← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 68

Sashe 59

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Ni rasa kunya ka sa nake hawan Wagga?
Ya kyalkyace da dariya to ai ku Daman Mata da kyale kyale aka sanku duk neman da mukeyi suwa muke kaiwa kudin? Ko bakiji ance Mana *Bayin Mata muke?*
..... Nidai naji sauka ...kina korata?
A'a Ina dai son naje nayi tuwon ko?
Zaki zo ki daukon please?
Dan Allah Anwar kazo da kanka.... Ya bude motar fine... Zanzo bye take care ya shige .
Tayi Yar dariya kawai ta tafi.
Karfe takwas yazo shida sadeeq gidan falo biyu ne na farko da na can ciki, bai tsaya komai ba ya wuce ciki abinsa... Sadeeq Kuma ya zauna na farkon shida su Aisha.
Riga da skirt ne jikinta sun kamata, ta zumbula hijab ta wuce da abincin a tray.
Sai kace muna a gida, ji yanda ka dararrashe... Yayi murmushi kawai.
Ta zuba mishi komai ta mike.... Ina zakije?
Ke wace irin bagidajiya ce Yar kauye? Haka are serving Mai gida???
Ta galla mishi harara, ya ce, naji dai Amma zauna ki cire wannan hijab din..... Ta zaro ido to Bari na dauko kallabi ko gyale..... Ya ajiye chokali ya kalleta fuska daure.... Ina son ba daddy mamaki Amma da alama wannan gardamar taki zata janyo Miki.... Tayi saurin cire hijab din gashin ta ya warwaro bisa bayanta warrrrrr ya sauka....yabi gashin da kallon ya hadiye tuwo ba shiri Amma duk da Haka bai saki fuska ba....
Ta yi tsumu kunya ta baibayeta, musamman da ta lura Yana yawan kallon kirjinta. Kayan sun matseta duk ta takura.
Ba tare da ya kalleta ba ya ce ```Kinsan kina da kyau Bilkisu?```
Gabanta ya bada ras!
Jin tayi shiru yasa Shi kallon ta yace kinji??
Ta Kara yin shiru....wannan kalmar ta kinji idan ya fada tana Jin kamar ta gantsara mishi cizo....
Bazaki amsa ni ba?
Ya kafa Mata ido, ta danyi murmushi tana Kara sunne kanta sai murza hannu takeyi kamar Mai yin alwala....
Yayi murmushi,kina da kyau Bilkisu Ina son structure dinki ... Tsikar jikinta ta bada wani Yarrrr.....
Ya ajiye chokali tuwon yamun dadi akwai Wanda zakiyi mun dumame da safe?
Um, ta ce a hankali.
Amma kamar generator dinku bashi da karfi ko? Naji AC din Bata tafiya da kyau ko kuwa fault din nata ne?
Huh?? Ya ce Yana kallonta...
Kila, ta fada ahankali... Wai kin takura ne?
A'a ta fada tana sunne Kai.
Bana son wannan ruwan daukon wasu marassa sanyi a can...ya nuna karamin fridge... Ta Mike ya bita da kallo, Koda ta juyo yayi saurin kawar da Kai kamar Yana latsa waya..... Ta mika mishi ya hada da hannun da ruwan ya fizgota , ta fada jikin sa zata kurma ihu ya toshe Mata Baki..... Kina ihu su sadeeq zasuce ga Bilkisu can ana harka...ya fada Yana Yar dariya.
Ta runtse ido jikinta ya Fara kyarma.... Dan Allah kayi hakuri..... Wayyo na shiga uku...
Wannan kunyar taki ke tunzurani kinki sakin jiki dani..... Dan Allah Zan saki sakeni ka gani.... Ya zagayo da hannayen sa ta gaba ya harde su daidai kirjinta ya soko kansa ta wuyanta Yana Mata Rada..... Ke nifa ba dutse bane ko katako.... Ta runtse ido wayyo na shiga uku Dan girman Allah ka sakeni.
Zan sakeki Amma wallahi Kika motsa kinji na rantse yau ba me kwatarki.... Naji Zan tsaya please na tuba. .... Ya cire hannuwansa ... Ta saki ajiyar zuciya kanta kasa sai kyarma takeyi duk ta tsorata....
Kyarmar ta mecece ya riko hannunta..... Dan Allah kayi hakuri..ta fada kamar zatayi kuka.... Ya Kara rungumota Dan Allah ki jira....Anwar kace zaka ba daddy mamaki fa.... Eh na sani. Ya fada kasa kasa .
Dan Allah ka sakeni.... Ke wallahi bazan iya ba, Dole na ringa taba ki don ki Saba kunyar Nan tayi yawa....ke Yanzu na say Miki ido kawai ba Dan romance ai Kya ce bani lafiya...... Wayyo ni Bilkisu na shiga uku...ta fada a hargitse .
Ya shafa gashinta.... Ina son gashinki .... Jikin ta ya bada tsammmmm....ta runtse ido.
Dan Allah kizo muje gidana ki kwana.... Sai kawai ta rushe da kuka.... Ke wasa nakeyi yi shiru.... Ya saketa Yana dariya... Jikinta sai kyarma yakeyi.... Ta goge hawayen ya bita da ido.... Haka kike da tsoro?
