← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 68

Sashe 66

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

turawan nan kuwa duk sun rikice an Gama kashesu da salo. Wani juyi da sukayi cikin wata rawa ta duke Anwar bai San ya sauko ba ya balle rafar kudi. .... Wuri ya dauki ihu...gani Bilkisun ta canza salon rawa sun mayar dashi tsakiya suna wani takun..... So sai mutane suka karasa gigicewa kawai ya canyota da karfi ya rungume aka dauki ihu aka taso ana barin kudi........ Biki yayi biki.... Partyn ya bada kala.......live aka ringa nuna program din a tashoshin television na gida da waje..... Sai Sha biyun dare aka gama..... Sai da suka tabbatar kowa ya tafi sannan suka shiga mota . Ya janyo ta jikinsa, waye ya koya Miki rawa haka? Ta danyi dariya..... Bude Baki kiyi mun magana ko Kuma na yakai hannun bayanta zai zuge Mata zip din Riga...... Ya hakuri jira inyi magana... Ya kyalkyace da dariya kaiii kin fiye tsoro. Daddy jiya ya aika da motoci na abinci na ce kada ya siyi komai Amma yaki yarda, Ni Ina da kamfanin shinkafa meye za a kai mun? Ni ke shigowa da Mai Ina da kamfunan man gyada Amma..... Duk da Haka ai al'ada ce..... Al'ada addini ce? Ni yaban ke tsingirin gatarin ki na tafi abina..... Ta danyi dariya. Ya Kara matsawa kusa da ita ..... Ina son salo irin na daddy Bilkisu a gaskiya ya iya dattako da daukar ma Kai mutunci.... Ta ce hmmm kawai tare da Dan muskutawa don taja baya.... Ya Kara matsawa ya janyo ta ya Fara lalube...... Ta ce innalillahi na shiga..... Ke! Kin shiga ukun ko? Ke Wai kin San shiga uku kuwa? Ta soke kai... Ya Kai Baki wurin kunnen ta ya ce ```please in zuge zip?```.... Ta ja baya da sauri..... Kayi meye? Nidai don Allah ka rufan asiri. Ta fada kamar zata mishi kuka . Ta Riga ta Kai karshe bakin kofa ....ya Kara matsowa Yana Yar dariya to Wai ke gobe ya zamuyi anya bazaki bani wahala ba?....... Ta kudundune Kai ta ce *Na bani* ya kyalkyace da dariya yace ikon Allah.... Motar ta tsaya. Ta say hannu zata bude ya kamota jira Mana saurin me kikeyi? Anwar nidai Zan tafi gida Dan Allah..... Na Fara Baki tsoron ko? Tayi shiru. Yayi dariya..... Ya tallabo fuskarta ke ko Yar karar Nan ki kawon gudummuwar tsumi Nasha ko?..... Ta zaro ido. Ya kyalkyace da dariya, amma dai kin San nasan su waye sokotawa ko?..... Kai Ni ban Sha komai ba..... Ya Kai hannu zai kamota ta makale jikin kofa..... Karya kikeyi kinsha Mana Dan Allah an dafa Miki kaza?...... Na shiga uku ni Bilkisu.... Ya kyalkyace da dariya... Nidai Dan Allah ki dauri kici Kisha kinji ko?....... Naji sai da safe.... Ya janyo ta da karfi ta fada jikinsa yace .... Yawwa kin yarda kenan nasan Kuna ci. Ohh yau ni tawa ta sameni ni Bilkisu.... Ya kyalkyace da dariya kina birgeni wallahi. Ya Kai Baki a kuncinta Bari ko nan na Dan sumbata...... Ta runtse ido, ya Dan Kara tattabata yana fadin, ai nayi namijin kokari Bilkisu na ba da mamaki shekara daya ban komai ba .....Hana ai wallahi ko ban nema ba ya kamata gobe ki nemeni da kanki ko? ya saketa.... Da sauri tabar motar yabita da dariya..... Gabanta sai faduwa yakeyi ita kawai tasan ta Gama mutuwa taje gidan sa. Washe gari ko ita bata San inda zasuje da daddy ba don baya son fada Mata kada ta Tara mishi jama'a da kuka. A airport ta kura mishi ido Amma yasha mur babu fuskar tambaya. Koda ta shiga jirgi ta fahimci abinda ke Shirin faruwa sai kawai ta Fara kuka..... Ashe tun kwana biyu da suka wuce an kai duk Wanda zaiga gidanta ya gano. Tsinken ragin ta ya Kai daki....... Gidan ba kowa sai Mai gadi kadai, Shi kansa Anwar din bai sanar da kowa ba . Kuka take wiwi....gidan Yana daddy tsoro ya firgita ainun yasan waye Anwar Amma zahiri gidan ya tayar mishi da hankali Shi kansa ya tabbatar diyarsa ta Gama Dace duniya. Ya Mata nasihohi masu shiga jiki ya janyo Mata ayoyi da hadisai, kannen ta duka biyun suna gefe suna Yan kwalla Yanzu gida ya koma sai su daddy kadai saboda su Daman London suke karatu basa Zama Nigeria sosai. Da zasu tafi ta rike su, ta na wani irin kuka. Haka suka lallabata suka barta kwance bisa gado ji takeyi kamar zata mutu. Anwar kuwa karfe Sha biyu ya Gama sallamar duk wasu Baki. Banda Aisha da Maryam saboda su daga Kano zai Sanya akai su gida. Ana saukowa masallaci suka wuce Kano din . Gidan su makil da jama'a ana wani sabon bidirin. Kano ta Kai ta kawo unguwar ta cika makil....... Isowarshi yasa garin da unguwar Kara rikicewa..... Yayi ma Aunty Salma waya da Hajiya rukayya Bako da su zo su dauki Amarya a tafi da ita can cikin dangi..... Har lokacin Bata daina kuka ba, bayan ta shirya sun fito kawai ta hango su Aisha Nan ne zuciyar ta, ta Dan saki. Bai yarda ko da wasa ta ganshi ba.... Acan aka kaita inda Hajiya... Nan fa ta ringa ganin gata da tarairaya......karfe hudu su Aisha suka tafi ba tare da ta sani ba, ya masu Sha Tara ta arziki Maryam duk ta gigice hada kukanta. Karfe takwas aka shirya wata kwarya kwaryan dinner wacce har taso tafi ta Abuja danginsa sun yi namijin kokari. Sai basarwa yakeyi, ita abun ma sai ya ringa Bata mamaki ganin bai waccen zakewar ko me yasa yake ma Yan Kano Isa da takama?. Sha daya nayi yace a tashi haka dare yayi. Suna fitowa ya shige mota da Amarya sukayi gida kawai...... Hannunsa da nashi rike maimakon taga sunyi bangarenta Wanda aka kaita dazun sai taga yayi nashi da ita. Gabanta ya bada ras! Suna shiga falon farko ya saki hannunta ya garkame kofa ya zare key ya kalleta muje sama ko?............✍🏼😄
Chapter 66 · 0% Book details