← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 68

Sashe 38

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai na sameka class....fine, gobe mu hadu new lecture rooms by four. Yana fadin haka ya kashe wayar.
Ta bi wayar da kallo tace ikon Allah..... Allah ya kawoni ni Bilkisu.....
Tayi shiri daga sallar la'sar, a hankali take tafiya ga nisa daga masallaci zuwa classes din, kanta a kasa kadan kadan take gaisawa da mutane.
Kugin mashin taji a bayanta tayi saurin Kara matsawa gefen titi, gabanta suka tsaya, ya sauko sanye da kananan Kaya kamar kullum ya rufe ido da facing cap... Ajiye ni a nan.
Ta dago ido da saurin Jin maganar sa. Shida sadeeq ne bisa sabon mashin fari duk leda jikinsa.
Sadeeq Ina wuni ta fada tana murmushi.
Lafiya Lau Bilkisu.
Ta Dan kalli gefen sa Ina wuni.
Yayi kamar baiji ba, ta ce ai kaji tsiyar Shi dizgi wurinsa bai daukeshi bakin komai ba.
Ka kawo man upstairs Yanzu please ya fada Yana kallon sa ya juya da mashin din Shi Kuma ya jera da ita suka ci gaba da tafiya bai ce komai ba,
Ina gaishe ka amma kayi shiru.
Ya dago ido cikin facing cap kince sadeeq Ina wuni Ni Kuma kin wani ce Ina wuni sunan nawa Yana Miki wahalar fada ne?
Murmushi tayi kaii ikon Allah Wai haushi kaji?
Anwar Ina wuni?
Sunana Hamza.... A'a Nan Kuma daya fa. Sunan da kowa ke kiranka Zan ambata sai dai idan kana neman magana ne sai inji.
Shiru kawai yayi Mata.
Tayi Yar dariya yau gadara ake ji, ta fada cikin zuci tana satar kallon sa Yana ta faman Shan kamshi Yana Bata rai.
Maganar meye zamuyi kace mu hadu yau?
Kina sauri ne?
Tayi dariya ohh ni Bilkisu halan bani da ikon tambaya.
Murmushi kawai yayi ta gefen kunci.
Suka shiga class din ba kowa sai mutum daya shima da alama chargy yakeyi, kasancewa farkon semester ne.
Ta toge bakin sit....ya kalleta wuce ciki ko ni Zaki saka cikin kujera?
Ka zauna ni Bari....... Ya ingizata da karfi tayi ciki ya bita dole ta matsa da sauri kada ya Kara kamata...... Kina da gardama, na fada Miki idan Baki son Ina kamaki ko taba ki kada kiyi mun gardama amma da alama kina da kunnen Kashi...... Ya karasa maganar Yana Zama kujerar kusa da ita.
Da sai ka bada tazarar kujera daya tunda magana ce zamuyi ba karatu ba...... Bazanyi hakan ba.
Tayi shiru tare da sunkuyar da Kai tana wasa da yatsun hannunta.
Yasu daddy?
Lafiya lau, dazun munyi waya yace mun zasu tafi Paris da mommy.
Haba?
Allah.
Yayi murmushi *Yan gayu*.
Ta Dan harareshi.
Dafatan baki sanar da kawayenki abinda ya faru jiya ba, kin San bana son yawan surutu ne yasa bana nuna ni din wanine.....
Aisha ce Kuma ta rigani sani... Tasan meye?
Kuna da kudi?
Kice wallahi.... Tayi murmushi Allah kuwa, ta bashi labarin yanda sukayi.
Ya danyi tsoki, kawai don Ina sa Kaya masu kyau Shi zai nuna muna da kudi? She's not well.
Eh din. An dai gano ka.
Ya danyi dariya kawai.
Wace magana zamuyi kace nazo?
Ba gashi munayi ba?
Ko wata ta daban kike so muyi?...... Tsayuwar mashin din sadeeq yasa maganar da zatayi ta koma.
Ya dora Kai bisa table ta bi bayanshi da kallo.
Ko baka lafiya ne yau? Naga duk kayi sukuku Anwar..... Sadeeq ya shigo ya ajiye ledoji bisa table din gashi nan Zan je na karbo sako isah kaita idan ka gama ka kirani.
Bai dago Kai ba Yana duke ya rufe ido kawai.
Tayi shiruuuuu tana kallonsa...
Anwar..... Ta kirashi a hankali.
Ya dago Kai ya akayi?
Baka lafiya ne?
Ya yamutsa fuska yunwa nake ji ..... To ba gashi nan sadeeq ya kawo maka ba Kuma kana Jin sa Anwar kamar karamin yaro kayi shiru.
Fiddo ki ban ya fada tare da kokawa ya kife..... Bata San lokacin da tayi dariya ba ta Mike tare da saka hannu ta janyo ledar sai gogar jikinsa takeyi yaki Kuma gyarawa.
Ta fiddo hollandia biyu milk and strawberry, tashi gashi ta fada tare da fiddo wata leda, katuwar gasassar kaza ce taji cabbage da kayan miya nade a foil paper.
Ta bude ikon Allah dadi za'aci Alhaji Anwar..... Ya dago Yana Yar dariya keni wallahi tuwo nake son ci miyar kuka..... Ta kalleshi ka iya tukawa ko?.
Yayi murmushi Allah da gaske nake Ina son cin tuwo Bilkisu ya langabe Kai.
To ka je ka siyo Mana.
Ke zakiyi mun. Zan siyo semo kiyi mun anjima...... Kam wallahi kada kasa ma ranka abinda bazaka samu ba. Zan samu yau sai naci tuwo Kuma ke zakiyi mun.
Ya bude kazar ya cire wurin cinya ya Fara ci.
Tayi shiru kawai.
Wane kike so milk din ko strawberry?
Kai wane zaka sha?
