Sashe 1
Wa Zai Furta Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
🤐 WA ZAI FURTA??🤐
0⃣1⃣
*Gaba daya labarin tukuici ne ga Hajiya Rabi badawi ( maman Ibrahim ) Allah ya shirya Miki zuri'a ya Kara arziki Aunty Rabi tawa*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD MARUBUCIYAR ALJAZEERA DA DR. JUNAID. Barka barka da samun karuwar baby girl Allah ya raya ya dayyaba*
*Domin KU AUREN FARI FANS da YABA kyauta group*
*FARKO*
*Federal University dutsinma*
Gudu-gudu, sauri-sauri take tafiya Babu abinda kirjinta keyi sai dukan tara-tara, dodazon mutanen dake chunkushe bakin gate wadanda security suka dakatar don bincike saboda Babu dalibin dake wucewa wurin sai ya gwada I D card, takaici da karuwar faduwar gaban suka Hana ta sukuni, sakamakon yaune ranar farko da zata Fara shiga aji a makarantar.
Tana cikiniyar wucewa taji an janyo hijabinta alamar an mayar da ita baya Shi Kuma ya wuce da sauri Yana faman daga ID card din nasa, ta bishi da kallo saurayi ne matashi dogo..... *Anwar! Anwar !!* Wani ya bi bayansa da gudu, dai dai ta nuna nata ID card din ta wuce Shi Kuma ya juyo don ganin Mai kiransa har lokacin bai tsaya daga saurin da yake faman yi ba.
Ta kalleshi sosai tare da samun tabbacin fuskar bazata taba guje mata ba, tayi guntun tsaki tabi wata hanya.
Da tambaya ta gano ajin, da Shi ta Fara tozali lokacin da ta kunno Kai, ta hade fuska gabas da yamma ya bita da kallo har ta zauna ....kallon ta yakeyi Yana karanta karancin shekarun ta yanda har ta shigo jami'a wannan yar ficiciyar diyar...... Ya Dan tabe baki, may be giyar kudi taja iyayenta mata jumping.....shigowar lecturer din yasa Shi watsar da zancen.
Sakamakon sune Yan alfarma list din karshe na admission yasa lectures duk sunyi nisa har wasu sun kusa karewa, da alama ajin ita kadaice musulma domin duk matan ajin arnaku ne babu Mai alamar ko gyale ko wace ka gani gashi hirtsi-hirtsi.
Yawancin su ko *zo in kashe ka* basa ji da hausa, a gurguje malamin ya raba script na test din da yayi, yace class rep. Ya raba ma kowa, layi-layi yake bi. Zuwa can malamin idon sa yakai gareta, ya tako zuwa inda take tare da Fara jefo mata tambayoyi.
Gaba daya hankalin Yan ajin ya dawo kanta ana jiran aji idan zata iya bada amsa da turancin kamar yanda yake magana wasu nata sumke dariya cikin su harda Anwar saboda kowa yasan yaran hausawa da kwabar turanci.
Ta Sha *mur* kawai yayi maganar duniya taki bashi amsa. Kowa mamaki yakeyi *Anwar* ya Kara binta da kallo duk miskilancin sa yau ga kakar sa ya samu. Hankalinta a kwance ko motsi takiyi haka malamin ya gaji ya kyaleta tare da Shan alwashin idan tasan wata ai Bata San wata ba. Dai dai lokacin da class rep ya gama raba takardun. Lecturer din ya ce Wanda baiga nashi ba ya fito, mutum biyu suka fita duk Mata sunfi mintuna shidda a tsaye kafin yace su kadai ne? Duk akayi shiru yayi ta maimaitawa Amma ba Wanda yayi magana, ya fiddo takardu uku yace *Hamza Yusuf* ya Kira sunan yafi sau goma Amma da alama baya ajin yace shine highest he scored 9/10 ya kalli biyun yace kune second highest kunci 8/10 ya Mika wa kowace takardar ta da one thousand naira, yace class rep ya turo mishi *Hamza yusuf* office domin ya amshi kyautar sa da Kuma script din nasa.
