← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 68

Sashe 57

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

.......Ta shako wuyanta ta buga da table, gyalen ta ya fadi hular gashin da ke kanta itama tayo kasa, wani chukuikuyon kitso ya bayyana ba 'a ko ganin tsagar ga kegen can manne a wuya.....kaiii Bilkisu kina hauka...mAnwar ya fada a firgice..... Ta nuna Shi da hannu daya korar mun wadannan kattin ta kallesu tana zare ido.... *What the hell are you doing here*?????.... Wata Kara mufeeda ta saki ta dago ta da karfi goshinta ya Kara tsawo kamar wani bread da ake Kira danbisije na funtua...
Ya yunkura zai riketa ta Kara buga kanta a table....Zan nakasa ta Anwar wallahi...... Ya daga hannuwa sama okay ..okay... Ya kallesu kuje waje... Kofar class din da bakin tagogi students ne makil ...... Idanun ta sun kada sunyi jawur tana magana tana zare mishi ido...... Kai bazaka iya maganin ta ba ko? Zan ci ubanta yau saboda duk makarantar nan yarinyar nan ta tsone man ido..... Zan yi..wallahi zanyi maganin ta please kada ki janyo mun bala'i kada kiyi kisan Kai Bilkisu.... wannan cin fuskane ki barshi ta mayar da gyalenta please....Ta ingizata da karfi tayi baya ta fada cikin sit bayanta ya daki kujera da karfi ta saki wata Kara.... Yayi wurinta da gudu a firgice...... Tayi tsalle ta dira gabansa kana tabata Ina karairayata....... Chief security suka gani da wasu securities subhanallah meke faruwa anan.... Yana ganin Anwar yace ranka ya dade da kanka???
Dan Allah ku fita da mufeeda kuje da ita.... Magana yakeyi a harmutse duk ya rikice, Bilkisu kuwa ya dake ta Sha mur Kai baka taba cewa ita ce tayi wannan tashin hankalin ba....... Ya kalli security daya je da ita clinic.... Yallabai kuyi hakuri muje office... Ita ce tayi gaba...... Zuciyar ki tayi yawa Bilkisu wannan yarinyar ta wahala me yasa Zaki.... Ta dalla mishi harara , ka Sanya a daureni na daki sahibar ka kasa a kaini prison..... Ohh my God,
Da gudu sadeeq ya dawo cikin makaranta jin wannan mummunan labari,
Abin mamaki Bilkisu ta Sami shaidar lallai mufeeda ce ta Fara tsokanar ta..... Anwar ya shiga ya fita case ya mutu. Suka fito duk ta chukuikuye fuska... Sadeeq yarinyar kaga zata yi kisan Kai ko?
Bilkisu me...... Na rantse da Allah idan ka Kara mun maganar waccen Yar iskar Zan sameta har dakinta na Mata tsinannen duka Wai Anwar kasan Hali na kuwa?
Na sani a yau, na sani wallahi Dan Allah kada ki Kara kula ta zan kawo karshen matsalar..... Kada ma ka kawo zata ci ubanta.... Ya kalli sadeeq duk sukayi murmushi.
Kawo key din na dauko Miki motar sadeeq ku jira anan..... Ya wuce da sauri, sadeeq ya danyi dariya, duk kin hargitsa mun Anwar kin San Shi baya son tashin hankali..... Tunda takai fagen mufeeda ko? Ai Dole ya hargitse, wace irin masifa ce Suleiman ke bai gani ba?
Kasan Allah ka gaya mishi idan bai nesa da mufeeda ba sai na halaka ta...... Itama daga yau Dole ta shiga taitayinta kuma Zan fada mishi.
Ya iso, ganin baida niyyar fitowa yasa ta fada baya ta zauna Dole sadeeq ya shiga gaba.... Suna fita yayi hanyar gidan sa Yana fadin Bari ki Fara ajiye mu tukun ta mishi banza kawai.
Har ciki ya shiga da motar suna tsayawa ta fito ya dan koma gefe ta shiga wani mugun ribos da tayi sai da ta birge duk Wanda ke shiyyar.... Ya bita da murmushi kaiii sadeeq yarinyar can karshe ce..... Suka kyalkyace da dariya Ina so na ce ta dafan abinci amma duk na tsorata da ita.... Sadeeq ya kwashe da dariya Bilkisun kake tsoro????
.... wallahi tsoronta nake sadeeq, ya fada Yana dariya.
Kaga tsawar da ta daka mun Wai na ce su mustapha su fita???
Duk suka Kara kyalkyace da dariya.... sadeeq ya ce ko baba da babansa.
Mufeeda kuka kawai takeyi, ba dukan ya Mata zafi ba, irin yanda ta cire Mata hular gashi ta tozarta ta gaban jama'a..... Ta kasa daina kuka, kunya ta hanata fitowa daga clinic din ta tafi daki.
Hakuri kawai kawayenta ke bata, Asma'u ta ce Ina ga mufeeda ki shafawa kanki lafiya ki kyale Anwar... Wallahi ko Zan rasa rayuwata bazan hakura dashi ba..... Duk suka zaro ido.
Amina ta ce wallahi matar sa da gaske sunyi Aure mufeeda ki fita batun Anwar ki tsira da mutuncin ki nifa nake gane Miki Yanzu irin wannan cin mutuncin keda dadi?
