Sashe 14
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ayi ta hakuri kaman yarda na ce Ina da hidindimu Shi yasa
*Zainab wowo ce*...✍🏼💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣7⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*Ina alfahari daku kawayen yarinta:*
*Rakiya Amadu m/bread da badiyya Amadu m/bread*
***************
*Federal University dutsinma*
Aisha, sumayya da khausar sune kawayen Bilkisu na kut da kut!, Tare suka zo makarantar secondary school daya sukayi watan federal Bakori dake shiyyar funtua ta jihar katsina.
Aisha da sumayya political science sukeyi, khausar na micro biology sai ita Bilkisu dake Economics.
Su ukun dakin su daya, Bilkisu kadai ke nata dakin.
Mafi yawa su ne suka fi zuwa dakinta ko a secondary ana tare Amma ita komai nata daban ne.
Tana yawan yin girki baka raba ta da ko miya ce Shi yasa Mafi yawa sune ke zuwa wurinta neman abincin musamman irin lokacin da semester ta raba tsakiya komai yayi zafi.
Khausar na bala'in son Anwar Amma tun lokacin da ya dizga ta daga magana taji ya fita ranta.
Aisha ce ta shigo dakin tana ta kokarin yanka carrot da zata Sanya cikin farar hinkafar Daman tun safe kafin ta fita tayi miyar kifinta.
Ke yunwa fa nakeji har bana gani.
Tayi murmushi to gashi Bata karasa tsanewa ba ko zakiyi tsame yau ma?
Mtsew tayi guntun tsoki, tare da kwanciya bisa lumtsetsiyar katifarta, wannan uwar shinkafar Kuma fa ko yau kin tabbatar zamu zo kwaraka ne?
Ta dan tabe baki Anwar ne Mana da rigimar sa nace zanyi girki Wai zaici na tafin mishi dashi class 4 idan zamuyi tutorial.
Hmmm, kawai tace.
Ta Dan waigo Fadi kada ta kasheki.
Ta kyalkyace da dariya keji Kama Kai ai bandai *furta* ba ko?
Murmushi tayi kawai,
Daga Nan Bata kara mata magana ba.
Yar madaidaiciyar cooler ta samu ta zuba mishi miyar Kuma tayi amfani da Yar roba Mai marfi.
Saboda kurewar lokaci a daki tayi sallah tun kafin ta sallame yayi mata missed call biyu.
A gurguje ta shirya ta fito.
A bakin gate ta kirawo shi, bugu daya ya dauka.
Malama kinfa shanyani,
Ya hankuri gani na shigo school kana Ina?
Lecture room 2, ya fada.
Okay I'm coming......ta kashe wayar.
Sanye take da doguwar riga ta lace coffee brown, hijqbinta kalar flowers lace din maroon.
Tana saka kafa wayar ta na Kara *Daddy ne ke mata video call* ta karasa da sauri tana murmushi.
Ya hangota Amma sai yayi kaman bai ganta ba har ta zauna kusa dashi dai dai kuma lokacin da ta ajiye mishi ledar abincin sannan ta latsa wayar.....Hello daddy. Ta fada tare da fadada murmushinta zuwa Yar dariya.
Yabi fuskar ta ta da kallo Yana masifar son tayi dariya Shi kadai yake ganin abinda yake gani.
Bilkisu ya kike?
Kina class ne?
Eh daddy kaga nazo karatu ne wurin Anwar ta kanga fuskar wayar saitin Anwar din.
Yayi saurin sunkuyar da Kai...... yarinyar nan nada hankali kuwa?
Anwar?.......ya dago ido da sauri....barka da wuni Daddy ya fada da sauri tare da rusunawa Yana Dan murmushi.
Dariya yayi ......Kaine Anwar? Yau ba'ayi fadan ba kenan?
Ya zaro ido kadan kunya ta baibayeshi yayi saurin kallon Bilkisu atuhumce.
Ta janye wayar.....mun shirya daddy yaban hakuri ta fada tana dariya.
To yayi kyau. Allah ya taimaka a kula dai kada amanta Allah Yana tare da kowa a zahiri ko badini.
Na sani daddy.
Ta zaro ido Wai daddy kana sokoto ne???
Eh mun zo nida mommy bikin saifullahi ko?
Ta zumburo Baki daddy......ke sai anjima kuyi karatu kada lokaci ya shige......
Daddy zakuzo din ko?
Eh in shaa Allah zamu shigo jibi......yeeeeeee ta fasa Kara yayi saurin latse wayar Yana dariya.
Ta kalli Anwar su daddy zasu zo jibi......ya dalla mata harara. Ya akayi yasan muna fada?
Ta danyi guntun tsoki.... Ai sun Sanka Ina Basu labarinka sosai.....kina cewa me?
