Sashe 42
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
```Ya juya hannun da karfi, wallahi duk ranar da wannan hannun ya yi gigin taba Bilkisu sai na karya shi, nima akanta Zan iya kisa```......... Ya wurgar da hannun. Sannan ya kalli wadanda ke tsaye *What the hell are you doing here?* Ya daka musu tsawa...... Suka Fara darewa, mufeeda ta juya zata tafi ya fizgota..... ``` Bata hakuri```....... Tayi saurin kallon sa, Jin haka yasa kawayenta Suma suka Fara yin baya, Bakiji abinda na fada ba? ```ki Bata hakuri ko Kuma wallahi....``` Ta fizge hannunta, bazan bayar ba..... Ta wuce da sauri kamar zata tashi sama..... Aisha ta rike hannun Bilkisu tamau. Ita kuwa kanta a kasa kawai tayi shiru...... Ya kalli Aisha, me ya hada su ne? Me kuwa zai hada su inba kaiba??? Ita har Yanzu tana zargin akwai wani abu tsakanin ka da Bilkisu shine fa suka tare mu Yanzu mun dawo sallah..... Mtseww ya doka tsoki. Ya Mika ma Aisha basket ungo je Mata dashi ciki..... Ta juya kawai zata tafi ya yi saurin fizgota ta fada jikinsa kanta ya daki kirjinshi........ Yaushe Zaki fahimci da gaske bana so ki ringa tafiya idan nazo wurinki ko muna tare? Ya hakuri sakeni please..... Ya Kara manneta jikinsa..... Aisha jeki tana zuwa. Ta wuce tana dariya da mamakin wannan rigimammiyar soyayya. Wai Anwar Kan ka qalau? Na shiga uku ni Bilkisu ka dubi Allah ka sakeni..... Yana rungume da ita ya Fara tafiya a hankali ..... Na shiga uku Anwar..... Ya sunkuyo Yana kokarin hada fuskar sa da tata tayi saurin sunnewa jikinsa tana Kara fadin na shiga uku ni Bilkisu..... Ya manna bayan ta da Bango sannan ya matsa baya kadan ya rabu da jikin ta yasa hannuwa biyu ya tokare bango tare da Dan sunkuyawa fuskar sa daidai tata suna shakar numfashin juna ya kafa Mata idanu....... Innalillahi Anwar Wai meye haka? Ta fada tana faman yin kasa da Kai.......Haka zamuyi firar tunda ita Kika zaba..... Na zabi meye? Ka gyara Mana dan Allah ka matsa..... Allah ba inda zanje, ba dai taurin Kai gareki ba? Wallahi zanci gaba da binki yanda kike so, ke me yasa baki da tausayi?...... Tausayin me Wai? Ta fada tana kallonsa kamar zatayi kuka. Gashi yauma saboda mufeeda zaki Kara guduwa kibar ni anan Kuma kin san zuwan naki ne....... Nayi Alkawarin Zan tsaya I'll give you the time you...... Never mind, I'm okay like this.....Anwar am not okay please shift back na tuba kayi hakuri Dan ...... Ke nafiki wuyar lallashi fa ki natsu muyi magana nafi Jin dadin hakan ma..... Tayi kwal kwal, ya kamata..... Na rantse da Allah kina mun kuka Zan mayar dake Nan... Ya nuna kirjin sa. Ta hadiye kwallan ba shiri , kayi hakuri Anwar bazan Kara ba I promised. Yayi murmushi naji but next time. Kina da sauran tuwon nan? Babu. Yayi Yar dariya Yana kallon Dan karamin bakin ta da take ta faman turowa. Duk kin cinye?, Amma fa yayi dadi. Zuwa nayi godiya waccen useless din ta Bata mun plan.... Ba komai nidai jeka sai da safe. Ya kyalkyace da dariya kina korata ne?. Ya Mike ya tsaya daidai ta saki wata ajiyar zuciya Mai karfi ya bita da ido Yana murmushi...... Matsoraciya kina motsawa Zan.... Ba inda zanje ta fada tare da makurewa jikin