Har ya kai bakin kofa ya juyo what is your name? Kanta a kasa sai da ta kusa da ita ta zungurota sannan ta dago har lokacin fuskarta a murtuk, da kyar ta iya bude baki tace *Bilkisu Abdullahi gada* ya kada Kai *Discuss the macro objectives of ERGP In Nigeria* you'll present it next week in front of everybody as your make up of this test.....ya na gama fadar haka ya fi ce abunsa, ta sunkuyar da Kai kawai tana rubuta question din a bayan littafin ta .......kowa ajin ita yake kallo ganin ba wani alamun damuwa a gareta .....Anwar ya kalli abokin sa yace waccen yarinyar gadararriya ce yayi murmushi ta kaika?.
Ganin an Fara mikewa yasa tayi zumbur ta Mike Babu inda tayi ma tsinke sai sit din Anwar Yana ta kokarin tattara takardu zai Mike ta tsaya kansa, agidan ku ba'a koya maka tarbiyyar daratta mace ba? Ta fada Kai tsaye gaba daya shock ya Kama Yan ajin masu niyyar fita duk suka dakata, da sauri ya kalleta..... Ta jefe Shi da wani mugun kallo na wulakanci kafin ta ce kawai don ka dauki mutane banzaye Ina tafiya zaka Kama mun hijab ka mayar dani baya .......ke! Ya daka mata tsawa tare da mikewa tsaye .....itama ta daka mishi tsawa, zaka dakenine marar tarbiyya? Tare da zaro mishi ido idan hannunka ya Kara gigin taba mun hijab wallahi duk Wanda ya tsaya maka a school din nan sai na ganshi mtseww....ta buga tsoki sannan ta nuna Shi do yatsa, ka kiyaye ni banzo Nan don inyi wasa ba kasa hakan a ranka ta watsar da takardun kasa ta koma ta zauna, wani uban tsalle yayi wallahi sai ya daketa aka rike Shi yana ta faman ihu kamar mahaukaci , ko ajikin Bilkisu taci gaba da rubutun ta kawai da kyar aka fitar dashi ajin.
Mutane sunfi ashirin bisa kansa suna bashi hakuri hada Yan aji uku da hudu akan kada ya biye Mata yarinya ce. Da kyar aka shawo kansa.
Ya fakaici idon kowa ya tafi amsar script dinsa domin baya so a gane Yana da kokari cewarshi Shi baizo don nuna shidin wani ne ba, yayi wa malamin karyar baya aji ne kawai.
Yana komawa hostel ya Fara karatun presentation din Bilkisu domin yi mata tambayoyi, ita kuwa da yake wani gida take na haya dakuna shidda ne a gidan kowa ne daki sai mutum hudu ko biyar su Kama Amma ita nata Bata Kama da kowa ba iyayenta ita kadai suka Kama wa daki daya sakamakon dakunan suna da tsada ko wane da kitchen da toilet akan dubu dari da ashirin 120k. Notes din da aka wuce ta tabi wadannan Yan matan biyu dasuka ci gift ta karbi nasu tayi photo copy ganin sune masu kokarin ajin. Karfe biyu suka koma wata lecture din Bata yarda ta makara ba, taki sakar ma kowa fuska saboda tana son sanin halin kowa don tasan dawa zatayi abota.
Karatun hauka Anwar keyi saboda Bilkisu ya gama tsanar yarinyar kamar yanda itama Bata kaunarsa, kullum tunanin sa yanda zai rama wulakancin da tayi mishi yayin da ita Sam ta shafe babin sa ta manta da al'amarain shi daga masallaci sai daki tayi kwanciyar ta tana duba litattafai abinda ya shige mata Kuma sai tayi goggling.
Ranar presentation ta zagayo kasancewar ajin sunfi dari yasa malamin zuwa da microphone tana cikin tashin hankali da firgici Amma miskilancin Bilkisu yasa ba Wanda ke gane hakan. Abinda kawai ya kawo malamin shine don tayi presentation din kusan Shi da Anwar Abu daya suke sakawa a zuciya watan sai sun kunyatata.
