← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 68

Sashe 3

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Federal University dutsinma* Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Bilkisu bata Sami sakewa ba, karatun Yana mata mugun wahala, ahankali take bin su chinyere suna nuna mata abubuwa duk Wanda ta fahimci Yana da kokari zataje don Kara fahimtar abinda ya shige mata. Su Anwar sune Yan baya ga komai, ya biye wa mashiririta yaki nuna ma kowa Shi din Mai kokari ne, masu karyar suna da kokari sai ya kwantar da kanshi Yana Jin yanda suke kwabar bayani musamman idan akazo gun lissafi. Hankalin sa a kwance duk C.A din da akayi shine overall, Yana amsa sunan Anwar a zahiri ba Wanda yasan Shi da Hamza Yusuf a badini. Fahimtar halin Bilkisu na rashin girman Kai yasa Shi suke gaisawa da ita sama-sama Yana son kulla mu'amula da ita Amma Yana ganin hakan a gareshi zai zubda mishi aji. Ita kuwa a gareta Sam bai ma gabanta ko kadan idan an hadu a gaisa idan ba a hadu ba Bata ko tunanin sa. Shine ma sau da yawa take Dan takura tunanin sa kadan kadan. Ta Dan Fara sakewa da su chinyere saboda ta lura sune masu kokarin ajin, takan zauna tayi tunanin akwai department din da yakai Economics barin wuta duk makarantar? Sau da yawa tana tunanin Anya ba hausa ko Islamic zata koma ba? Ta gama tsorata da makarantar musamman yanda taji ana bada carry over, probation da Kuma withdraw. Takan yi tunanin ai ita abun kunya ne gareta ta sami Koda carry over din ne ma hakan yasa ta Kara dagewa tana Kara naci cikin karatun ta musamman da jarabawa ta karato kullum tana library ko Kuma tare da su chinyere tana Kara koyon karatu. Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class tana faman karatu yazo wucewa kunnensa like da air piece har ya gitta said yaga kamar ita, yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko gizo idanun sa keyi Masa kamar kullum? Kamar kada ya dawo sai Kuma dai ya koma don tabbatarwa .....ita din daice tana ta faman Mimi da baki ya kyalkyace da dariya lokacin daya kunna Kai ajin hankalinta naga littafi har yazo ya zauna kusa da ita....tayi firgigi cike da tsoro ko da taga shine bata San lokacin da ta balla mishi harara ba.....yayi murmushi afuwan matsoraciya duk wadannan mutanen meye zai kamaki da rana gatse gatse haka? Ya karasa maganar Yana janyo littafin ta gaban sa, meye kike karantawa ayi mun bayani. Haushi ya turnuketa domin karatun ya Fara shigar ta sosai gashi yazo zai rikita ta, Tasha mur tare da janyo littafin Dan Allah karatu nake zaka rikitani ka tashi ka bani wuri.....bazaki koya mun ba? Nima Yanzu ai nake karantawa ta fada cikin fada fada, yayi murmushi it's alright go ahead and read ya sunkuyar dakai kawai bisa desk din. Ta ci gaba da karatun ta ba tare da ta Kara bi ta kansa ba. Idan ta karanta sai that bude can karshen littafin ta rubuta haka haka Yana ta lura da ita duk ta dage bakin Rai bakin fama Nan da nan ya gane hadda ce takeyi. Yana so ya mata bayani Amma ya rasa ta inda zai Fara...... Tana son kamshin turaren sa ainun Anwar Dan gayu ne matuka Yana daukar wanka gashi kyakkyawa. Kamar ta karanci zuciyar say ta Dan karkato Dan Alalh wannan kalmar me take nufi? Ta sungo mishi littafin a gaban sa. Daman tun zaman sa kusa da ita ya kashe music din hakanan wayar ke jikin kunnen sa.........yayi kamar baiji me tace ba har sai da ta kalleshi sannan ya Dan zare wayar daga kunne Shi ala dole baiji me tace ba ya dan kalleta Shima kina magana ne? Cewa nayi me wannan kalmar ke nufi? Ta nuna mishi da yatsa ....yabi hannun nata da kallo Yana kallon Zara zaran yatsun ta ya ce bari muji sentence din, Ya fada mata ma'anar kafin yace kin gane course din nan ne? Ta Dan bata rai to gashi dai Ina karantawa...... Ya Kara janyo littafin gaban sa ya budo shafin farko...... Kin San fa abun duk labari ne Kinga.......ya Fara mata bayani a hankali ahankali Nan da nan ta Fara fahimta sosai saboda bayanin nasa duk da hausa yake mata. Haka haka har ya gama mata littafin. Taji dadi sosai da sosai ta fadada fara'ar ta ohhhhh Ashe ka Gama covering komai ko???.......a'a fa nima kawai na gane darasin ne lokacin da yake bayani a class.....Amma wallahi ka iya bayani saboda har kafi malamin ma iyawa....ya danyi dariya tinda na Miki bayani da hausa ko? Ta kyalkyace da dariya yabi fuskar ta ta Yana Kara kallo ta bude jakar ta to Dan Allah ka gane wannan math din? Ta fiddo littafin. Dariya kawai yake cikin Rai Amma a zahiri yadan basar.......ya kalli littafin, gaskiya ban iya Shi ba Amma ki bari yau sanje dakin wani dan aji hudu ya koya mun gobe sai mu hadu in nuna Miki......da karfe nawa? Ta katse shi, Yayi murmushi duk lokacin da kike so goben....... 