← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 68

Sashe 51

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ya zauna bisa carpet ya Mike kafa. Ta dauko ita ma ta zauna dan nesa dashi kadan suna kallon juna.... Ya kalleta yace kamar irin Amarya da angon Nan ko? Ta galla mishi harara. Yayi murmushi, Dan matso Nan kin mun nisa gaskiya... Ta Dan matsa kadan kada taja kuma ya kamota. Ina son wannan rigar ina Kika siye ta? Mommy ta siyo mun Dubai...okkay. Me yasa bazakiyi mun kwalliya da wadanda na kawo Miki ba ko kina Jin kunya? Tayi murmushi kawai. Dan Allah ki saka, Waye telan ki? Mace ce,can cikin Area 8 ne shagon yake. Ki debo kayan da Zaki Kai dinki gobe idan mun fita mu biya kinji ko?..... Nifa bazan bika ba.. Ya kalleta dalili?? Tayi shiru. Kina Jin nauyin tambayar mommy ko? Tayi shiru. Shikenan, Yanzu Zaki iya magana da Hajiya? Ta danyi kasa da Kai tana murmushi nidai ka jira ba yau ba... Ya kura Mata ido Anya ba sauri zanyi a daura Mana Aure ba? Ta dago da karfi... Ya maida bayansa jikin kujera ya Dan kwanta.... Yes, saboda kunyarki tayi yawa gaskiya gara kawai na kawar da ita da wuri don Zaki ringa takurani. Yar tsiwar ma an daina mun sai uwar harara .......Kai zaka karasa mun karatun? Waya fada miki Aure na Hana karatu? Ta harareshi Yanzu ma kana neman kisan Kai Ina ga da Aure Kuma??? Yayi murmushi ko Yanzu ma nikaf Zan siya Miki masu yawa ba shegen da zai Kuma ganin wannan beauty face din ba.... Ta zaro ido nikaf????? Kwarai kuwa. Ta zumburo Baki... Ya danyi dariya ya tashi zaune ko kin fi son kullum ana tashin hankali???? Tayi shiru yaga kamar ranta ya baci. Ya Kira sunanta a hankali..... Kinji haushi ko? Ai wannan tsananin ke bana so, kana abu kamar Wanda bai yarda Dani ba kullum... Yayi murmushi, wallahi na yarda dake.... To me yasa kake da takura? Saboda *Ina son ki* Ta kalleshi da sauri.. watau duk lokacin da yake cewa saboda ..yayi shiru abinda baya son fada kenan? Kin gane ai Yanzu ko? Ta Dan harareshi kawai. Ya kyalkyace da dariya yace *Bilkisu H. Bushara*........ Ta Kara galla mishi harara. Sai goma da Rabi yabar gidan. Tana shiga ta tarar da daddy falon Yana kallon News. Ta wuce sum, sum, sum..... Zo nan Bilkisu. Cikin Jin kunya ta karaso ta zauna kasa kusa da kafafun sa. Anwar din ya tafi? Eh, Da alama zaiyi kula sosai ko? Tayi shiru tana sunne Kai. Sai dai Shi din ya fiye damuwa ko? Ta Kara yin shiru tana murmushi. Ya Aiko da iyayensa kamar yanda na umurta hakan ya nuna tabbas sonki yakeyi da gaskiya. Amma kina ganin zaman ku makaranta Yanzu a Haka bazai takura ki ba yayi affecting karatun ki ba Bilkisu? Nima Ina tunanin haka daddy, saboda Yana da rigima sosai..... Na sani. Ko muyi wata shawara nida ke bazaki fadawa mommy ba? Eh, daddy. Ta fada da sauri. Kinga tashin hankalin baya shakkar kowa kada yaje wata Rana ba fata akeyi ba yayi aika aika.....ko ? Ta daga Kai. Ko in sa iyayensa su dawo na daura Miki Aure dashi cikin sirri ba tare da ya sani ba? Ta zaro ido cikin firgici zatayi magana yace jira kiji dabarata....... Bazamu yarda ya sani ba, dalili kuwa shine irin damukar da yake Miki tabbas Yanzu zai Kara sake salo Kinga hakan akwai haramci Amma idan akwai Aure ko hannun ki ya taba ga Allah babu laifi iyaka kici gaba da nuna mishi Baki so har a Samu ku Gama... Kin gane ai ko? Ta daga Kai. Koda wasa kada ki fadawa kowa kinji ko? Ta ce toh, Yanzu mubi wannan shawarar tayi ko? Ta daga Kai yawwa,to ungo ya Mika Mata kudi...sadakin ki ne dazun kafin su tafi an riga an daura Miki...... Kudin suka Fadi sai kyarma kyaf,kyaf,kyaf..... Ya Bata labarin duk yanda akayi sannan yaci gaba da lallashinta har ta daina zubda hawaye. Amatsayin sa na uba na gari ya fada Mata sharuddan Aure don ta kiyaye......... Tana shiga daki ta fada Kan gado ta rushe da wani irin Kuka Mai tsima Rai. Anwar kuwa na shawo kwana ya haska sadeeq can nesa bisa wani dakali da alama waya ce yakeyi. Ko gida bai shiga ba masu gadi suka bude gate da sauri securities suka fito.... Ya sauka yace su shiga dashi ciki ya koma Yana sando a hankali ya nufi gurin da ya hasko sadeeq.... Zaune yake ya bada baya Yana waya. Ya daga hannu zai bashi tsoro sai kawai yaji Yana cewa...... Wallahi tallahi baba an daura mishi Aure yau.. ya koma ya tsaya tare da rungume hannu. .... Hajiya ke fada mun Amma basa son Anwar din ya sani..... Gabansa ya bada dammmmm.... Yaci gaba da cewa, wallahi kudin neman aure suka Kai shine mahaifin yarinyar kawai yace sun Isa shaida Aure aka daura... Wallahi kuwa. Amin amin... Eh, bana tunanin yarinyar ta sani gaskiya. A yanda aka ce mahaifin yarinyar ne yace lallai sai an daura auren saboda rawar Kan Anwar yayi yawa..... Eh sai dai mun dawo din. Amma Dan Allah baba kada ka fada ma kowa babu Wanda yasan hakan. Amin ya Rabbi. Ya Mike ....juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin want irin yanayi ya razana ya firgita yayi baya da sauri ..........😄✍🏼
Chapter 51 · 0% Book details