Sashe 50
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
...... Falon ya dauki surutai kowa sai fara'a yakeyi da murna. Alhaji Hassan ya kalli daddy ya ce, ranka ya dade Ina neman afuwa amma Zan yi tambaya.... Cike da fara'a ya ce bisimillah Alhaji.... bisimillah kowa ma na jinka.... Akan daurin auren nan ne, a gaskiya kaina ya daure ban taba ganin irin wannan ba, mun zo neman Aure ne ba Sanya baiko ba, Jin magana ya kawo mu, amma kwatsam ka karbi Kaya da kudi a matsayin kayan Aure da sadaki dan Allah me yasa ka yanke wannan hukunci Kuma ka saka sharadin baka son yaran su sani.... Ya Kara fadada murmushi kafin ya Fara magana Yana kallon Alhaji Muhammad tambuwal, kaga maganar ka ta fito na wata kila su bukaci dogon bayani ko? Duk sukayi Yar dariya ya maida kallonsa ga Alhaji Hassan ya na magana cikin natsuwa: Abinda ke faruwa a gaskiya rawar Kan Anwar yayi yawa, tun asalin tura Bilkisu karatu dutsinma na kaita tare da masu tsaronta ba tare da ta sani ba, na baza securities sosai akan sanar Dani duk wani movement dinta. Lokacin da suka Fara takun saka ita da Anwar na Sanya aka mun bincike akansa, Ashe babu Wanda ma yasan yaron shine *Bushara*, shaidar da ya samu ya sanya ban dauki mataki akansa ba saboda naji cewa yana da halin ko in kula, gadara, Yana Kuma da son addini. Bayan mun Kai Mata ziyara na hadu dashi sai naga fuskar yaron kamar na Sansa, kwatsam kuwa taron da kamfaninsa yayi a Lagos nagan Shi a daily trust. Boye boyen daya ringa yi ma Bilkisu yasa na bashi dama amma a gaskiya zafin sa yayi yawa daga baya muka gane kishi ne. Yana da rawar Kai musamman idan Yana tare da ita, ga kuruciya, ga giyar so da giyar kudi kunga komai zai iya faruwa, Shi yasa na yanke shawarar kawai mu daura masu Aure yanda komin ya Kai hannu ya taba ta Yanzu hankalin mu bazai tashi ba matar sa ce. Dalilin da yasa bana so a fada masu shine, matukar ya ji matar sa ce Yanzu tabbas bazai barta anan gidan ba, kuma a gaskiya bamu shirya aurar da ita Yanzu ba abun yazo Mana kwatsam Babu yanda zamuyi... Na biyu, wallahi sai ya Mata ciki Kota halin Kaka duk da ba haramun bane Amma ga al'ada irin tamu ta hausawa hakan zaifi dacewa idan ta tare a gidan sa kuma gashi wuri daya suke karatu..... Zahiri, inji Alhaji Hassan. Yawwah, to Shi yasa na ce mu kyalesu har sai sun gama makaranta sannan tunda saura shekara daya..... Amma wani hanzari ba gudu ba Alhaji Muhammad ya fada...duk aka mayar da hankali wurinsa.. A sanar da yarinyar domin ta san cewa akwai hukuncin Aure akanta, kasan yaran Yanzu kuma tabbas Kun San cewa shaidanu Yanzu zasuyi ta kunno Kai. A fada Mata sannan a ja Mata kunne a sanar da ita implication na fadawa Alhaji Hamzan ita abun zai ba ruwa...... Kuma fa. Kowa yafada Yana girgiza Kai. Kenan idan mun fahimceku Anwar din kawai za'a boye mawa? Haka ya kamata gaskiya daddy ya fada. Masha Allah hakan yayi Amma dole mu sanar da Hajiya na tabbatar baza ta Bari ya sani ba zahiri..... Hakan Yana da kyau. Duk suka fada lokaci guda. Nan aka kasa komai aka Basu nasu aka masu Sha Tara ta arziki suka tafi suna Murna...... Tafe