Tayi murmushi.
Kinji?
Hmmm kawai tace.
Magana zakiyi meye kike fada ne?
Ka gane sun San wajen ka nake daukar karatu to ya kirane yace yau bamuje karatu ba nace munyi fada dakai shine........yaushe mukayi fada?
Me yasa zakiyi karya? Sai kice fushi nakeyi dashi ba kice muna fada ba.......naji sorry oya muje ta bude littafin.
Ko sai kaci abincin zamuyi?
No, Zan tafi dashi hostel ne.
Okay.
Lafiya lau sukeyi tana ganewa sosai, yana magana tana satar kallonsa idan taga ya maida hankali ga littafin sai ta daddage kuwa ta Kura mishi ido.
Yana da kyau, natsuwa da Kuma kamala problem dinsa kawai miskilanci.....da yazo zai kalleta sai tayi saurin kawar da ido....haka..haka....sunyi nisa sosai sai taji an kwada mishi Kira ```ANWAR```.....
Dukkansu suka kalli wajen... Mufeeda ce.
Gaban Bilkisu yayi mummunan faduwa.
Saboda, mufeeda ana raderadin budurwar Anwar ce physics department take yarinyar ta hadu karshe saboda iya daukar wanka, Bata fi Bilkisu kyau ba Amma saboda iya gayun ta yasa idan tana wajen baza'a taba ganin kyan Bilkisu ba da kullum cikin hijabi.
Sanye take da wani material dinkin Riga da skirt, tayi kyau matuka fuskarta sanye da kwamemen glass ya mata kyau sosai.
......... Ta tsaya daga jikin taga alamar ganinsa take sonyi.
Kawayen ta Kuma na gefe suna jiranta.
Ya kalli Bilkisu please Ina zuwa, ya mike.
Wani abu ya taso mata ya tokare a makogoro tunda ta yi kasa da Kai bata dago ba.
Tana ta latsa waya ta ma kasa gane inane take shiga tana fita.
Agogo kawai take dubawa.
Mufeeda nada daukar hankali, kafin kace me.....Anwar ya fara shafa'a.
Ai nayi tunanin bazaka taso ba tunda ance tsoron ta kake ji.
Yayi murmushi sai kuma na taso Kika gane hakan ba gaskiya bane ko?
Wai meye tsakanin ka da yarinyar can da kullum baka tashi koya mata sai da marece Kuma ku biyu kawai?.
Yanzu dai gani. Ya fada Yana murmushi.....
Ta dalla mishi harara minti nawa ta baka ne?
Ni kamar baka cikin natsuwa ma wallahi. Baka daukar waya baka amsa gayyata idan ma an iske ka..... Ikon Allah mufeeda ki Bari zamuyi waya anjima Kinga Babu dadi......babu dadi ka barota kazo wurina?
Bai San lokacin da ya kyalkyace da dariya ba ......dai dai lokacin da Bilkisu ta dago Kai, kutumar bala'i....
Yana mamakin yanda yanmata ke tuhumar Shi akan Bilkisu.
Mikewa tayi ta hada litattafan sannan ta dauki ledar abincin kawai ta fito......
Ba karamin razana yayi ba don yasan kwanan zancen..... *Bilkisu*.......... *Bilkisu*.... *Bilkisu*!!!....... Amma Ina! Ko waige....
Duka yaushe ya samu suka daidaita, mtseww.
Please zamuyi waya ya fada tare da Dan rugawa *Bilkisu*.......
Sauri takeyi sosai, ya cimmata da kyar...Dan Allah kiyi hakuri.
KO kallonsa batayi ba.
Wallahi ban manta dake ba Ina cikin kwatanta mata naga kin fito......... Nace ka manta Dani ne? Ko kaji nace nayi fushi ne? Kaje ka gama da ita ni lokacin da kake free Zan dawo tunda nice nake nema a wurinka......kiyi hakuri Dan Allah.
Ta tsaya cak tare da kallonsa..... Banyi fushi ba, kamar yanda ba haushi naji ba, ai kana da damar ka ko?
Wannan bin da kakeyi mun Shi zai hasalani don haka ka koma ka kyaleni.......ya daga hannuwa sama, naji Amma kiban abincin Mana......wallahi bazaka ci Shi ba. Ta fada tare da wurga mishi kallon da yafi komai tsana sannan ta tafi tabar Shi tsaye.
Wai me yasa bazai kyale yarinyar nan ba?
Duk Yan mata na shakkar sa me yasa ita bata tsoron yi mishi gadara?
Ko ya ayyana zaiyi fushi da ita Shima me yasa baya iyawa?
Yaja wani dogon tsoki....... Ya wuce a fusace.