Ta goge kwallan da suka zubo ko Zan kyale Anwar sai na Rama wulakancin da ta mun wallahi bata Sha lale ba..... Ai kuwa next ba ita ce zata nada Miki duka ba wadannan kattin da ke gadin ta..... Ku duk baku San abinda naji ba, wallahi Anwar fa shine *Hamza bushara* ...... Duk suka kwalalo idanu suna kallonta. Da gaske Asma'u?
Tayi murmushi wallahi kuwa, aini tuni na Fara sensing Anwar wani shege ne ko Kuma baban sa ne wani don gadarar gayen tayi yawa ko lecturers Kuna ganin shakkar sa sukeyi..... Mufeeda ta saki wani irin kuka irin shikenan ta shiga uku kawai..... Amina ta dafa kafadarta kiyi hakuri ba class din ki bane Anwar maganar gaskiya sai irin su Bilkisun saboda Kinga babanta wani me itama tsaye take.... Ba wani babanta wallahi ko Yar gidan malam shehu ce tunda Anwar na sonta shikenan.....Kuma idan Kun tuna zuwanta ance sun Sha fada sosai da ita dashi tun farko ta nuna Bata tsoronsa, ke kuwa mufeeda ke ce Kika bayar da kanki yaushe Zaki ringa bin namiji Kuma guy kamar Anwar kema ai kinsan kin siya ma kanki buhun wulaknci.
Tana kokarin parking Aisha sauko daga napep ta shigo da gudu...... Wai kin daki mufeeda?
Ta fada tana shessheka , ta fito motar, ta bi su mustapha ( body guard ) da harara tayi ciki tana fadin Aisha yarinyar nan Bata da tarbiyya Kuma duk laifin Anwar ne...Anwar Kuma? Shi meye nasa aciki?
Ta hayayyako Mata tafi karfinsa ne da bazai ce ta kyalesa ba? Me yasa sauran Yan matansa ke tsoronsa ita kadai ce zakakka????
Amma Yanzu kinji yanda ake Mata Allah ya Kara a school? Wallahi mufeeda ta shiga uku ko kunya ta isheta kinji labarin da ake yi kuwa?... Maryam ta kallesu ya akayi ne? Tana kwance falo suka shigo
Ta cire hijab ta fada bedroom dinta.... Aisha ta zauna...wallahi Bilkisu ta nakada ma mufeeda tsinannen duka har tana cire Mata hular gashi..ta karasa maganar tana kyalkyatar dariya.. Maryam ta tashi zaune bani in Sha.....
Hmm yarinyar nan ta debo ruwan dafa kanta Wai inba ita jakka ba waye zai shiga shirgin Anwar da Bilkisu soyayyar da kowa ji yake da kansa, soyayyar da sukeyi ma juna ta gadara wa ita ta shiga tsakani????
....ta danyi kasa da murya Wai kinsan an daura musu Aure Ashe?
Maryam ta zaro ido.... Tayi saurin Dora yatsa a lebe alamar tayi shiru....
Haba nidai wallahi nayi mamaki abun fa akwai alamar tambaya.... Kuma kin San waye Anwar?
Ta zaro ido tana girgiza Kai alamar a'a.... *Hamza bushara*..... Ta kwalalo ido ta dafe kirji..kice wallahi.
Tayi Yar dariya wallahi kuwa ta budo Mata waya duba ki gani... A nuna Mata. Ta Kara zaro ido... Bilkisu ta sani?
Tayi dariya wallahi ta sani yarinyar can hmmm kibar ta kawai..... *Bushara* Maryam ta maimaita... Yanzu Bushara takeyi ma wannan iskancin Aisha..... Aisha ta kama dariya fitowarta yasa duk sukayi shiru....
Ta zauna bisa kujera Maryam kinyi break?
Eh, ta fada a darare....
Aisha tace naji ana Kiran wayar ki kuwa.... Ta janyo jakar sai kawai tayi tsoki ta wurgar.... Bazaki dauka ba?
Kyaleshi Anwar ne..... Maryam ta zaro ido..
Aisha tace me yasa bazaki dauka ba?
Me zance mishi?
Duk wannan hatsaniyar waye ya janyota?...... Meye laifin sa Bilkisu?
Ta Sha mur, Aisha har Yanzu Ina mamakin me yasa yarinyar nan ta kasa rabuwa dashi?
Kina ganin ba laifinsa bane??
Ba laifin sa bane..... Ta Mike tare da buga tsoki tayi kitchen......yunwa nakeji Maryam Ina masu aikin?
Maryam ta kalli Aisha itama ta kalleta Aisha ta kyalkyace da dariya Maryam kuwa kasa darawa tayi. Ta rike Baki *Bushara*..... Kut!
Ya kalli sadeeq nifa wannan fitinar yasa naso na mayar da ita Abuja kaga Yanzu da alama ni ne nayi laifi.... Sadeeq yayi murmushi ai dole taji haushin ka mufeeda ta kasa kyaleka itama tana nuna bata tsoronka kaga kuwa Bilkisu Dole ta tuhumeka....
... sadeeq ya zanyi da yarinyar Nan? Wulakancin duniya wane ke ban Mata ba?.... Duk da Haka ya kamata kayi wani Abu da zata kyaleka... Kamar ya? Dukanta zanyi?
Zagi na gidan duniya na Mata amma Bata da zuciya domin Allah meye laifina?
Ka barta zuwa anjima kilan ta dauka..... Bilkisun? Tabbb, yarinyar nan wuyar lallashi gareta Yanzu kaga Ni ta janyo mun jidali shegiya.... Sadeeq ya kwashe da dariya....
Chapter 57 · 0% Book details