suke suna al'ajabin dattakon wadannan mutane, abun ya matukar birgesu Alhaji Hassan yasha alwashin shima zai ma yarsa irin wannan gatan da tsare mutunci. Tana kwance yau duk ta tashi tana Jin jikinta wani iri babu kwari, ga kasala ga yawan faduwar gaba, tayi lamoo wayar ta tayi Kara. Tayi shiru don tasan shine kawai zuciyar ta a yau najin haushin sa kadan....ga naci ya dunga Kira ba arziki ta daga... Hello ..ta fada a hankali. Ke yunwa nakeji kiyi mun faten dankalin nan da kikayi mun last week. Kamar ta kurma ihu Shi duniya baida wata damuwa sai ta abinci? Kinji? Ya fada da karfi. Naji.. Ya danyi kasa da murya Zan Sami gasassar kaza? Lokacin ne ta danyi murmushi, ka lissafo kawai abinda za a maka Yanzu zaka Fara Zan Sami kaza?? Sai ka lissafo goma. Ya kyalkyace da dariya sai meat pie da Dan yam balls Amma kada ki cika mun yaji irin wancen kinji ko? Naji sai me? Yayi murmushi sai kiyi kwalliya sosai kisa gyale Banda wannan Dan iskan zanzo don bama zai San fita ta ba. Ta ce hmmm. Ya naji kin yi la'asar ko an Fara fargaba ne? Ta galla ma wayar harara fargabar meye? Ya Kara dariya ya ce wallahi basan an mako mun harara. Tayi murmushi hmm Kai dai ka sani.... Kema kin sani kilibabba Anwar na kalbinki amma kina wani sharewa irin ba sosai din nan ba..... Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar Allah ya shirya ka... Hubby zaki ce bagidajiya. Ke wallahi kina Abu kamar wata Yar kauyen kumus.... Tayi murmushi kawai. Yayi kasa da murya kidan canza mun suna Mana sweetheart....... Kai wallahi Zan ajiye wayar Nan ...ya Kara kyalkyacewa da dariya yace ya hakuri nayi shiru. Ta zumbure baki. Yaushe Zamu fita yawo cikin gari? Ana wannan Corona virus din zaka fita yawo? Ke ban son unnecessary excuse.... Cutar ce unnecessary??? Ya ja guntun tsoki.... Ko *Amigo* muje please...... Anwar kana so asanya ni a labarai ko? Yayi murmushi to muje ShopRite nasan kinfi son can. Ki bari anjima Zan baki labarin abinda ya faru ranar da na ganki a ShopRite din na buya.... Ta zaro ido ka ganni? Yayi dariya eh, Fada mun Yanzu, Ki Bari sai nazo, Yanzu nake so . Yayi murmushi. Kin tuna ranar da Kika tarar da securities a bakin kofa kikayi ta fada a Baki wuri?? Ta zaro ido ba munyi waya lokacin ba, Ina kallon ki ai nine a wurin..... Innalillahi. Ranar ne na biyoki har gida naga address dinki.... Na shiga uku. Kin fita uku....ya fada Yana dariya. Yau Zan baki labarai kala kala idan nazo kinji ko? Tohm, ta fada a hankali. Sai nazo ko? Okay. Ta latse..... Daddy bai Sami damar shiga gida ba sai biyar saura. Suna falon sama ita da mommy ya shigo... Ta Mike daddy oyoyo... Bilkisu meye kike dahuwa Kuma naji gidan duk ya hargitse da kamshi? Mommy tayi karaf tana dariya.... Aikin Anwar ne. Yayi murmushi da alama kin gaji uwaki wurin kula da miji ....... Maganar ta makale. Yayi saurin canza Babi da kallon mommy muje na ganki ya juya zuwa daki. Suna shiga ta kalleshi har an daura? Eh, Amma fa sun kawo shawara.. Ta me fa? Ya zauna Baki gado, sun ce a sanar da Bilkisun Kuma I reason with them, kin ga yarinya ce karama kada ta je tana