← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 68

Sashe 19

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zainab wowo ce dai😄✍🏼💖
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
0⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*Wallahi tallahi inajin dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty Rabi dayi Mata addu'a da masu yiwa mahaifina addu'a na gode Allah yabar kauna my fans my pride ana mugun tare irin sosai dinnan*💖🤝🏼.
*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda zaka ba kowa ba arziki irin nasu o'e ba daga mu sai 'ya'yanmu🙄 Wanda ya tsargu dashi nake*😏🤣🤣🤣🏃🏻‍♀

_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*

👉🏼 *Unex*💖( Babu kamar ki ).

*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon munafukai*😄

👉🏼 *AUREN FARI FANS*💕💕💕💕one love well.

*INA CIGIYAR MZ*🗣🗣🗣😄

***************
*KADUNA RIGASA*
Tabbas Ummi Taji uwar bari,
Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in kwatar ma kaina yanci. Mutane dake cewar duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.
Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba sai da nazo, Bata laifi, bata gundurar sa. Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don mallakarsa.
Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).
Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.
Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.
Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban iya ba.
Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa nayi abinda yake so. Idan Kuma na sameshi daki...........ohhhhh na fahimci zancen ki. Ta katseta tana Yar dariya.
Baya Miki korafin Baki da kula?
Wallahi yanayi Aunty.
Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.
Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare, ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kibar wurin.....ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.
Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda Shi mutum ne Mai tsananin son kula.
Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaaa Nan da Nan sai ya harzuka.......gabanta ya Fadi...tohhh wannan dalilin ke sawa kullum sai sunyi rigima?
Ikon Allah.
Ta yi shiru dai, taji Amira ta shiga ranta sosai ganin ba bakin ciki ba Jin zafi ta zauna tana Mata irin wannan bayani Mai tsada Wanda ta tabbatar idan ita ce bazatayi hakan ba.
Kunya ta kamata sai kawai ta sauko bisa kujera.....Dan Allah Aunty Amira kiyi hakuri abubuwan da nayi a baya wallahi hada zuga irin ta mutane Amma Yanzu na gane........Dan Allah tashi ki zauna ba komai. Shawarar da Zan baki shine ki kuji fitar da sirrin auren ki ga ko wanene wasu ba shawarar kwarai zasu Baki ba, ko meye kiyi keda mijinki ba Wanda yaji ya gani ko wace Kika gani gidan aurenta wallahi hakuri takeyi. Shi Aure 90% hakuri ke raya Shi sauran 10%din ne ilimi da soyayya. Saboda haka Dan Allah ki zauna mu fahimci juna tunda kaddara ta hada mu ba kanmu aka Fara ba iyayenmu da kakanni duk haka muka gansu Kuma zamansu lafiya ba don Babu kishi ba sai don hakuri da hangen nesa.
In shaa Allah Aunty Zan kiyaye Allah yayi Mana jagora..........
Tirkashi, competition zai tashi muje zuwa muga cikin Amarya da uwar gida wacece zata amshi first position????????
**************
*Federal University dutsinma*
Chapter 19 · 0% Book details