← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 68

Sashe 43

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

dare ko? Kai Kuma ka gane sa ido nonsense ya Kai mishi duka. Allah Anwar Kai munafuki ne....... Ya kyalkyace da dariya Kai Allah ne ya fiddani da wuri ina zuwa na tarar da mufeeda ta janyo gardawa zasu daki Bilkisu..... Ya dauki waya ya Fara nemanta. Da gaske??? Sadeeq ya fada Yana mamaki. Wallahi, yarinyar Bata da tarbiyya....kaga Ina Kira taki dauka gobe Zan buge Mata warning na karshe idan Kuma bata ji ba nasa a koreta ko waye ubanta..... Anwar kabi sannu, fitina kwance take.... Sannan yarinyar nan kada ka takura Mata fa. Naji. Ya fada Yana kokarin tube Kaya. Washe gari ta tashi da wani ciwon ciki Mai tsanani ta kasa zuwa class. Suleiman na ganin an Gama lecture ya kirata saboda yasan ta dawo.... Anwar na bayansa Koda yaga yasa waya a kunne sai ya kura mishi ido yasan tabbas Bilkisu yake nema. Hello.... Lafiya dai ko? Naji muryar kamar Mai bacci kamar Kuma wacce bata lafiya.... Ciki?, Subhanallahi..... Anwar najin haka yayi zumbur ya mike ya ce zo muje sadeeq... Sauri yakeyi sosai, sadeeq ya fito da gudu, Ina zamu je? Bilkisu ce Bata lafiya.... Me ya sameta? Kamar naji Yana ambaton ciki it might be ciwon ciki... Suna zuwa bakin titi yace tare Mai napep ka taho dashi.... Ya tsallaka da sauri. Allah ya rufa Mata asiri akwai doguwar Riga a jikinta , Aisha na ta faman dama Mata oat ya shigo dakin..... Kanta ba kallabi gashi ya bazo a gadon bayanta ta kifa Kai a filo tana ta murkususu Aisha kuwa daga ita sai shimi.... Ya fado dakin.... Duk suka firgita. Aisha tayi saurin janyo bargo . Ko kallonta baiyi ba ya zauna bakin katifar.... Ciwon ciki ke damunki? Ya fada Yana kallon Bilkisu cikin damuwa.... Firgigi ta dago tare da janyo towel dake kusa da filon ta rufe kanta.... Anwar meye haka? Ta fada da kyar . Ya doka tsoki. Tashi muje hospital. Ba sai naje ba na Sha magani..... Tashi muje hospital ya fada cikin daga murya..... Ta kalli Aisha ita Daman su kawai take kallo. Cikin ya Kara katsawa ta runtse ido tare da dukewa.... Ya dagota da karfi ya kalli Aisha Ina hijab dinta?????.... Wayarsa tayi Kara... Ya dauka sadeeq ya? Kana inane? Gani a bakin gidan ban ganka ba.... Okay Ina zuwa...ya kashe. Tana son magana amma ta kasa saboda murdawar da cikin keyi ... Ya taimaka ma Aisha suka saka Mata hijab kawai sai ya sungumeta....... Yi sauri ki fito...ya fada Yana kokarin fita da ita. Sadeeq ya zaro ido Wai ciki ka shiga???? Seriously tayi penting ne???? Aisha ta fito da gudu rike da kofin oat. Sadeeq ka same mu Sima hospital ya fada, ya kalli Mai napep muje sima. Suna Zama ta janye jikinta daga nashi ta dora kanta bisa kafadar Aisha. Bai bi ta kanta ba yace Aisha meye taci ne? Bata ci komai ba Daman haka take fama dashi..... Ciwon cikin? Eh, tana da wani magani da take Sha ne? Eh, Amma dai baya lafawa da wuri. Wane irin ciwon ciki ne Haka? Tayi shiru kawai. Kinji? Ta ce hmmm, Daman duk wata sai tayi? Bai gane ba ya kalleta duk wata Kuma? Eh. Mtseww...... Ya kalli Bilkisu kin taba zuwa asibiti an Miki