuwan sa saboda kullum daddynki cikin waya yakeyi Yana jiyo labarin badakalar ku.....kamar ya mommy??
Tayi Yar dariya akwai wadanda kebin movement dinku kullum...... Ta zaro ido yasan Anwar na zuwa gurina mommy???
Tayi murmushi har ciwon cikin da kikayi ya je har cikin dakin ki,sannan ya balla Miki kofa.... Ta zare ido na shiga uku na... Ke dakata, tunda bai nuna Miki ba wallahi kada ki nuna kin sani Babu ruwana.... Cikinta yayi kulululu ta hadiye miyau kut!.
Mommy Dan Allah laifina ne? An fada mishi Nima bana son haka ko?
Ina Jin abinda yayi saving din ki kenan....
Ta saki ajiyar zuciya kaiii Anwar case ne.
Ko bude kayan basuyi ba yanda suka ajiye haka aka barsu a wurin.

*WASHE GARI*
Chapter 47 · 0% Book details