bango. Kiyi hakuri ya fada a hankali, wallahi Nima fa bana son Ina taba ki Bilkisu ki daina mun gardama kinji? To, ta fada a kagare. Sadeeq ma yaji dadin tuwon nan. Ina Kika Sami manshanu? Ina dashi. Ta fada a hankali. Duk jikinta yayi sanyi....ya Kara tsareta da ido sai ta bashi tausayi. Bilkisu.....ya kirata a hankali. Taji wani Yarrrr, tsikar jikinta duk ta tashi, ta kasa amsawa. Ya Kara cewa Bilkisu...... Na'am ta fada tana murza yatsunta. Dan Allah kiyi hakuri kinji ko? Ba komi ta ce a hankali. Da komai. Gashi naga duk kinyi relax, please I'm sorry. Ba Kya so Ina taba ki ko? Ta daga Kai alamar eh, yayi murmushi to duk laifin da nayi Miki idan muna magana ko Ina a wajen don't leave me, kinji ko? Ta Kara daga Kai .....yayi murmushi Baki magana? Ta ce hmmm. Dan Allah ki daina bana so kinji? To Wai me yasa baka iya kyaleni in tafi?...... Saboda.. sai Kuma yayi shiru Yana murmushi. Saboda me? Ta tsare shi da ido. Bazaki gane ba, yace Yana Yar dariya. Zata Kara magana ya yi saurin cewa na saka Miki turaruka a basket din da na maido Allah yasa kamshin suyi miki. Biyana kayi kenan? Ya zaro ido na Isa in biyaki? Allah kadai zai iya biyan ki Bilkisu. Na zo dasu ne tun daga gida ban dai kawo Miki bane ....... Turaruwanka Zan saka ajikina? Nope, na Mata ne musamman na siyo Miki. Hmm, na gode sosai. Yaushe Zaki Kara mun tuwo? Sai an kwana biyu kuma . Gobe me Zaki dafa? Ina ruwanka, Kai fa abinci ne damuwanka ni kuma ba girki nazo yi ba karatu..... Dariya yakeyi har Yana dukewa...... Wannan tsiwar taki na bir.... Sai yayi saurin canza magana yace tana bani dariya. Ta ce hmmm, ai gara na fada maka na lura Kai baka san ayi abu Dan marmari ba. Dan Allah kiyi abinci dani gobe.... Indomie Zan dafa malam..... Zanci indomie din please ki taimaka. Mtsew taja guntun tsoki. Amma ki bari Zan Miki waya ten minutes before yanda Ina zuwa kin karasa naci da zafi..... Kaci a Ina? Ka Bari Zan Aiko maka.... Bana cin indomie idan ta shiga wani kwano ba plate ba daga tukunya..... Kiyi hakuri zanzo nan in ci..... Anwar! Ta Kira sunan sa. Ya kalleta Bilkisu! Shima ya fadi nata . Idan na tambayeka zaka bani amsa saboda Allah? Ya danyi Yar dariya in shaa Allah. ```me yasa yake son takura mun bayan ga wadanda keson attention dinka kaki basu sai ni da ban nema ba?``` Ya fada murmushin fuskar sa ya zuki iska ya hurar..... Saboda kece best friend Dita. I'm More comfortable with you than any other girl in this school. Tayi shiruuuuu, ya kalleta ko ba wannan amsar kike son ji ba ya karasa maganar Yana dariya. Ta galla mishi harara. Kin San fa a tarihi abincin ki daya na taba ci duk school din Nan apart from sadeeq da ke Mana girki sometimes da Abdul Mai indomie... Yanzu kuwa I don't think ko na sadeeq zan Kara ci....... Ta zaro ido sai nawa? Naki zanci. Gaskiya gara na fada Miki Zaki ringa Mana girki once in a day ko twice idan kina da lokaci...... Amma ka debo dala ba gammo ..... Ya kwashe da dariya. You are my personal person am sure you'll do it.... Bazan yi ba. Naji bazakiyi ba shikenan Amma gobe zanci indomie ko? Eh, amma daga ita karka Kuma cewa don bazaka samu ba.... Yayi murmushi