janyo ma kanta bala'i ba tare da tasan akwai sharadin Aure a kanta ba Kinga mu Allah zai Kama da laifin rashin sanar da ita tunda Bata sani ba..... Zata firgice gara ayi shiru. Ba wani firgici kar ki nuna kin sani Ni Zan Mata magana da kaina.... Me zai hana ka mayar da ita nan gwagwalada ta karasa ..... Biyota zaiyi, wallahi Anwar bazai yarda ba. Shikenan, Yanzu goben zamu tafi sokoton? Eh, ke zakiyi gaba Zan biyoki bayan kwana biyu tare da Bilkisun. Shikenan Allah ya tabbatar Mana da alkhairi......ammeeenn. Bisa bike yazo yau, karar yasa ta fito da sauri ta leka ta taga daidai Yana cire helmet. Kananan Kaya ne jikin sa, ya ajiye helmet din ya saka facing cap.... Mommy zo kiga Anwar yau a bike yazo.... Ta yi murmushi, daga race ya wuto nan din ko? Race Kuma? Eh, kin manta da marece idan mun fita muna haduwa dasu da yawa yaran ministers, president da su Anwar din? Wai sune?, Hada Shi kenan?.... Gashi Kinga alama.!. Zata Kara magana ta ce kije tun kafin ya nemeki ta Haye sama abinta. Yana tsaye bakin kofar ta karaso, bazaka shigo daga ciki ba kayi tsaye? Ta juya ciki ya biyo bayanta kin yi wa mommy magana Zan daukeki muje yawo? Ta mishi banza har suka zauna bisa dining. Kinji? Ta ce a'a bazamu fita mu biyu ba..... Saboda kada na gudu dake? Ta Dan kalleshi, Yanzu fa wannan maganar na iya haddasa matsala...kinji? Kaci abincin Mana..... Ya janyo plate gabansa zanci amma kibani amsa. Tayi shiru, Ko na tamabayeta da kaina? Ta kalleshi da sauri, yayi murmushi Allah kuwa.... Ya kamata kana da kawaici fa.... Akanki fa bani da Shi gara ma ki sani.... Zamu je? Kaiii Wai Kai me yasa ka fiye naci? Saboda na turo da maganar neman auren ki. Ka bari sai Nan gaba.... Family na sunji dadin zuwa gidan nan fa, suna ta mun addu'a da murnar na dace da Mata in shaa Allah.... Ta ce hmm. Yayi dariya Allah kuwa, an karamta su mood din su ya kasa boye hakan Amma sun dawo da wasu Kaya da goro Wai namu ne Haka akeyi? Kai ni ban sani ba...... Ya kyalkyace da dariya ke wannan kunyar fa dole ki ajiye ta gefe kinji.... Ta galla mishi harara. Ya Kara yin dariya.....wannan hararar bansan lokacin da za a daina ta ba ko kuwa salon kallon love din naki ne Haka...... Sai kawai tayi murmushi tare da doka guntun tsoki....Kai dai ka sani....kema kin sani. Duk sukayi dariya. Hajiya na son ganinki duk ta rikice na aika Mata da hotunan ki Wai Bata yarda ba zakuyi video call..... Ina ka Sami hotuna na? A wayar ki na dauka lokacin Dana tafi da ita kin tuna???? Ta galla mishi harara tun lokacin abinda ke ranka kenan??? Ya kyalkyace da dariya meye ke Raina? Tayi mishi banza. Ya Dan gyara Zama ya lunkuma yamball baki kin San fa tun ranar da Kika raba kudin da hahilin nan ya baki class zuciyata ta bani na Sami matar Aure....ta Kara galla mishi harara. Ya yi murmushi me yasa Wai ranar bakiyi gardama ba Kika bani kudin? Ta ce hmm. Anya ba tun tsiwar farko kin kamu da so na .....ta dauki robar ruwa ta Mike kawai ya taso bowl din yamball din a hannu da sauri Yana dariya zo ki daukon meat pie din idan kin gaji da table din..... Nima fa nafi son Zama kasa.....