Sashe 2
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
Amira kiyi hakuri wannan auren da zanyi ki daukeshi amatsayin kaddara wallahi wallahi bazan taba wulakanta ki ba don girman Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan......baban Ahmad Dan Allah ka fita ka bani wuri wallahi ko ganin ka bana sonyi na tsaneka da dukkan wannan rayuwar.....ya zukunna na tuba na rantse Miki da Allah ba zanyi auren nan don in wulakanta ki ba mu daukeshi matsayin kaddara Amira kiyi hakuri nasan ban kyauta Miki ba, ta Mike tsaye yaudarar maza wacece ban sani ba? Haka kuke cewa Amma wallahi ka zalunceni ka cuceni kaci amanar kauna.....kada kice haka na rantse da Allah har gobe Ina kaunar ki.....karya kakeyi baka kaunata da baka ga wata har ta birgeka kake kokarin kawo ta gidan nan ba. Shima mikewar yayi bacin Rai zaisa ki Fadi haka Amma Ni nasan wallahi ba haka bane Amira kiyi hakuri laifi ne na riga nayi na tuba Dan Allah kiyi hakuri.....mtsew ta wuce nabar maka dakin tunda Kai bazaka tafi ba. Tabar Shi Nan tsaye.
Ya dafe Kai kwalla suka zubo mishi Shi kansa yasan Yana kaunar Amira Kuma baida niyyar Kara aure, matsalar kanwar abokin sa ce yasan kaunar da yarinyar keyi mishi tun Yana saurayi da farko Yana ba yarinyar fuska ba tare da Yana tunanin zata iya like mishi haka ba, kowa yasan suna tare Yanzu idan yace bazai aure ta ba kamar yanda abokin nasa ya bukata lallai zasu Bata.
Ya zauna bisa gefen gado ya dafe Kai dole in lallaba Amira har ta sauko tabbas bazan yi auren Nan ba matukar Bata cikin kwanciyar hankali.
Ya kwashe kusan kwana biyar Yana faman lallashi kafin ya shawo kanta hakan yasa Shima ya Sami sukuni da kwanciyar hankali. Nan da Nan suka Fara hidimar aure shida ita . Ya dauketa suka tafi Kano hado lefe, ya zauna gefe yace to ki Fara zabar lesuka , tayi jimmmmm kamar zata ce dauko mun Yan dubu uku da dari biyar sai Kuma wata zuciyar ta kwabe ta da cewar kisa tsoron Allah ga wannan lamarin bazaki taba tozarta da wulakanta ba.
Ta Fara ma lesussukan kallo tana tambayar farashi har aka kawo na karshen masu kudin daga dari suka Fara, ta ce nawa za a Sanya ne? Yace yanda duk kike ganin ya Isa ni Dan kallo ne, ta dunga darzo manya manyan lesussuka tana warewa idan ta dauki red Shi sai ya dauki pink ko maroon, haka sukayi tayi har aka Gama da suturu aka koma kayan shafa da kalmomi.
Sun kashe kudi yafi miliyan uku sannan suka je gurun jakun Kuna da akwattai nan ma aka darje kusan set takwas ta daukar ma Amarya pink shi Kuma ya dauki sky blue.
Bata kawo komai cikin ranta ba, tana ta addu'o'i na Kara karfin guiywa kamar yanda mahaifiyarta ta Bata shawara.
Ita dashi aka Kai lefe, gidansu yayi wa Amarya sabon gini kusa da nata, sai dai yafi nata kyau nesa ba kusa ba saboda tsarin yabanbanta.
Sati daya saura bikin ta dawo gidansu da maraice ta tarar an fitar da kayanta duka anata fenti tayi tsaye turus, sai gashi ya fito daga gidan amaryar yace shigo kiga anyi wa Amarya jere Amira. Gabanta ya bada Ras! Da karfi ta daure tana yake tabi bayansa, na mutu.....kawai na mutu...abinda take nanatawa kenan cikin Rai ganin dukiyar da aka lafta gidan. Sai dai kwalla su cika idanunta tayi saurin mayarwa ganin yanda yake ta zakwadin nuna mata ko'ina. Jikinta yayi mugun sanyi ya kamota suka zauna babban falon Wanda suka Fara wucewa, Amira ya naga jikinki kamar yayi sanyi? Ta Dan kakaro murmushi ba komi tana faman sunkuyar da kai, yayi kasa da murya ki aminta Dani Amira tunda Kika kwantar da hankalinki tare da kwantar mun da nawa wallahi na Miki alkawarin bazan taba watsa Miki kasa a ido ba, yanda mutane suka zuba Ido suga wata baraka Basu gani ba Yanzu daga wurin ki ba wallahi bazan taba bari su gani ba.
*Wannan gidan naki ne bana amarya ba* ita gashi can ana mata fenti kayanki gasu can ana sakawa mota za a Kai wa su *Umma* ( mamar ta ).
Tayi saurin dago Kai Amma suna hada Ido sai ta rushe da kuka.....ya rungumota kiyi hakuri na Miki laifi I knew!
Ita kanta Bata San ya sunan kukan da takeyi ba Yanzu. Amma Tasha almwashin zata Kara daurewa taba maradda kunya har sai taga iya gudun ruwansa though har yau ta kasa aminta da kalaman sa tana ganin kamar yaudara ce irin da mazan yau.
Ya sungumeta zuwa dakin da Basu shiga ba Nan taga ikon Allah duk yafi dakunan kyau da girma yafi ko'ina Jin kayan alatu sannan taga akwatunan da ya saya jere sky blue yace kema ga lefenki can. Kece shaida Babu abinda na banbanta sai kala.
Ahmad da Almustapha ma nasu na tafe gobe anmun waya sun zama ready.
Ta kankame Shi ta saki wani irin kukan Dadi.....kayi hakuri abinda na maka wallahi bazan taba watsa maka kasa a ido ba.....ya Kara rike ta nasan haka Amira kiyi hakuri.
Tuni labari yakai gidan su Amarya Nan da nan maganganu suka tashi wasu na cewa ta Gama dashi wasu na cewa tsoronta yakeyi surutai kala kala har Amarya takai ga ta harzuka.........😄😄 Turkashi a tsumayi diyar Aunty Rabi (mamn ibrahim) kada a manta a ringa Sanya mun ita cikin addu'a Allah ya Kara mata yawancin kwana ya shirya Mata zuri'a da rufin asiri.
Har Yanzu babana ma Yana bukatar addu'a Allah ya bashi lafiya yaba maman mu ladar jinya.
💞 Ni din dai ce Zainab Dahiru wowo maman Abdullah 😄😄💞
🤐 WA ZAI FURTA??🤐
0⃣2⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( maman Ibrahim) Allah ya shirya Miki zuri'a ya Kara arziki*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD KO DA YAUSHE*
*DOMIN KU AUREN FARI FANS ANA MUGUN TARE*