Ta hada Kai da guywa kawai....
Ya Mike shikenan tashi ki saka hijab muje ki rakani ...ya dauko hijab din a hannunsa.
Ta Mike .... Wallahi ko kiyi shiru ko na tafi da ke ... Tayi saurin goge kwallan, yayi murmushi matso na Sanya Miki hijab din... Ta matsa ya rungumota..... Dan Allah ki Dan ban minti biyu .... Ta sunne jikinsa ta Kara sakin kuka.... Ya buga tsoki... Kedai wallahi akwai ruwa ruwa...
Aure Dadi gareshi ki kwantar da hankalin ki mu.... Ta Kara sunne Kai ..ya kyalkyace da dariya to sakeni shikenan ba abinda zamuyi.
Ya saketa a hankali, Ya koma ya zauna bisa kujera ya zuki iska ya fesar tare da fadin ohhh my God.
Tayi tsaye har lokacin Bata daina kyarma ba ya fizgota ta fada jikinsa Yana fadin idan Baki saki jiki ba Allah yau sai dai mu kwana anan.... Ta sunne jikinsa, kokarin dagota yakeyi taki yarda.... Yayi dariya to ki daga ni na tashi ko?
Ta kasa dagowa.....wallahi Zan birkitar dake... Ta Mike da sauri ya riko hannunta tare da mikewa ya janyo bayanta ya kwanto samanta kansa bisa kafadar ta Yana magana cikin Rada Rada.... Bilkisu Ina Jin tsoro fa Anya Zan iya ba daddy mamaki wallahi duk kin rikitani.... Nidai Dan Allah kayi hakuri Anwar na tuba..... To ki jiyo in Baki kiss...... Ta zame ta zukunna tare da kankame jikinta tana fadin wayyo.... Ya Dan zukunna shima.... Wallahi kiss kawai zanyi please....nidai Dan Allah ka rufa man asiri....
Yayi Yar dariya okay naji tashi na tambayeki... Ta Mike da sauri ya matso ta matsa baya... Ya kalleta ya da matsawa?
Ta zumburo baki kayi tambayar inaji.... Ya nufota ta ringa baya baya... Bata Ankara ba taji ta daki bango ta kankame jikinta.... Ya tsaya gabanta ya harde hannuwa ya goya su a kirji tare da kura Mata ido duk sun kankance.....
An taba kissing dinki?
Jikinta ya bata tsammm..... Kinji? Ya fada.
Bazakiyi magana ba?
Wallahi ban taba ba..... Hada wallahi?
Wallahi tallahi ta fada kamar zatayi kuka...
Kina so kiji yanda akeyi?
A'a Dan Allah kayi hakuri.. .... Me yasa bakya so?
Tsikar jikinta ta Kara bada Yarrrr.....kinji?
Hakanan...
Ya sunkuyo daidai fuskarta tare da dafe bangon da hannu yace ki shirya anytime from now Zaki ji yanda akeyi.
Ya tallabota yasa Mata hijab ya figi hannunta suka fito....
Sadeeq shida Aisha kadai a Falon Maryam tayi ciki abinta..... Ta kalleshi idan ka Gama muna waje.....
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta sanyata jikin mota ya matso kusa da ita sosai kamar zasu hada jiki ya Fara Mata magana a hankali.... Ina so ki sani ni ba katako bane,in shaa Allah bazan kasa ba daddy mamaki ba Amma da sharadin sai kin daina wannan kunyar kin sakemun jikinki..... Ta runtse ido ya sunkuya Yana lekenta..... Wannan kunyar taki wallahi tana Sanya mun sha'awar ki Bilkisu tabbas idan Baki saki jiki Dani ba to I have no choice but to sleep with you..... Ta juya ta kife Kai ga mota *na shiga uku ni Bilkisu*..... Ya juyo da ita, matsalar bani da kunya ko a gaban waye Zan iya taba ki don haka kina da aiki ja don duk ranar da na bukaci taba ki Kika Hana kamar yau to ki sani Zan...... Anwar please.... Ta fada tare da runtse ido. Ya kyalkyace da dariya... Sadeeq ne ya fito Shi kadai ba Aisha .... Ya kallesu to pigeon muje ko?
..... Sadeeq yarinyar nan ta fiye kunya fa tana takurani da yawa...
Tayi sukutiiiii, Sade yayi murmushi Bilkisu ya da kunyar miji Kuma?
Ya zagaya ya shige mota.....Yana fadin kasan baka Gama ba ka fiddoni..?
Ya kalleta sadeeq bai gaji ba ko mu koma?.... A'a kuje Dan Allah...ya Kyalkyace da dariya matsoraciya kizo mun da dumamen school gobe zanci a mota kinji ko?
Ta Dan saki ajiyar zuciya ta ce toh.
Ya langwabar da Kai Bilkisu bana son tafiya wallahi.... Ta ce ya Salam! Amma a zuci...
Zan say kawo Miki irin pad din kamfanina kiyi amfani da ita ance tana da kyau sosai idan Bata Miki ba Kinga Dole a canza sabuwa..