8:00am Zan jiraka anan. Ya zaro ido 8? Gaskiya sai dai 4 saboda barci bazai barni na fito da wuri ba. Kamar zatayi magana sai Kuma ta fasa ta ce Allah ya kaimu lafiya tare da janye littafin yabi Dan karamin bakin ta da kallo har ta sunkuya. Ta Mike tana kokarin sagala jaka ta kalleshi tana murmushi Dan Allah ka koya da kyau Zan jiraka anan din goben in shaa Allah. Yace ba damuwa.....see you then. Ta wuce. Yabi ta da kallo kamar ya rufa mata baya amma Shi kansa yasan bazai iya hakan ba ( saboda gadara ). Zuciyarta Fara fes! Ta isa daki taji dadin bayanin Anwar matuka. Washe gari tana fitowa masallaci ta wuce class din kamar yanda sukayi alkawari, ta fiddo wani course theory ta Fara karantawa kafin ya iso. Ta nayi tana Dan kallon taga tare da duba agogon wayarta har kusan hudu da arba'in. *Anwar* kuwa Yana can Yana shakar barci abinsa sammm ya manta da maganar su. Allah ya taimaketa kawai sai ga su chinyere sun shigo karatu Suma Kuma cikin sa'a statistics din zasuyi solving sai kawai tayi joining suka Fara. Tana yi tana tunanin watakila Anwar bai iya bane Yana Jin kunyar zuwa....ta tabe baki to meye na karyar zaije ya koya bayan yasan bashi da wani kokari....mtsew taja guntun tsoki. Bai farka ba sai shidda saura ya tashi a hargitse ga takaicin lokacin sallah ya shige ga Kuma tunanin sabawa Bilkisu alkawari da yayi. A gurguje ya watsa ruwa yayi sallah ya fito da sauri. Ya shawo kwana ita Kuma ta fito ajin zata tafi. Tana hango Shi tayi sauri bi ta dayan side din tabayan azuzuwa tayi hanyar fita gate sauri sauri.....tana tunanin watakila Yana can Yana faman koyo don yazo ya birgeta..tayi tsoki to karya tame ne? A hargitse ya shiga ajin sai wurge wurgen ido yakeyi girman Kai da nuna Isa sun Hana ya tambayi su chinyere ko sun ganta. Rai bace ya fita Nan ya Fara bin azuzuwa neman ta. Helen ta tabe baki I don't like this Anwar honestly.... Mtsew don't mind idiot abeg inji chinyere Nan gulma ta tashi. Ya cika girman Kai da nuna Shi wani ne, baya yi ma kowa magana sai abokansa uku. Surutai kala kala saboda Shi din Daman baida farin jini a class din tun zuwansu Wai ya cika fadin Rai da gadara. Tunda ga ranar bai Kara Sanya Bilkisu a ido ba yayi neman har ya gaji gashi baida no. Ta bai Kuma San Wanda zai tambaya ya bashi ba haka Kuma baisan accommodation dinta ba hostel take ko off campus. Wasa wasa abun ya Dan dameshi. Ranar da zasu Fara jarabawa da yake ta karfe uku ce tun biyu saura yake hall din Yana so ya ganta, ita kuwa tun 8 tana library sai biyu da Rabi ta fito bayan tayo sallah. Kansa sunkuye baiga shigowar taba har ta zauna bayansa. Lallai Anwar ka kyauta shine ka shanya ni rannan ko? To kayi dai dai ta fada tana faman hararar sa . Da sauri ya dago Kai zaiyi magana kenan invigilators suka shigo tare da fadin everybody out..ta rigashi fita, ko da aka Fara shiga ma tayi saurin fadawa don Zama gaba gaba. Alhamdulillah jarabawar ta mata dadi ainun domin duk abinda ta karanta suka fito. Ita ce ta biyar din bayarwa ( submitting ) bata jira kowa ba tayi masallaci don gabatar da la'asar saboda lokacin biyar da kusan ashirin. G Haka semester din ta kare ba tare da sun Kara haduwa da Anwar ba, ko kadan Bata yarda su hadu tasan karya zai shirga mata don kare kansa. Shi Dan garin Kano ne ita Kuma Abuja mahaifinta ke aiki Amma asalin su Yan katsina ne. Washegarin da suka Gama jarabawa tabar garin Anwar kuwa karfe biyar na ranar yabar dutsinma. Hutun baida tsawo sati biyu akayi aka dawo. Sun dawo da sati daya aka saki result a *portal* Murna tsalle ga Bilkisu saboda ta cinye ko wane Bata da carry over ko daya ga point dinta 4.33 Hakan ba karamin dadi yayiwa Yan gidan su da iyayenta ba. Anwar kuwa 5:00 dai dai ya samu saboda duka courses din da sukayi goma Sha daya ko wane *A* yaci. Yaja bakin sa ya tsuke. A cikin ajin kowa nata fadin result din sa daga Mai 4 point sai masu 3 point da abubuwa. Duk Wanda ya tambayi Bilkisu sai ta ce lafiya Lau ne ni Daman carry over ke bani so to ban samu ba. Bata yarda ta fada ma kowa result dinta ba. Tana zaune an gama lecture din wani mugun malami ta kura ma dan rubutun da tayi ido tana nazarin ya zata ci jarabawa da Dan wannan rubutun? Suleiman ya mata sallama. Suleiman matashi ne Shima a cikin ajin Mai natsuwa da son addini babancin say da Anwar yafi Anwar saukin Kai da yarinta. Ya zauna kusa da ita bayan ta amsa sallamar Dan Allah Hajiya Bilkisu na kasa bude portal dina ya akeyi ne? Tayi murmushi Ina wayar taka in nuna maka? Wallahi daki na barta ki nuna mun da taki.......hankalin Anwar na kansu haka kawai sai yaji ya tsani Suleiman karon farko
Chapter 3 · 0% Book details