is alright! Zan koma ciki, na gaji da tsayuwa....... To muje ga bench a can mu zauna akwai sakon da Zan fada Miki...... Tana son mishi gardama tana tsoron ya Kara damkar ta, ta yi Dan jimmm ya tsareta da ido...... Muje ta fada a hankali. Kaiiii, amma fa kin bani mamaki na ji dadi sosai ko kefa? Ai gardama bata da amfani..... Suna tafiya Yana surutai kamar ta shako wuyansa takeji. Suna niyyar Zama wayarsa tayi Kara. Ya dauka hello..... Ya zauna tare da Mata nuni da hannu alamar ita ta zauna. Ta Dan raba can karshe a dosane. Ina jinka ya fada Kai tsaye. Ta Dan saci kallon sa sai taga hankalin sa na ga babbar wayar sa Yana latsawa lokacin ne ta lura da iPhone 11x+ yake rikewa ta Dan zaro ido tana satar kallonsa. Wai ita yau wannan tsadadden yaron ke bi.... Ikon Allah, Ina ma zai *FURTA* Yana sonta? Wallahi zata bashi amsa da gaggawa.... Har Yanzu tana wasi wasi shin da gaske friends din ya tsaya ko kuwa ita ya mayar friends??? Ko in jaraba cewa Ina sonsa?...... Tabb idan Kuma yace baya Sona hakan ya kawo karshen friendship din mu? Ko Yanzu a tafi a Haka nasan wasu zasuyi ta misunderstanding irin su useless mufeeda.... Ko banza dai a FUDMA nabar record............ Ke kici kanki tubbb ya tofa Mata miyau... Tayi firgigi innalillahi...ta sa hijab tana gogewa... Wannan wane danyen wulakanci ne haka zaka tofan yawu?.... An tofa sai tsareni da ido kina kallo? Ya harareta..... Bata San lokacin da tayi dariya ba, lallai wanzami baya son jarfa, Kai duk kallon da kakeyi mun nace me? Eh, aini bana munafurci nake ba ke kuwa sai kin lura bana kallonki sai kina dan sacewa kina..... Mtseww ta doka tsoki. Ya kyalkyace da dariya. Ke bakya gajiya da hijab kamar matar liman? Kai Kuma baka iya gani ka kyale??? Ya langabar da Kai don Allah gobe kisa gyale ki fito idan na zo cin indomie....... Bani da gyale. Anan ko? Abuja kina sa.... Maganar ta makale ta bishi da kallo. Abuja ma bana sawa ni hijab nake sakawa ko gida..... Dan Allah Bilkisu... Ta kalleshi Kai bana sa gyale fa. Saboda me? Saboda Ina kishin mijina!!! Waye mijinki??? Mai rabo.... Ta fada tare da Dan kallon sa.... Yayi murmushi, lallai ya more ko wanene. Ta ce hmmmm. Amma fa mijinki zai Sha rigima. Ko? Ta ce tana murmushi. Eh, Mana. Hmmm. Kaima matarka zata rigima..... Ni Ina da rigima??? Kwarai kuwa. Wace iri? Na ci, magiya, damuwa....Kai komai ma. Amma Kuma I'm sweet ko? Ta harareshi a'a chewing gum.... Ya kyalkyace da dariya..... Tashi muje ki shiga gida idan Kika biye mun zan iya kwana haka dake ban gaji ba..... Tayi zumbur kamar tana jira. Ya Mata kallon kasa kasa har taji Yar kunya.... Ta Dan juya tana murmushi. Kin gaji dani already ko? Um um. Eh Mana . Hmmm. Tace. Zan tura miki assignment din nan ta WhatsApp kinji ko? Har kayi? Yayi murmushi kawai. Har bakin kofa ya raka ta sannan yace okay have a pleasant sleep.... Same. Ta fada tare da shigewa...... Ta biya dakin su Aisha ta dauki key ta wuce. Kagare take taga turarukan da yace. Ai kuwa ta gansu don tsadaddu ne designers Kai Anwar babba ne ta fada tana juya daya Wanda yafi daukar hankalinta. Mashin ya hau bai Kira sadeeq ba. Kai Yanzu ka gane firar