← Book details Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 68

Sashe 27

Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta dan rike kugu tana Yar rangwada.... Mura kakeyi haka?
Wuffff.... Ya riko kugunta, kece Zaki Sanya mun ita Yanzu, Ina Kika Sami kananan Kaya haka?
Sai faman shinshinarta yakeyi ya nutsar da kansa cikin wuyanta.
Tayi wani juyi tare da mayar da fuskar ta gab da tasa saboda ya sunkuyo tayi warrrr...... Kawai taji ya hada bakin sa da nata...... Fittt... ta fizge. Ta danyi baya tare da buga wani makirin tsalle rigar tayi sama cikinta ya fito fili..... Kanka qalau kuwa?
Ya yunkura zai Kara chafko ta tayi baya tana Yar dariya idanunsa sun kada sunyi jawur.... Ya kalleta kamar Mai Shirin yin kuka *Dan Allah ki tsaya bani da karfin binki ko'ina*.......
Amma kasan ba anan kake ba ko?
Ya langwabar da Kai, please one kiss.... Tabbb wlhi Haram. Ta fada tana wata karairaya.
Ya kura Mata ido duk hankalin sa ya tashi.... Amira kada ki hadu da fushin Allah ki tsaya....
To Yanzu....... Charaf! Taji ya damke ta cikin taku daya. Yana riketa ana dukan kofa da karfi.
Kafin yayi wani motsi ya jiyo muryar hajia ( mahaifiyar sa ) tana fadin Amira ko Bata ciki ne?.
Ya buga wani uban tsoki ya ingijeta ya wuce bedroom dinta da sauri.........

***************
*Federal University dutsinma*

It seems like baki da gaskiya fa!. Ya fada tare da tsareta da ido.
Ta dake ta kalleshi Yanzu dai Wayata ce zaka tafi da ita ko?
In shaa Allah, ya fada Yana murmushi.
Wai meye zakayi da wayata ne Anwar?, Bincike......., Ya fada Kai tsaye Yana kallonta, tayi shiruuuuu.......
Naji Zan baka, kawo na goge abu daya shikenan....menene?
Wallahi dana goge Zan baka hoto ne.....hoton Suleiman?
Ta doka tsoki Wai Kai komai Suleiman??????
Eh, ai kema komai shine....mtsewww to ba nashi bane nawa ne.
Kiyi hakuri bazan Baki ba don Ina son ganin hoton.
Ta Sha mur bani da Riga ne, Shi yasa da best Aisha ta daukemu muna cin abinci akwai hotuna da yawa nawa sai ka gaji da gani amma wannan bana son ka ganshi.......Ni Kuma naji Shi kadai nake son gani ma .....ta zaro ido. What?
Cikin fushi ta juya gara ta nade tabarmar kunya da hauka... shikenan sai da safe ka cinye wayar ko kaje wurin Yan gyaran waya su bude.....dawo dawo....zo ...zo..zo please. Gashi zo ki goge ya fada da sauri Yana fiddo wayar daga aljihu.
Ta kusa sakin dariya Amma ta daure ta Mika hannu okay bani.
Ya rike wayar yaki saki.....ki rantse da Allah ba text ko hoton wani Zaki goge ba...... Wai me ka daukeni ne?
Ya langwabar da kai hoton nawa Zaki goge?.... Ikon Allah ta fada duk ta Fara kosawa, guda daya ne ko?
Ta sakar mishi wayar ganin baida niyyar Bata..... Ya Kara mikowa ungo amma kiji tsoron Allah kada ki gudu da ita Kinga na rantse.
Wallahi Zan baka Yanzu.
Ya sakar Mata ta Dan ja baya ta fidda key din sannan ta shiga setting ta chanza password din, tana dannawa zata Kara confirming yayi fit!!.... Da wayar, Wai meye kikeyi?.
Kawo na karasa please baka zanyi...... Password kike canzawa??????? Ya fada Yana Mata wani kallo.
Tayi murmushi, Yanzu dai Kara confirming ka Sanya *Balky02* shikenan.......
Dirowa yayi bisa mashin din saura kadan ya fada Mata tayi saurin ja da baya, kawai ya Fara binta Yana magana cikin daga murya.... password Kika chanza? Hankalin sa duk ya Fara tashi cikin bacin Rai....... Ai ...ai ....tanayi tana ja da baya Yana binta.
Gama korar awakin na rantse da Allah sai kin sanar Dani tsohon password dinki da dalilin da ya Sanya Kika canza....au ni Kika mayar photo?
Bayanta ya daki bango ta daga hannuwa sama Dan girman Allah ka ja baya Anwar......waye password dinki?
Ta runtse ido...... Dan Allah kaja baya Zan fada maka...... Kina fadawa Zan koma inda nake meye tsohon password dinki?
Dabara ta fado Mata, sunan da ake kirana gidan mu ne Kuma bana so ka ...... *Balky* shine abinda ake kiranki saboda har daddy da mommy suka tafi banji sun kiraki da wani suna ba bayan haka wane password ne Kika goge Wanda bakya so na sani?
Ka koma yanda kake kada wani ya ganmu a...... Suleiman kike gudu da samarinki ko? Ya Kai hannu daya a bango.
Ta runtse ido na shiga uku.....sai kwalla sharrrr....... Ya kura Mata ido jikinsa yayi sanyi sosai, ya sauke hannun a hankali ya Dan ja baya tare da saka hannuwan sa duka ga aljihu ya kura Mata ido.
A hankali ta bude ido, ita kanta Bata iya fadin ga dalilin kukan, saboda wani yanayi ne ta fada Mai rikitarwa.
Ke shagwababbiya ce?
Kamar ta shako wuyansa,
Tayi mishi banza.
Meye tsohon password dinki?......woohoho, Anwar idan maye ne ya Kama mutum tabbas sai mutuwa.
Kina so kiga irin tawa rigimar ko?....... *Yar Fara* ta fada a hankali, kakata ce kafin ta rassu take kirana da haka shine na saka........ta karasa maganar tana addu'a a zuciya ya Allah ya ceceta ya yarda da hakan.
Yayi jimmm, sannan yayi murmushi me yasa baki so nasan haka?
Ta galla mishi harara ban sani ba .....Nima meye zakayi da wayata?.
.......yayi Yar dariya, bincike....ai Ni ban boye Miki ba.
Karfe nawa?
Ina ruwanki da ko karfe nawa keda kike bakin kofar gida fadawa kawai zakiyi?.
Ina binki bashin abinci Wanda aka mun kwalele lokacin da mufeeda tasa nayi laifi......ta doka uban tsoki, kaje ta dafa maka mana.
Saboda me?
Saboda yarinyar ka ce.
A'a na kawata nake so my best friend Bilkisu.... Hmmm.
Ko ni ba babban abokin ki bane?
Shine, ta fada a gajarce.
Kika ce mun bakya fitar dare ya akayi yau Kika fito ??? Wannan karon Yar dariya tayi Wai haka kake da masifar tambaya?
Ya bi kumatunta da kallo, yau Kika San haka?
Tayi hamma ,
Barci yazo?
Da sauri ta daga Kai.
Yayi murmushi, to jeki kwanta...... Ta juya da sauri daman kafafunta duk sunyi dayi saboda tsayuwa.
Tace sai da safe.......ya bita da kallo Jin bai amsa ba ta Dan waigo....ya tsareta da ido ta dalla mishi harara.....wallahi ka fiye kallo da yawa. Ya matso da sauri me?
Ta kwasa da gudu ta fada gida tana fadin Wai yau meke damunka ni Bilkisu??????
Ya Kama dariya kawai ya juya ya haye mashin. Tana jinsa ya tada ya tafi sannan ta shige daki.
Ta cire kayan ta mayar Dana barcin da ta cire ta kwanta.......akwai tambayoyin da nake son yiwa Anwar amma inajin nauyi.
Ta lumshe ido.....yau dole ta kwana karatu kada gobe taci kaniyarta, abubuwan da suka faru suna dawo Mata a hankali.
Ya Allah kasa Anwar mijina ne....ta fada a hankali.
Tayi tagumi, nasan Yana Sona.....Amma Ina son ji daga bakin sa, ya Allah yasa da gaske abinda nake gani a idanun sa har cikin zuciya ne ya bashi ikon *FURTAWA*........ Ta lumshe ido........