Fuskar ta tamau ta Mike ta isa gaban Allon yayin da ya Miko mata abun maganar jikinta ya tsinke da kyarma anan ya fahimci hakan wurin amsar abin maganar yanda hannun ta ke kakkarwa. Idanun ta suka kawo ruwa tayi saurin cewa *innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta tsaye tare da sunkuyar da Kai kasa ta Fara magana a hankali cikin taushin murya wacce ke cike da tashin hankali.......
My name is Bilkisu Abdullahi gada and I'm here to present the macro Economic objectives of Economic recovery and growth.......yanayin fitar turancin nata yasa ajin natsuwa tare da Kara zura mata ido lecturer din ya Goya hannuwa biyu kawai Yana kallonta Shima .....
Bayani take karantowa cikin natsuwa tana Kara lankwasa turancin nata cikin kalmomin kwarewa da birgewa hakan ya Kara tarwatsa zukatan kowa ciki harda Anwar ta share kusan mintuna hamsin tana magana har sai da malamin ya dakatar da ita Shi kansa jikinsa yayi sanyi.
Ta saki ajiyar zuciya a hankali har lokacin kansa na sunkuye ....ya kalli Yan class din *Any question*? Duk akayi tsit! Amma wasu idanun su Yana ga Anwar kallonta kawai yakeyi ya rasa ma mezai fassara tunanin sa. Malamin ya watsa hannu tunda ba tambaya ni ina da ita, ya jefa mata daya.....tayi jimmmmm kamar bazata iya amsawa ba kafin ta Dan motsa kadan ta Fara zakulo bayani, gaban ta yazo ya tsaya Yana kallonta har ta Gama, sannan tayi shiru.
Yafi mintuna shidda baiyi magana ba kafin ya kalli Yan class yace please will you help me give her a roundplus? Duka ajin yadau tafi.......raf raf raf abun mamaki ciki hada Anwar.....ya fiddo five thousand ya Mika mata congratulations you score 10/10 wallahi......ajin ya dauki ihu da sowa.... Ta danyi murmushi kadan kafin ta karba ta wuce abinta har lokacin jikinta na karkarawa.
Duk ajin ya rikice da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa, haka malamin ya fita kamar jira Anwar keyi ya Mike ya Isa wurin ta, congratulations sai a bamu ladar ganin ido......Ibrahim da sauran Yan aji kowa ya zaro ido domin kowa yasan Anwar da gadara, rainin saying da Kuma girman Kai.
Kowa na jiran abinda zatayi sai kawai ta dago tana Yar dariya ( domin Bilkisu Bata da riko ko kadan da anyi mata zata rama Kuma ya wuce har abada wurinta).
Ta tura mishi kudin to gashi ai ba nisa sukayi ba ta fada tana Kara Yar dariya, tadanji kunya matuka domin neman fada yazo, ya danyi murmushi kya turan kudi? Kiban kaso na kawai ko rabawa zamuyi? Ta Dan kalleshi kadan.......gabansa ya Fadi kwarai a karo na farko. To mu raba Mana ta fada tana maida kanta bisa littafi.... Okay ya Mika hannu bani nawa toh, ta nuna kudin da baki gasu nan ka dauki naka kabar mun nawa..
Yayi Yar dariya kafin yasa hannu ya dauki 2500 yabar mata 2500.
Amma Kuma ya kasa tafiya sai juya kudin yake da hannu Yana murmushi. Ta dago Kai ta juya mishi ido alamar tsayuwar ta mecece tunda ta sallameshi? Sai kawai ya bushe da dariya yace okay thanks. Ya fice class din abikansa da wasu Yan ajin suka bi bayansa, ta kwashi Yan takardunta tayi daki domin sai 2 zasu dawo wata. Yana tsaye duk an rufeshi ana mishi surutai sai dariya kawai yakeyi tazo ta raba ta wuce ya ringa satar kallon ta har ta kule.....
*****************
*KADUNA RIGASA*