Bani da choice as long as nidai cikina zai cika..... Ta yi dariya kawai ta dauko milk din ta Fara Sha a hankali.
Zakici kazar ko kunya kike ji?
Ta Kara Yar dariya, na ci abinci na koshi.
Me Kika ci?
Taliya muka dafa.
Zaki mun tuwon?
Zan maka Amma ka Bari sai gobe yau dai marece yayi sosai.
In siyo semo din?
Ina dashi Kar ka damu.
Good.
Ba za kici ba da gaske?
Allah na koshi....... Zan baking baki matukar Baki sa hannu kinci ba..... Rage mun idan naje daki zanci da dare.
Mtsew, Allah ya raba ki da gardama.
Yaci gaba da cin abinsa.
Mamaki kawai takeyi Wai me yasa maza Basu da kunya ?
Kamar ya karanci zuciyar ta ya kalleta...... Ni banjin kunyar ki.
Ta danyi dariya ....yabi kuncinta da kallo....
Kin San cewa kina da kyau kuwa?....... Ta kalleshi da kyau me kace?
Yayi murmushi kina son in maimaita abinda Kika Riga kinji?
Hmm, tace.
Samarin ki nawa?
Zaka Fara ko?
Ana zaman lafiya ka Fara tamabayoyi marassa amfani kuma azo ayi fada ko?
Ba Kya so na sani ne?
Ina ruwanka da samari na an fada maka irin ka ce da kowace jik and jak ...... Ya sa hannu ya buge Mata Baki...... Kai Kai Kai ta rike Baki.... Sai tayi kwal kwal zatayi kuka.
Ya harareta wallahi yau kikayi mun kuka Zan baki mamaki ke baki da aiki sai shagwaba.?
Gaskiya bana son abinda kakeyi mun Anwar..... Gaskiya bana son abinda kake yi mun Anwar ya maimaita Yana kwaikwayonta.
Karfe nawa Zan zo na karbi tuwo gobe.... Zan Aiko maka Dan Allah ba sai kazo ba ko ka turo sadeeq ya karba.... Wani kallo ya jefe ta dashi kafin yace *why are you pushing me away?*
Ba haka bane...... Haka ne.
Bazan zo ba, ki Aiko mun ya Miki ko?
Tayi murmushi eh,
Duk ya kware tsokokin kazar ya tura Mata kasusuwa ga naki..... Ta danyi dariya wallahi kana da ci Anwar...... Ya yunkura zai Kara buge bakin ta tayi baya tana dariya.
Tashi muje kada six tayi na gaji tunda ka gama.
Ki shanye tukun.
Tabbb bazan ya ba.
Shi yasa ba Kya kiba.
Hmm, kawai tace.
Wayarsa tayi Kara Yana dubawa ya Mike please Ina zuwa...... Ta mishi wani kallo ya nuna Mata fuskar wayar Alhaji Abbas ne kin gani?... Ya fice Yana dariya kunya ta Dan Kama ta ganin zai fassara ta.
Ya Dan dade kafin ya dawo tana ta latsa waya taji yayi fit da ita.......
Bani naga suwaye samarinki.......Aka Kara kiransa a waya.
Ya kalla sai kawai yayi tsoki, sai ka bar nan ka kirata ne?...... Sai bani kawai yayi picking yasa handsfree.....
Ya akayi?
Haka ma zaka ce?
Baki bani amsa ba nace ya akayi ne?
Jiya an Kai maka abinci ka dawo dashi, tun jiyan nake kiranka kaki dauka Wai me yasa..... Nace kiyi mun abinci?
Sai kace sannan zaka ci?
Ke idan Baki da abin fada Ina da abinyi ya kashe wayar.
Ya kalleta kin yarda Yanzu ita ce ke damuna bani nake binta ba?.
Kai ji Ni me nace toh?
Sai kince? Rigimar ki ai nasan ta.
Wannan semester din na ganki da wani Kato wallahi sai naci ...... Maganar ta makale ta zaro ido ya Mike da sauri tashi muje na rakaki.
Ka karasa abinda kake son fada?
Yayi murmushi kawai,
Ya daure fuska ta mike ka Isa ka hanani gaisawa da mutanen arziki na?
A matsayin a na wa to da zaka Sanya mun irin wannan dokar?
Ke ya Isa tunda nayi shiru kuma Dan Allah ki kyaleni.
Suka jera suna tafiya.
Suna karyo wata kwana su mufeeda na tahowa ta tsaya gaban sa kutumar uba Wai kana cikin school din Nan............???????✍🏼

*Zainab wowo* 💖💖

Zan kawo muku wani true life story anjima Dan Allah Ina bukatar comments din ku please. Na gode masoyana Ina kaunarku🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣7⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

***************
*KADUNA RIGASA*
Duk ina son ganin ku falona da karfe takwas...
Ya tura ma kowace sako.
Duk sun you zugum suna mamakin wannan Kira , abinda bai taba ba.
Ya rage karar TV.
Agurguje ba lokaci maganar zata dauka ba, da farko Ina godiya da Jin dadin yanda ko wace ke kokarin faranta mun da Kuma dagewa wurin kyautatawa, hakika naga canji a gidan Nan. Allah ya saka ma ko wace da mafificin alkhairi.
Magana ta karshe doka ce Zan saka na neman shawara ko neman izini ba.
Daga yau na Hana ko wace ziyarar dakina matukar ba ita ce da girki ba. Sannan daga yau kada wacce ta Kara bina ko ta shiga sashen dayar ku matukar Ina ciki.
Wannan shine.
Ummi kina iya tashi ki tafi sai da safe...... Ya Mike yayi ciki.

***************
*Federal University dutsinma*
Chapter 38 · 0% Book details