Sha biyu saura ya shiga daki.
Dakin a cike ana jiransa.
Ganin hada Yan 100level yasa bai saki fuska ba kada su Anas su kawo mishi wasa( .....Kai Anwar case ne ).
Kowa jinin sa akan akaifa don karamin aikin sa ne ya fatattaki kowa yace barci zaiyi.
A hankali yake kallon kowa daman duk dudumar za'ayi dakin Babu Mai hawan gadon sa,
Ya zauna bakin gado yace to bisimillah....... Duk suka zaburo.
Bai Sami kansa ba sai uku saura.
Tuni su Anas sunyi barci.
Ya kwanta daga Shi da best Daman akwai wuta ya janyo laptop dinsa yayi connecting da wayar Bilkisu ta nuna mishi option ya shiga *transfer file*...
Gallery din ya shiga, a screen din system din yake kallon pictures din......ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin hotunan ta da yayi ba Wanda ta dauka babu hijab.
Duk duniya ba abinda yake son gani a kullum irin ya kalleta ba tare da hijabi ba.
Tsikar jikinsa sai tashi takeyi yayi ma wani hotonta kuri da ido Yana kallon kirjinta........hazbunallah ya fada.
Ya zaro ido ganin wani hoton Shi Kuma ba kallabi gashin ya zubo Mata a kafada ya zarce kirjin ta...... Attachment ne ko nata? Ya fada Yana rike Baki......
Wannan yarinyar anya Bata fi karfina ba?
Zumbur yayi ganin ta cikin kanan Kaya riga da wando tana rungume jikin daddyn ta, gefe mommy ce da kannen ta biyu maza. daganin pic din kasan ba Nigeria bane......yayi Mata kuri da ido Yana kallon kugunta..... Ya fadada murmushi *this is Dubai*....... Nawaoooo.
A hankali yake ingiza hotunan a system din sa. yarinyar nan gaskiya ta gama haduwa.......kutt!!! Ya Kara rike Baki.
Duk wani hotonta dake cikin wayar sai da yasa a system dinsa.
Ya shiga videos, mafi yawa Indian music ne.
Ya shiga text nan yayi karo da text din Suleiman Yana kyarma ya Buda.
```Aslm, Dan Allah lecture din yau karfe nawa ne ?```

Ansa: ```Four```

Na biyun

```Bilkisu ya murar? Allah ya Kara lafiya?```

Ansa:
```Amin thank```
Chapter 27 · 0% Book details