← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 68

Sashe 36

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

****************
*KADUNA RIGASA*
Ta fada bisa gado ta saki kuka..... Ya karaso Ummi tashi ya dagota.... Kiyi hakuri wallahi ba abinda kike tunani bane I just hugged her..... I don't want hear about it.
Naji but kiyi hakuri ya rungume ta, I was confused these days.
Tsakanin Miji da Mata sai Allah cikin second zancen ya sauya launi ya shawo kanta ....
Kuka sosai Amira keyi tana cewa tabbas na ma kaina wauta me yasa na bayyana Mata abinda yake so da Wanda baya so? Me yasa na sakar Mata ragama...
Tabbas ya shiga rudani ya kasa tantance daya cikin biyu... Ta Kara rushewa da kuka.
Yayi lamooo bisa cikinta, ita Kuma tana shafa kansa.... A hankali take magana.
Kafi son matarka Dani, har Yanzu ka kasa sabawa da ni matsayin matarka, a kullum...
Ya rufe mata baki da hannu, I'm sorry baby, Ina sonki musamman Yanzu da Kika dawo normal wife kina biyayya ga sharudda na sannan kina kula dani....
Me yasa kake saurin kamuwa Koda kuwa wani abun munyi shine saboda makircin mu na Mata?..
Yayi shiruuuu..... Ya kasa magana hakika ya gano inda zancen ta ya nufa, ta yi murmushi hakika Yana da kyau ka Zama jarumi Mai iko da bukatar sa.
Kiyi hakuri please I'll change..... Hmmm Allah yasa zaka iya.
Kuma Ina rokon ka Dan Allah idan kasan har Yanzu kana kokwanto akan son da kakeyi mun.... Ba wannan maganar Ummi ya fada tare da janyo ta jikinsa..... Wallahi Ina sonki fiye da yanda kike tunani sometimes Ina rasa meke damuna amma na gano bakin zaren na Miki alkawarin zakiga canji.
Please am sorry dear.
Ya Kara rungume ta........✍🏼

*Zainab wowo ce*💖🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣6⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.* ( Allah ya Kara tsareki daga sharrin munafukai Kuma azzalumai ).