test? Tayi shiru kawai tana murkususu. Ya Kara doka tsoki. Ya dauki waya....hello yah good morning doctor please I have emergency patient are you.... Good. On my way... Ya ajiye. Ya kalleta sorry. Aisha dai tayi zugum. Bakin gate suka tarar da kijerar daukar marar lafiya. Aisha ta Fara sumke dariya. Suna saukowa yace hau Bilkisu...... Tayi karfin halin maka mishi harara sannan ta dafa Aisha suka wuce..... Ya biyota Baki lafiya amma Baki daina gardama ba ko? Dashi aka shiga wurin doctor. Ka ce ya fita , ta fada tana kallon doctor din cikin fushi..,.. yadanyi dariya to kaji yallabai an koreka. Wallahi ba inda zanje ka Mata test kayi scanning..... Ya Fara Mata tambayoyi. Ta yi shiru.. akayi Justin duniya tayi magana taki. Dole Anwar ya fita. Yana fita sadeeq na isowa....Aisha na zaune tayi zugummm tana kallon ikon Allah. Doctor menstrual pain ke damuna Amma bana son ya sani. Ina Shan wannan maganin amma baya mun idan akwai Wanda ya fishi pls help me...... Ya danyi murmushi I expect it. Ya karbi maganin ta runtse ido tare da dafe cikin lokacin da ya katsa..... Sorry ya fada tare da mikewa..... Ya dauko wata allura yace Amma fa zata Sanya ki barci sosai, sannan ya rubuta wani magani ya ce gaskiya babu Shi anan sai Kano ko katsina Yana da tsada kwarai.... Ba komai rubuta... Burummm ya banko kofa daidai ya Gama allurar tana murzawa. Ta dalla mishi harara..... Doctor meye tace Yana damunta? Yayi dariya it's normal an Mata allura ga magani nan na rubuta Yana da tsada da kudi sosai....... Ya karbe takardar Yana karanta sunan maganin. Ya fiddo waya..... Hello musbah ga magani Nan Zan turo maka asiyo mun carton dinsa a Aiko Yanzu Yanzu ko ka tado wani ya kawo sannan kace a fada maka maganin menene da Kuma yanda ake shansa. Kaje wurin nagari pharmacy kace ni na Aiko kaga hamisu a wurin....... Ya Mika mishi hannu thank you doctor. Tashi muje.... Idan kin hada Baki da doctor wannan maganin zaisa na San komai. Idanunta suka Fara nauyi alamar allurar ya Fara aiki. Allaurar zata sanyata barci sosai fa.....okay. Ya ce Yana Shirin Kai hannu ya taba ta, ta mike da sauri tare da maka mishi harara...... Yayi dariya Kai yau Ina Shan harara ni Hamza. Ta fito ya biyota ga oat din ki zauna Kisha Aisha Bata... Ka barshi Zan Sha a daki.. muje please. Ya kalli Aisha allura akayi Mata Mai Sanya barci shine ke dibarta ga idanunta nan sun Fara canzawa da kunje kada ki yarda ta kwanta bata ci komai ba...... Ko na ajiyeta.... Ya banka mishi wani kallo. Wancen Mai napep din da na tsayar Kuma fa? Ta kalleshi ka bi sadeeq ku tafi mu sai muje a napep din na gode. Kamar zaiyi gardama yayi shiru....sai Kuma ya kada Kai okay. Idan kin tashi barcin ki mun flashing please. Ta ce toh. Ya zaro dubu biyu ya Mika ma driver yace mayar dasu inda ka dauko mu. Ya Dan leka Allah ya bada lafiya Zan kawo Miki maganin kinji ko? Ta ce toh, tana ta faman lumshe ido..... Jinsa take har cikin ranta. Bata so ya tafi.....ashe shima hakan yakeji.......Sadeeq ya kalleshi abokin Bilkisu..... Ya Kai mishi duka. Shi Kuma ya tuntsure da dariya.....
Chapter 43 · 0% Book details