Sashe 54
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bilkisu..... Ja'iri ashe mace kabi Shi yasa ka dage Kai anan zakayi karatu.... Ya yi dariya Wai waye ya fada miki mace nabi? Coincidence ne ya hada mu, amma ni ba ita nabi ba.....yaki nuna ma kowa yasan wainar da ake toyawa. Har suka je sokoto suka dawo bai nemeta a waya ba. Hakan ya Bata mamaki, ta Fara tunani ko daman rashin sanin inda alakar su ta dosa yasa yake yawan takura Mata Yanzu da ya tabbatar magana taje ga iyaye yasa ya Sami natsuwa?. Har iyayen nata sai da suka fahimci hakan. Shi kuwa yayi amfani da wannan Dan hutun ya Fara zirga zirgan nemar Mata transfer zuwa University of Abuja. Ko sadeeq bai fadawa ba yasa aka had a mishi transcript dinta cikin sati biyu ya kammala komai. Hatta kayan ta kafff yasa an balle dakin an kwashe sannan ya gyra kofar ya rufe. Yana jira akoma ya Mata registration...... Ranar da aka koma, ya aika da komai washe gari yazo da takardun gidan su. Tana ta shiryen komawa, bai Mata waya zai zo ba sai dai suka ganshi kwatsam, ta gama kulewa fushi sosai takeyi dashi saboda kusan sati daya kenan basuyi waya ba. Yanayinta kawai ya kalla yasan fushi takeyi. Yana zaune bisa hannun kujera alamar kamar sauri sauri yakeyi, ta Kara daure fuska..... Wai fushin na menene? Ta mishi banza. Yayi Yar dariya, kiyi hakuri abubuwa sun mun yawa ne, bana zaune..... Kuma shine baka da lokacin kirana??? Ya Dan yi murmushi to ke ba sai ki Kira ba? Ko laifi ne Mata ta Kira mijinta..........dammmm gabanta ya Fadi ta kalleshi da sauri yayi murmushi yes tunda na Aiko gidan ku ai kin Zama matata ko wani ya Isa ya shigo Yanzu neman aurenki? Ta Dan saki ajiyar zuciya, ya kusa sakin dariya..... Nayi missing dinki sosai Bilkisu, Ina ma ciki amma nasan komai na Dan lokaci ne daga ranar da aka mikon ke nasan komai ya Zama labari....... Gobe Zan koma school. Ta fada a hankali. Keda waye Zaki koma? Ban sani ba daddy yace na Fara sanar dakai tukun. Da banzo yau Kuma fa? Zan maka text. Saboda me bakya son kirana? Tayi shiru, Ya kamata ki rage kunyar nan fa. Tunda na Aiko gidan nan Bilkisu duk kin canza kinyi sukuku Anya kina Sona? Ko baki son kiyi rayuwa Dani? Baki magana? Kina damuwa ne akan rabuwa dasu mommy??...... Sai kwallah suka zubo mata sharrrr...... Ya Salam ya tashi yaso gabanta , tunanin ta zai kamata kamar yanda ya Saba sai taga ya zauna gabanta ya harde kafa....... Kinga ki kwantar da hankalinki wallahi Bilkisu bazakiyi dana sanin Aure na ba, bazan taba Bari ki tozarta ba. Ke shaida ce, duk kudi na da commitment nawa bai hana na baki time din kanki ba, Ina son kula Shi yasa Nima nake kulawa dake, Ina son ki fiye da dukiya ta, wallahi tallahi ko Yanzu da Kika ga na Dan kaurace Miki I wanted to prove your parents how good I am, and how I truly loved you. Kin San cewar nasan an daura Mana Aure?........ Ta Mike tsaye ta zaro ido, ya Kara Yar dariya yes I knew it and I promised my self I'll never touch you again, tunda an ce *Ina da rawar Kai* Ta Kara kallon sa da sauri, ya Kara dariya. Ya Mika Mata takarda ga Shi gobe gobe Zaki je kiga registration officer na nan University of Abuja akwai abinda Zaki karasa, ta Kara zaro ido. Me kake nufi? Ya Dan Sha mur, Ina nufin na mayar da ke can anan Zaki gama.... Kai kuma fa? Ni Zan karasa a dutsinma..... Wallahi ban yarda ba ta Mike tsaye.... Shima ya Mike, wannan shine umurnin da na Baki Kuma abinda na zartar a matsayina na mijinki....... Akan meye zakayi haka? Saboda na nunawa kowa cewar ba sha'awar ki nake ba sonki nakeyi saboda Allah......Anwar.... Bilkisu kada Kija maganar nan, kada kuma ki sanar wa iyayen ki cewar nasan an daura Mana Aure kawai Ina son ke ki amince da *Ni Anwar son da nake Miki na Aure ne ba na sha'awa ba*.............😄✍🏼