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

************
*Federal University dutsinma*

......Ta rike kugu ta tsare shi da ido sannan ta ce *Who are you?*
Ya kyalkyace da dariya *Nine Anwar*..... Wallahi ka Fara bani tsoro ni ban yarda da Kai ba,kawai ta firgice mishi tana baya baya...... Tana neman Tara mishi jama'a ya Fara magana a hankali ```look calm down please I'll explain let's go```.......ba inda Zan bika sai kwallah sharrrr, duk jikinta ya tsinke da rawa.
Ya zaro ido yace ```this is serious```....... Yallabai an saka a mota.... Please zanyi magana bani minti biyu just go away...
Bilkisu please kizo muje Zan Miki bayani.... Wallahi bazan bika ba. Kai Bari na fada maka ni ban ma yarda da dakai ba......sai kuka.
Ya runtse ido yace ohh my God this girl nawaoooo.
Ya fiddo waya, ya Kira sadeeq.... Sadeeq please come to Abis super market now am there with Bilkisu... Ya latse wayar..... Kiyi shiru Dan Allah ke ba ki wuyar kuka what's wrong with you???
Ta mishi banza...
Ya sa hannu zai kamota tayi baya saura kadan ta fada cikin kwalayen lemuka.... Zaki Fadi fa ya daka Mata tsawa.
Ta makure wallahi kana tabani Zan maka ihu.
Ya kura mata ido kawai ya maida hannuwa ya rungume.
Yana hango sadeeq mashin ya ajiyeshi ya fita da sauri..... Please save me she's suspecting me...mtsew ya doka tsoki ya wuce Shi.
Tana tsaye ko motsi ta kasayi, sadeeq ya kalleta zo muje Bilkisu kinji.
Duk jikinta ya mutu ta biyo shi, ya bude Mata mota tana Zama shima ya shigo ya rufe kofa, Sadeeq ya shiga gaba suka tafi.
Bayan an sauke kayan kaf, sadeeq ya kalleta ya akayi ne Bilkisu me ya faru?
Kwallah suka zubo mata, Dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru menene ya faru? Idan Kuma kina da tamabaya akan Anwar kiyi mun Zan baki amsa wallahi...... Wanene Anwar?, Wallahi ni ban yarda dashi ba, duba ka gani ta nuna mishi tulin kayan da hannu wannan siyayyar hankali ce? Kuma naga dollars sun fado aljihun sa yace ajiyar ka ce he's always hiding something from me why?.…..
Kiyi hakuri...... Wallahi bazanyi hakuri ba yace mun Shi a kauyen Kano yake Yana business da wani ubangidan sa Kuma...... Karya yakeyi. Sadeeq ya katseta.
Ya kalleshi da sauri, me kake nufi?
Ina nufin gidan ku akwai kudi Kuma cikin garin Kano kake ba kauye ba. Ya kalleta what else do you want to know?........ Ya ingijeshi shikenan ka tafi tunda taji daga bakin ka Zan Mata bayanin saura.
Ya yi dariya, wannan rawar kafar da kakeyi Shi ke tona maka ASIRI..... I said go ya Kara tura shi.
Allah ba inda zanje.
Bilkisu karya yakeyi babba gida ya fito.
Ni meye nawa a ciki da yake boye mun? Ta fada tana hararar sa, ya yi murmushi hankalin ki ya kwanta Yanzu?
Ban sani ba ta juya...... Ya kamota, me yasa baki ganewa ne ke? Nace idan Ina Miki magana ki daina tafiya bazaki daina ba ko? Sai ranar dana kamaki gaban wadanda kike ji ma kunya Zaki.....Amma Kai iyakar Dan iska ka Kai.
Saketa wallahi.
Ya saketa Yana Yar dariya.
Kinga Bilkisu je kirawo kawayenki su shigar Miki da kayan Nan.....bazata dawo ba Kuma wallahi binta zanyi ciki Kama fada Mata.
Don't mind him jeki abinki.
Ya bita da ido.......
Zaka rikita Yar mutane Anwar wallahi ta tsora fa da gaske...... Ya kwashe da dariya kawai.
Asirin ka ya Fara tonuwa sai ka yi kokari Kuma Yanzu ka *FURTA* Mata.... Uwarka.... Yakai mishi duka.
Yarinyar can sadeeq rigimammiya ce Kuma shagwababbiya...... Komai sai ta bude Baki tana kuka.
A gaskiya ka takura mata..... Fitowar su yasa ya tsayar da maganar.
Ko kallonsu baiyi ba ya ce Bilkisu minti biyu..... Ya danyi gefe can nesa.
Tayi tsaye, sadeeq ya kalleta kije kada ya Kara Mata Mana lokaci I'll talk to him please.
Ta wuce kanta kasa, ta rasa inda zata sa ranta.
Ta tsaya nesa dashi,
Ya kalleta ki matso koni nazo Nan.... Ina jinka daga na...... Taku daya ta ganshi gabanta wallahi kina motsawa Ina kamaki, ya fada.
Tayi kasa da Kai.... *tawa ta sameni ni Bilkisu* tace a zuciya.
Ya kamata kiyi mun godiya ko?
Ko nayi laifi ne?
Hmmm, na gode Allah ya biya.
Good, yace Yana murmushi.
Ya kalli hannun sa *I really like this watch honestly*
Ta ce hmm, kawai.
Yanzu hankalin ki ya kwanta kin Kuma yarda dani tunda kinji na fito daga babban gida?
Um, ta ce a takaice.
Gobe ba lecture ko?
Ta ce um.
Sai dare kenan zamu hadu?..... Anwar Dan Allah ka rage zuwa wurina bana son abinda zaiyi affecting karatu na gaskiya.
Ya kura Mata ido yayi shiru.....har sai da ta dago ido ta kalleshi.
Ta mayar da Kai kasa.
Kamar zaice wani Abu sai Kuma ya fasa yace okay I'll try.
Ta ce na gode, sai da safe.....
Ya matsa baya kawai ya bata wuri ta wuce.
Ta Dan kalleshi kadan fuskar sa ta canza alamar damuwa.... Kirjinta ya buga da karfi.
Kamar tayi magana Kuma ta fasa ta wuce.
Sadeeq na tsaye su Aisha Kuma sun shiga da kayan, ta mishi sai da safe ta wuce....
Har ta shige idon sa na kanta ya kalli sadeeq shi Kuma ya banka mishi harara, wannan rawar kafar ita zata......I don't know how to control my self. Abun ya Fara damuna.
Wata muguwar dariya sadeeq ya saki tare da fadin *Anzo wurin.*
Murmushi kawai yayi.
Kana hauka ne kayi Mata irin wannan shopping din?
Mtsew wallahi Bilkisu da kake gani ta banbanta da ko wace irin mace class din yarinyar yayi yawa could you imagine she refused to take abinda takeso sai da taga da gaske Zan kwashe kayan shagon?.
Da sai ka bita a haka for once gaba gaba idan kun Kara sabawa sai ta dauka...... I don't think so.
Kuma wadannan banzayen dollars din ne suka rikitata cos har muka Kare she was shocked but couldn't..... Gaskiya ta firgita.
Ya kamata fa ka Kama kanka gaskiya wallahi kada ta birkice maka kuma ko ta tsorata tsoron yasa ta gujeka.
Mtseew.... I said I'll try. Ya fada Yana yarfa hannu.
And ka rage kakkamata fa..... Ba laifina bane wannan fa, sadeeq yarinyar nan fa baza ka gane ba. Wallahi sai muna tsaka da magana sai ta nemi guduwa I told her this is what will happen idan tayi she refused to listen....and I have no choice than.... This is not an excuse idiot. Ya katse Shi.
Ya kamata fa ka duba kada kazo ka kasa shawo kanta bayan ta rikice maka..... Mtsew naji Zan jaraba.
Yanzu ai hankalin ka ya kwanta ka fada Mata Ina da kudi..... Kuna da kudi dai ba kana dashi ba.
Bari kaji na fada maka a yanda kayi Mata Yanzu wannan kadai ce hanya da zata fisshe ka.
Kana tunanin Koda kudi nane da gaske kana iya wannan gabatar? Kayi abinda hankali zai dauka Mana. Amma Yanzu na fada maka Kuna da kudi komeye ta dauka zata ajiye.
A yanda ta firgita some muka fada Mata bayan wannan wallahi Koda ta yarda a fili a zuciyarta zata ci gaba da wasi wasi Kuma hakan zai haifar Mata da bincike akanka... Kayi tunani Mana.
Kuma fa hakane.
Yawwa.
Amma Yanzu kaga tasan Kai Dan masu kudi ne zaka iya komai shikenan.
Yayi ajiyar zuciya *I too much like you sadeeq*
Suka kyalkyace da dariya tare da tafawa......
Chapter 36 · 0% Book details