Ta mishi banza.
Yayi murmushi kinji?
Um, ta ce.
Ko Zaki bini..

Ta ingijeshi ta kwala. da gudu ya tuntsure da dariya ya fada mota...... Sadeeq anya Zan iya zuba ma yarinyar can ido?
Ka rufa Mata asiri Dan Allah... Ya fada Yana Yar dariya.
Amma fa tana da tarbiyya sosai could you imagine ta tsorata simply don na yi hugging dinta?
.....wallahi Anwar Bilkisu na bani mamaki ta fita daban daga cikin Mata maganar gaskiya wannan lokacin kafin ka sami yarinya Mai kamun Kai irin ta Yana da wahala kasan abinda ke bani mamaki?
Ya girgiza Kai..
Yanda she's fully hijabite wallahi kaga fa tun zuwan ta school din nan Bata taba Sanya gyale ba Bata shigar banza ga addini sallah Bata wuce ta cikin jam'i naji ana rade radin ita za a ba Amira....
Ya danyi murmushi, wallahi har tausayi ta bani Yanzu duk jikinta ya tsinke da rawa sadeeq ta tsorata da nace zanyi kissing din ta wallahi hada kuka....
Ya kyalkyace da dariya ya ce baiwar Allah.
Sai ka lallaba ta ka Kara daurewa kada ka janyo ma kanka jangwam ta rikice maka Kuma...... Naga alama fa akwai rikici .
Kasan Aisha ta nuna tana da interest akaina?
Ya kalleshi haba???
Ya Dan Bata rai, no Bata mun ba, Ina son mace mai Jan aji nafi so na Sami mace wacce Ni ke binta tana ban wahala ba ita ce zata ringa zakewa ba..... Kamar Bilkisu kenan? Ya katseshi Yana dariya... Yayi murmushi Anya Zan Sami kamar ta at least ma ko wacce bata kaita ba.. da tana da kanwa ko Yar shekara biyar ce Allah da Zan jira..

Suka kyalkyace da dariya.
Chapter 59 · 0% Book details